shafi na talatin da hudu

98 11 0
                                    

🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘

MATAN QUATERS

✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah Azare
Ummu iman

Follow me on wattpad
@kulsumbappa facebook: @ukb696354.kb@gmail.com
Gmail Add @ ukb696354@gmail. Com

3️⃣4️⃣

Tashin hankali gobarar gemu!!!! zubewa ne kawai batai ba a wajen.
Laureeeeeee
Keeeeceeeeeee?
     Zubur ta miki zatai kanta
Sai muryar mahaifiyarta taji
   "
Kar ki kuskura ki taba ta!
  Kinsan kina son nashi kikai watsi da shi, kikai watsi   da 'yarki tilo da Allah ya baki?kikai wasa da damanki to Albishirinki duk wannan abinda kika ga shawaarata ce da  ta mahaifinki,  mukai mishi ko zaki dawo kan hanya ki rike mijinki ki rabautaaa   Lauratu ke kuma kar sanayyar ki da uwar gijiyar ki a da ya hanaki kula da mijinki,
Duk ku taru ku zama daya"
  Kai kuma Allah ya muku albarka
Mama anya kune mahaifana kuwa???
   Tassssssss don ubanki tsunto ki mukay.
   Haba umma kiyi hakuri
  Ta daga mishi hannu ka kyaleta
  Ya rage  naki  dabara ta ragewa mai shiga rijiya,
  
Da gudu  ta tafi daki ta fada gado tana kuka, bata taba tsintar kanta a bacin rai irin na yau ba tunda take a rayuwarta

Baban salima don Allah kaje ka lallashe,

Tana bukaatar kulawarka ace ka juya mata baya mahaifanta sun juya mata baya duk da nasan kaza baza ta taba taka 'ya'yanta don bata son su ba
Haka kuma sai ka duba karan da suka maka da soyayyar da suke maka ka kula 'yarsu,

********************
Balkisu tana cikin mawuyanci hali likitoce sun fi awa uku akan ta anata aikin ceton rai cikinsu harda dr WAFEEYA, ita kanta ta karaya da yanayin da taga yar uwarta a ciki,
  Mijin kuwa nacan yana ta sintiri a kofar dakin yaga dai bazai ficce shiba,
Alwala yayi bai saN adadin sallolin da yayi ba akalla yayi yafi. Minti arbain yana kwararo addu'oi a cikin sujadda cikin yana fahimtar abinda yake karaantawa har ya hakura ya sallaMe,
Ya tashi ya leka tagaan da take ciki,
Har ila yau likitocin suna kanta
Abin da ya Kara tayar mishi da hankali ganin iyayenta suna kira
Har zai katse sai yaga rashin dacen hakan.
Ya tattaro nutsuwa ya sa wa kanshi
Ya buga number bugu daya suka dauka cikin ladabi da mutuntawa yake gaida sirkin nashi  sukai barka wa junA daga bayA ya mika wa uwar
Ina BILKIN?
Nan ya hau in e na yana kame kame,
anya lafiya kuwa??
Don mun kira ba adadi bata dauka ba,
Lah ba komai kinsan yanzu a kaidar haihuwa sai sunyi awa shida tukunna a cikin dakin haihuwar saboda gudun samun wani matsalar to banbancin su da nigeria har wayar ma karba suke wai kara ma zai iya za su cikin firgice a awwanin farko na haihuwar,
  Ya samu karfin gwiwa na ta kwarrara musu bayani tamkar shine likitan,
Yana cikin wayar yaga ma'aaikataan jinyar sun zo diban jariran,
Inaa za'a kaisu
Da guntun larabcin shi yake tambaya
    Ko ba komai ya fahimci wajen uwar ne,
  Yabi bayansu ya ci gaba da leke ta taga da ikon Allah yaga jariran sun kama nonon  nan aka hau hamdala domin wata likita ce ta kawo shawaran hakan tsotsan nonon uwa da jariri yake yi yana rage matsalar zubar jini bayan haihuwar mace kuma yana taimakawa matuka gaya wajen daidaituwar mahaifa ta koma gurbinta da wuri shiyasa ake so ko ba ruwan nonon a basu suna zukaa.
Kamar daukewar ruwan sama Allah ya kawo saukin lamarin
Jinin ya tsaya chak
   Yayinda sabon da ake sa mata ya cigabA da shiga yana kewaya wa yadda ake so

********************
Ana ida sallar asuba KASIMU ya  samu Baban hydar yake ta bashi baki,
Tare da nuna mishi kuskuren shi akan sakaci da sake a lamarin  iyalan shi
( Yana daga cikin kuskuren da magidanta suke. Yi a wannan zamanin shine rikon sakainar kashi akan lamarin aure,aure ya zama sakaka ba ka'ida linzami na hanun mace,duk abinda taga dama shi zatayi lokacin da take so ta fita,
Ta dawo a lokacin da ta ga dama sannnan uwa uba namiji ya zama hoto tarbiyya da kula da gida duk miji ya barwa matarshi ragamar su ba dole a samu fitintunu ba
Kuma wai abin mamaki namiji yana kwance a gida zai tura matarsa cefani)
Sannan mal tukur kayi hakuri ba katsalandan zan maka a rayuwarka ba.
Shin kana samun lokaci da kake zama da matarka ku zanta?
   Ya girgiza kai,
Kai hakuri ina yawan ganinku a majalisar mani mai shago,
Miye amfanin zaman da zakai a majalisa iyalinka  tana gida idan shiru ya isheta ta tafi gidan makota ,miye amfanin hakan anan ake fara gurbata musu tunaninsu,
Yanzu miye amfanin hakan sai abu ya lalace kuce zaku daauki mataki bayan kayi wasa da damarka,
Yayi ta mishi nasiha tare da tunasarwa game da hakkin da yake kanshi.
Cikin shi yayi sanyi ya hau mishi godia in sha Allahu zan gyara kuma na gode sosaai.
Na kuma janye saken Zata iya komowa dakinta,
  Yauwa Alhamdulillah kuma don Allah kasan da wa iyalanka zata na muamala,
  ********************
Maman hydar dai tana ta ganin ikon Allah don cikin kaankanin lokaci UNAIZA ta kintsa komai tsaf an gyara gida,an yi abin karyawa  da taimakon baba musa ya share musu tsakar gida dA kofar gidan
Tana fitowa daga wanka ta wanki su UMAIMA da kannenta,
  Har ta kawowa maman hydar abin karyawanta ba wani abu bane dafadukan taliya ce da tasha soyayyen kifi dan Argungun
Sai kunun koko da aka dama yaji kayan yaji gashi fari tass
Waya ce take ta kara kusan sau uku tana dubawa
Tasa a kunnenta
Auntyn yara....
   Lah  maman umaima kuyi hakuri na tashe ku da sassafe
Ba komai suka gaisa cikin mutuntawa,amma ki bugo anjima tunda ya fita sallar asuba bai shigo ba
   Yauwa dama wayar ta kice na kira nakin ne ban samu ba,
  Ai kuwa nakan saata a fly mode ne idan zan kwanta  na taba farkawa zan bada khalid ruwa ashe na  kira babana cikin dare hankalinshi ya tashi.
  Ayya ba komai
Wai Abba ne yace a tambayeki   wani kala  kika fi so kayan daki???

Ban gane ba,
Cikin risinawa da girmamawa da rashin izza tace wai zai mana kayan daki ne,na zabi nawa kalan ne sai yace na tambayeki.
  Ayya amma Auntyn yara kar ki damu jiya jiya yayana ya turo min kudin kayan gadon nikaam har munje ALGAZARU na zaba yau Zamu je mu dauko,

ah Aunty wallahi Abba ma ya biya jira ake kawai aji naki ra'ayin a dauko,
Kiyi hakuri ba wai a rashi bane ko kuma rai ni bani.
Don Allah.
To Zubaida ki tsaba min kune yar birni kun fini sanin kala mai kyau,wanda zai dace da mi yarA,
Ki mishi godia Allah ya jikAan mahaifaa,
Suna sallamewa taji sallAmar baban umAimA  falo,
Yace
BaKuwarki ta tashi ne??
Eyy ta tashi

To kirata
    Ta fito da hijabi ta rakube. A gefe ta gaishe she cikin kunya,
Nan ya mata nasiha sosai akab hakkin aure da kuma hakkin da ya rataya akanta zuwa jimawa ki shirya unaiza zata raka ki,
Haba ta zube tai ta mishi godia. Marar adadi,

   Ya ce ba komai hakkin makotaka ne"
  Ya barta nan ya wuce daki,
UNAIZA ta bishi da wayar shi.
Haba tsabar murna da kyar maman hydar ta karya,
Tai wanka
Unaiza ta nemo doguwar riga ta bata,
ta sanya da kyar
Allah kenan mutumin da ka tozarta shi wai ashe shine masoyinka,
Har humraa mai dadi unaiza ta ba ta shafa
Kasimu ya fita Baba musa ya shigoo,
   Sukai shawarwarinsu akan maganar da sukai da zubaida,
"yawwa
Aunty kar ki damu inaga hakan ba komai bane
Kuma dai ba'a shaidar dan Adam  ne amma inaga wanda ya gaji arziki kamar bazai  yi abin da kike tunani ba,
Sai dai mi zai hana ki tuntubi maman Hanifaa"
   Yauwa to shi kenan
    Ita dai maman hydar abin yana ta daure mata kai amma ta kimtse
A hanya suka gamu da Mubaraka ta fito shagon mani
Ta kallesu da kyau ta yatsina baki hmmmmm,
Ba zuciya an sake mutum yaki tafiya,
ina ruwan karya marar zuciya,
Uban waye karya?
karya wacce ta wuce ki.
Kiyi lalata da wannan kiyi da wancan kekam ai kuda ce ke baki san halal ba mijin yarki ma kin kyale ne,

Unaiza ta dakatar da ita kar ki biye mata ba tsarar ki bace,

Ai mubaraka sudidi ta wuce ciki ya dura ruwa
Ashe an saN alakarta da baban daddy??

Tab chakwakiya
( baki idan ya san na fada bai san na mayarwa ba.)

Yauwa kar kice na miki shishhshigi nace kuna ta magana a waya da kuma kanin maigidanki?

   Ohh ehh Amarya tane muke wayan kina jin mu ashe???

Ehhh abin ne yake bani mamaki ance z'ai miki kishiya kullum sai kinyi bala'ei wa mijinki har sai an shigo an raba ku ko abinci baki bashi
Ni kuma sai naga akasin haka,,,

"Hmmmm haka rayuwa take ai maman hydar.

Suka yi sallama aka bude da gudu yaranta sukai yo kanta " mummy ina kika je mukadai
Baba ya mana abinci marar dadi.
    Taga gidan yayi  kaca kaca,
Oh Allah sarki gidana da na Bar ka fa kenan
Ta kama hannun unaiza

"Allah ya biyaku da Aljanna Allah ya saka muku da alheri kuma ki kara min godia,
Daga yau kuma  don Allah ki bani dama duk abinda ya shige min duhu zan zo na same ki"
Ba komai yiwa kai ne,
Sukai sallama ta rakota kofar gida
Ta juya ashe mijin yana ciki tana ganinshi ta zube tana godia na damar da ya kara bata,ya kara ja mata kunne da kashedi ya rabata da kowa a ung amma banda gidan Kasimu kuma shima ba kullum ba sai jifa jifa.

********************
Wafeeya ta ce drr na lura baby 3 din nan idan aka dauke shi yana kuka sosai,
   Mi ko min shi  na duba suka dudduba shi  inaga kamar hannun shi akwai damuwa amma bari na kira dr Amrishh ya duba shine yake fanin likitancin kashi na yara,
     Kafin mintuna anyi hoton kashi an gano matsalar inda take,
Sun basu  lokaci dA zasu yi mata aiki kasAncewar suna karkashin kulawarsu ne
Bilkisu duk bata san abinda ake tattaunawa akai ba gudun tashin hankalinta,
ba'a son ta shiga tashin hankali.
  Wafeeya ta koro bayani wa baban yan uku,
Maimakon ya damu sai ya hamdala wa Allah,,,,,,,,
   Yana ga hakan ma yazo da sauki tunda yan uwan ne suka danne shi shiyasa ko a scan biyu ake gani ba uku ba.

✍🏼✍🏼✍🏼
Maman Iman

MATAN QUATER'SWhere stories live. Discover now