🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️
MATAN KWATASKulsum Bappah
Azare
Ummu imanKu bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:ukb696354.kb@gmail.com
EMAIL: Ukb696354@email. Com🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻
6️⃣0️⃣النهاية
FINAL🔚🔚🔚
الحمد لله الذي بنعمته تتم الصالحات
Larabawa suka ce"*"مهما طال الليل سيظهر الفجر !! !"*
" *_WAI KOMAI NISAN DARE GARI ZAI WAYE_ "*Daga wajen taron gidan Alhaji BAGUDO aka wuce gaba dayansu Bello ne kawai ba shi a wajen,
Bayan kammala liyafar cin Abinci ne ALH SULAIMAN BARKINDO ya mika wa Kasimu key din motoci guda uku: biyu iri daya dayan kuma daban
Mai daban din naka ne biyun kuma na matanka ne,
Tukwicin gaskiya da rokon Amana da kayi kenan,
Ban taba tsammanin akwai sauran irinku a rayuwa nan ba,
Na fid-da tsammani gaskiya ashe har yanzu kuna da saura to!
Allah ya dorar da kai alan halinka na kwarai!!!
Kuma ina fatan Allah ya kara datar da kai akan gaskiyar ka,
Sannan ga takardar aiki wa kanin ka musa ina son ya zame min ma'aji sannan ina son na hadaka da yaro na kanin mai daki nane gashi nan sunan shi Fadeel ya zama shine manager kai kuma M.D saboda haka don Allah asa shi a hanya sosai kwanan nan ya dawo daga karatu to shima ina son ya koyi dogaro da kai ya san neman na kan shi,ALH BAGUDO yace " to gaskiya ka min shigar sauri na so ace MUSA ya maye gurbin Kasimu A PRINTING PRESS din mu amma duk daya ne Allah ya sanya Alheri,
Ke kuma zubaida ina son ki mikawa musa dan makullin motar ki,Musa yace "
" YAA SALAAM,!!!
gaba dayansu sukai musu godia rabo kenan haka yake
Unaiza tai musu kyakyawar Addu'a cikin harshen larabci sukai ta binta da Ameem Ameen,
Daga nan suka fita harabar gidan ganin sabbin motocin sun,
Kasimu yayi mamaki da yaga irin motar da aka mallaka mishi irinta ce ake cewa ONE IN TOWN fara ce kal samfurin MERCEDES 4MATIC new model dinta kamar a satin nan ma aka fidda taBai tsinke da Al'amarin mutanen ba sai da yaga motar zUbaida iri daya ce da ta unaiza kuma tsabar kara sanda aka ce unaiza ce zata fara zaba kafin zubaidan ta dauka ta ta.
Da yake itama akwai dattako tace " a'a ai nice babba karama ce take zaba tukunna"
Barkindo yace haka ne kam to ki zaba my daughterTa zabi kalan ROYAL BLUE,
unaiza ta samu golden kuma dama itace ta mata tun farko amma kuma baza tayi
azarbabin zaba ba,
To da yake Allah ya nufa itace rabon nata aka bar mata ita,
Unaiza a take ta kira mahaifinta ta fada mishi Alherin da aka mata yace
" Basu wayar to nayi masu godia"
Mikawa Alh Bagudo wayan tayi ya karba suka gaisa yayi mishi godiar jinyar zubaida
" Allah ya saka da Aalheri "Ya mikawa Barkindo suka gaisa cikin mutunci da mutuntawa,
Bayan komawarsu gida ne Sai ga Bello
kasimu ya kira shi
" Bello lafiya kuwa naka halarci wurin taron ba?" Lafiya kalau kawai cewa nayi gwanda na kwanta nayi bacci yafi min Zuwan naje na sha rana da zafi,
( Wai ya fadi hakan ne don ya kunta ta mishi ya nuna shifa bai damu bama irin ko ohon nan )
YOU ARE READING
MATAN QUATER'S
ActionZAMA NE IRIN NA YAN BARIKI, MATA SUBAR GIDAJEN SU, BA WANKA BARE WANKI SAI GULMA DA SA IDO.