🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘
MATAN QUATERS✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah Azare
Ummu imanFollow me on wattpad
@kulsumbappa facebook: @ukb696354.kb@gmail.com
Gmail Add @ ukb696354@gmail. Com🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻ALHAMDULILLAHIL-LAZI BI NI'IMATIHI TATIMMUS-SALIHAT,
Allah ya nufa yau 2/10/2019 na gama jarabawar zangon farko,
Ina barar Addu'ar ku Allah yasa mun dace,Sannan ina kara godia ga masoyana wadanda suke ta bibiyar MATAN QUATER'S
Allah ya kara kauna
Jinjinar girma ga REAL MAI DAMBU
Allah ya raba lafiya,بسم الله الرحمن الرحيم
2⃣2⃣
Tana ajiye wayar,
Kishingida tayi akan sallaayarta, taki komawa gado ta kwanta, saboda tasan baza'a dadi ba za'a faara kiraye kirayen sallar asuba,tana gudun makara.Maryama abinda nake so dake shine ki dage da Addua'a akan wacce kike yi,
Saboda hankali na ya gagara nutsuwa da abokiyar zaman kin nan,
Wannan hadin kan da suke yi da matan unguwar nan marassa da'a da tarbiyya nan sam ban yarda dashi ba,'' to inna in sha Allah zan dage,
Allah ya shirye mu gaba daya,
'' Amin maryama
Allah ya raba ku lafiya,Maryama bata iya amsawa a fili ba, can cikin zuciyarta ta amsa,
Saboda kunya da kuma tarbiyya da iyayenta suka ba,Nan inna ta umurce ta da ta tashi taje ta bawa mustafha abin zai karya kumallo,
Ta dan tsaya tana wasa da yatsun hannayenta,
Inna tace mata'' ke tashi ban son shiririta nasan yanzu haka yana jiranki ne,
na gode da gaisuwa,Ta mike,
Tana fita ta gamu da maman Auwal a tsakar gida,
Auntyna ina kwana?
Idan akwai abinda Maman Auwal ta wasa a rayuwarta bai wuce wannan gaisuwar reni da maryama take mata ba,
Ita tana ganin da gayya ma take mata harda cewa Auntynah mtwssssss,
Maman Auwal taso ta zuba mata rashin mutunci amma kasantuwar inna a gidan yasa ta hadiye.
UNAIZA ce ta fito rike da jakar baban umaima, shi kuma yana biye da ita a baya ,
Kana ganin su kasan ma'aurata ne da suke mutunta juna, basu da wata matsala da ta dame su,Ta karanto mishi Addu'o'i ya hau babur din shi ya tafi,
Juyawarta ke da wuya ta amayo sautin maman daddy tana cewa''
Hajia maman umaima ta QASEEMU,
TATTABARA UWAR SOYAYYA,
To dai ki sani
Shure shure baya hana mutuwa sai dai idan lokaci bai zo ba,'' Allah ko maman daddy?
Eh wannan rakiya da wani biyayya da kike nuna ma baban su umaima bashi zai hana ya kawo miki wata ba,
''Ayya maman daddy wazai ki kaari Allah ya bashi ikon kawowa ta kwarai,
ba tare da ta kara komai ba ta wuce cikin gida abinta,Haka kika ce UNAIZA?
YOU ARE READING
MATAN QUATER'S
ActionZAMA NE IRIN NA YAN BARIKI, MATA SUBAR GIDAJEN SU, BA WANKA BARE WANKI SAI GULMA DA SA IDO.