shafi na Ashirin da Tara

319 50 5
                                    

🏘🏘🏘🏘🏘🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘🏘🏘
 
MATAN QUATERS

✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
     Kulsum Bappah Azare
       Ummu iman

Follow me on wattpad
@kulsumbappa facebook: @ukb696354.kb@gmail.com
Gmail Add @ ukb696354@gmail. Com

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻

2️⃣9️⃣

UNAIZA kwana tayi tana Sallah da lazumi da yake Al'adarta ce bata taba kwanciya bacci sai tai Alwala ba,
   Tafi minti goma a sujadarta tana rokon Allah ya bata hakuri, da juriya,  shi kuma ya bashi ikon yin Adalci a tsakaninsu, kai bata daago ba sanda ta ambaci sunnan ZUBAIDA idan shigowarta Alheri ne, Allah ya tabbatar, Allah yasa ta zama abokiyar Arzikinsu kuma abokiyar hadin kanta da zaata taya ta tallafawa yaranta wajen samun ingantacciyar Tarbiyya , ba wacce zata wargaza mata gida da yaranta ba,,
  Daga karshe kafin ta sallame sallar ta_ bayan ta gama karatun TAHIYARTA ta kara kai kukanta wa mahallacinta tana mai cewa " Ya Allah ya ubangijin sammai da kasai yaa ubangijin musa da haruna,Ma'abocin Alarshi mai girma da daukaka, kada ka barni da Dabara ta ko wayau na, ya ubangijin jibirilu da mika'ilu, ka sanya duk abinda zai tayar min da hankali ko zai bata min rai yafi ruwan sanyi a gare ni, Allah kar ka barni da son zuciyata....."" Da kyar ta sallame saboda bacci da yake fusgarta,

( _GARE MU MATA AKWAI SIRRI BABBA A LOKACIN ZAMAN TAHIYYA KAFIN SALLAMA,DOMIN ADDU'AR WANNNA LOKACIN KARBABBA CE KUMA AKWAI BIYAN BUKATA_)
  
QASEEMU bai sare ba ana sallar asuba kamar yadda ya saba ya buga mata kofah,
Cikin bacci mai nauyi ta farka, tace "  na tashi""
 

Ranshi yaji ya mishi sanyi da bata share shiba,

Bayan ya dawo ne daga masallaci, ya tunkari dakinta amma sanda ya karanto ( *ALLAHUMMA LA SAHLA ILLAH MA JA'ALTAHU SAHALAN,WA ANTA TAJ'ALU HAZNU IZA SHI'ETA SAHALAN* ) ya samu gefen gado ya. Zauna ta zagayo tana murmushi ta gai dashi, sukai shiru na dan kankanin lokaci, itace ta fara numfasawa

" Amma inaga ya dace ka sanar da mutannen TANGAZA, don neman TABARRAKI,

      Haka ne ko maman umaima?
    Zuciyarshi ta Buga " *AKWAI SAURAN RINA A KABA* "

    Tabbas yasan akwai rigima idan ya sanarwa mahaifiyar shi,kasancewar yadda tadauki UNAIZA tamkar yar cikinta, kuma bata kaunar abinda zai tayar mata da hankali, uwa uba kuma bata sha'awar  namiji ya tara mata barkatai musamman mai karamin karfi,
Domin tana  ganin halinda mutanen gidanta suke ciki,
   
". Kar ki damu insha Allah zan shiga a weekend amma zaki min rakiya????
    Idan kaso hakan sai muje,
     Kaaga bari na tafi madafi kar ayi lattin fita yau,
    Kar ki damu,   naga dan dakinki ya  ya shiga madafin ya fere doya,
     Allah sarki Baba Musa Allah ya biya shi ya bashi mata ta gari,
bashi da matsala,
   Suka cigaba da tattaunawa kafin ta tafi madafin har,
      Ta samu har  yayi nisa,
Ya rusuna ya gaisheta,
Ta karbi matsamin. A hanunshi nagode Baba musa kaje ka shirya jiya kace min kana da hoton radin suna a gidan CHAIRMAN na SUBEB ;
tab ai kuwa na manta bari Bello ya fito wanka sai na shiga,
    To yau mai sarauta ya tashi da wuri ne??

  Ehhh Aunty,
    Naji kamar mutanen shi ne suka mishi waya,
     Wa kenan baba musa?
    Wa kuwa Aunty? in banda  maman Daddy ,
     Tai murmushi suna tare kenan??
    Baba musa yace "  *AI KOMAI AKAI DA JAKI SAI YACI KARA*"
    Maman umaima tace ba komai " *MuNAFURCI DODO NE*

    ********************

Mubaraka na kwance  shame shame a asibitin cikin makaranta,
    audugar mata kuwa an canza tafi leda biyu ,jini ne guda guda yake fadowa, abokan shedancin nata tsorata sukai suka kira Auntyn nata shiyasa ta nemi Bello suka buga sammako tunda baban daddy baya gari,
 
    To ke Mubaraka sake kikayi kikai ciki???
   Haba Aunty wani ciki bayan nace miki uncle T.J ya kaimu asibiti ansa mana IMPLANON,
An dai yi scanning jiyan da muka zo wai jinin ne ya kume min a cikin tunda, tun lokacin da akasa abin ba period nake yiba,
     Ohooo da sauki tunda ba  ciki bane, ( *KO INA MARABAR DAMBE DA FADA??)*
     Sun gama shawarar zasu kira T.J yazo ya dauketa ya mai data gida,
  Yanzu ma da yake da Babur din Bello suka zo yana jiranta a waje ne,

     tun a hanya maman daddy take gwada number T.J yana yi amma bai dauka ba,
Ashe yana gida ne bai fita ba,
     Sai chan wuraren sha daya na safe ya kirata,
     Uwar kadangarun bariki ya akayi ne???
     Kai fah baka da mutunci!! nace maka bani son wannna kirarin inama laifin ka nemo wani,
      - Kai T.J dann Bariki ne ajin karshe,. -

" Yo ina laifi don an kira mutum da halinsa ai hausawa suka ce " *HALIN MUTUM JARIN SA"
      Maman daddy ta katse shi ba wannna ba,
     Kasan halinda mubaraka take ciki kuwa???
     Eh naga sakon kar ta kwananta amma da yake ina tare da matata yau ta faranta min yadda baki tsammani shiyasa ban fito ba,
      Ranta bace, ta kare mishi kallo,
        kai Bariki bai yiba ta ayyana a ranta amma da yake yar dunia ce sai bata nuna abin ya dameta ba,
    Shiyasa naga fara'arka daban kenan yau??
    Kedai Bari wani magani na zuba mata cikin lemo tai ta aiki ba gajiyawa,,
   To matsatstsaku mai baki da yawa yanzu dai zuwa zakai ka dauko mubarakan ku taho gida ayi jinya,
      An gama ranki ya dade!!!,

Na manta ya kamata ku bi ku sayo hanta da sauran kayan karin jini...
       DUNIYA KENAN!!!

********************

Baban inti kuwa yana zaune yana ganin tashar  A.I.T sai ganin matar shi yayi da hilimin kayayyaki iita da mai aikin Bilkin suna shigowa,
    
  Wata rigimar kika kara dauko wa ??
    Abinka da tunzurarriya jira take     ta fashe,
    
   Eh rigimar na dauko,
  Ina ruwanka?
  Idan yan sanda suka zo tafiya dane sai kar ka tsari,'

   Kwantar da hankalinki ba ba ni na *KAR ZOMON BA RATAYA AKA BANI*
     Yo haba ka isheni jiya ce min na fiye kaudi  bani da nutsuwa,
Yau kuma kace rigima to nayi, kai K'ULUN KULUN KUBURA DA NI.MANA,
      Da yake yasan halin abarshi, wasa ya maida abin, " rabin ran ina kika samo??
   Ta zumbura baki ta shige daki,wayar ta ta dauko tafara daukan  hoton kayan tana turawa a STATUS,
     A karshe ta rubuta YANZU MUKA FARA KASUWA;YAN DAMFARA KU YI TAYI,
    RANA DUBU TA BARAWO RANA DAYA NA MAI KAYA
   Haka dai tai ta tura sakonni iri iri,abinka da rashin cikakken ilimi don rashin ilimi ne yake sa mata su mai da STATUS wajen cin zarafi ko maida martani wa makiyi,,
   Shi kenan kowa ya duba STATUS dinka yasan kana fama da abokan gaba ko yan Hamayya,)
     
To na dawo gare ka, ta kwashe tsaf yadda sukai ta fada mishi,
     Ta kyauta gaskiya, amma yanxu kam kin yarda ta fiki ko??

    TABARMAR KUNYA DA HAUKA AKE NADETA" ko yanxu tamin Gadara da  iko zan mata,ina itama na banxa take samu,na gwabnati suke ci,,

Allah ya shiryeki maman intisar!!!

****"***************

  Maryama ce tai sallama dakin maman Auwal, ta samu can gefen gadon ta rabe don gaba day dakin zArnin fitsari yake yi,
  Ta lura maman Auwal ko sallamarta bata amsa mata ba,. 
   Amma ta basar
    Dama shawara nazo da ita, mi zai hana ki samu inna ki bata hakuri..........

Katseta maman Aunwai din tayi,

   Ba yamma ce ba shawara ba ko kuma koriya tsabar kissa da kutungwila da makirci irin naku na zawarawa da suke aure mazajen mutane su kanai naye su, su hana su sakat su da 'ya'yansu, zaki zo ki min iyayi, na fiki sanin bariki na gaya miki, kuma innar zata tafi daga ke har mustaphan sai nayi maganinku,

       Ita ko maryama ko gezau dama tasan zata fuskanci abinda yafi haka ma,

  " Ko ma dai mi zaki ce gaskiya na fada miki, amma ki zauna kiyi tunani; baki dauko wa kanki hanya bai bullewa ba kam Gaba da uwar miji,
     Amai ne yake son taso mata, tsabar zarnin   dakin yayi yawa.
   
Yar mutan Azare!!!!
 

MATAN QUATER'SWhere stories live. Discover now