🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘
MATAN QUATERS
✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah Azare
Ummu imanFollow me on wattpad
@kulsumbappa facebook: @ukb696354.kb@gmail.com
Gmail Add @ ukb696354@gmail. Com🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻بسم الله الرحمن الرحيم
Gaisuwa ga daukacin members na MATAN QUATERS FANS,
ALLAH YA KARA KAUNA.2⃣0⃣
Ayya malam ai da ka kyaleta don bakin mutum daya dai ba zai gagara ba,
a wurinku ba
Mama ce ta jiyo su ta fito
Wai mi yake faruwa ne naji malam yana ta dumi?Wallahi kuwa indo ce tace mishi tana son ta koma gidan QASEEMU Da zama shine yake neman yaki maganar,
Eh ai dole naki ya,
Ya za'ayi su tattare gaba daya suje su takora mishi,
Yaushe ma ya koma birnin?Mi yake dashi?
Sannu malam akan mi zaka hakikance kace indo bazata ba naga dai duk mutum da yake birni kudi ne dashi,idan ba dan yana da kudin ba ya isa sayan gida a birni,
Kai kai kai sannu maimuna wa yace miki gida ya saya a birnin?
To kwantar da hankalinki,
Zaune yake a gidajen gwabnatin tarayya da take bawa ma'aikatan ta,To malam nidai ka kyaleta ta taje mana insha Allahu Allah bazai hana shi abinda zasu ci ba,
Ke salma ki fita daga idona na rufe,
Nace bazata ba fakat,Nan indo ta mike tana guna guni mama tana ta bambamin fada,
inna dai karshe tashi tayi ta shige daki don mama ta fara
cewa''
Kawai baka son a rabi dan lelenka ne, idan ba haka ba ya za'ayi ace za'a daura mishi nauyi mutum min da yake birni,''Haka dai rayukansu ya baci hakar su bata cimma ruwa ba,
Sun so ace ya bar ta ta tafi itama,amma ta yaya za'ace UNAIXA ita da yaranta ne zasu na moran QaSEEMU su a ganinsu kudi ya tara basu san cewa kawai karfin hali bane.
Sun tafi islamic chemist sunyi musu bayani ya hada mata mayukan su Habbatus sauda daya tofe da Ayoyin karya sihr, yace tana shafawa a cikin insha Allahu babu Aljanin da zai iya kawo farmaki,
Maman intisar ta fito kenan zata tafi gidan maman daddy domin ta dade basu hadu ba,
sai gani tayi ana sauki abubuwa a nannade a cikin wani farin leda ta rasa gane miye tsabar tsegumi na cinta
Fasa tafiyar tayi ta shiga gidan balki ta samu mai aikinta tana share falon,
ah luba ina kujerun kuma?ai tun jiya an fidda su,
Ke don Allah,
Allah gashi yanzu ma har an kawo wasu sabbi da za'a saka,
Suna haka sai ga bilkin ta fito cikin wani tsadadden voile ruwan sararin samaniya da akai mishi ado da fulawa mai ratsin ruwan fauda wuyanta kuya yasha sarkar zinare kirar kasar ingila
A' maman inti,
Na'am
Zan fita ne naga ana sauke abu na gagara fahimtar miye?
Oh kujeru ne da akayi order suka iso,
Kai har sun zo?
Ikon Allah nima baban inti dazu yake ce min sunyi magana da kafinta zai zo wurina na bashi sample din da nake so?
YOU ARE READING
MATAN QUATER'S
ActionZAMA NE IRIN NA YAN BARIKI, MATA SUBAR GIDAJEN SU, BA WANKA BARE WANKI SAI GULMA DA SA IDO.