🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️
MATAN KWATASKulsum Bappah
Azare
Ummu imanKu bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:ukb696354.kb@gmail.com
EMAIL: Ukb696354@email. Com🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻
3️⃣9️⃣
Kasimu ranshi idan dubu ne ya baci,
Inna ce ke tausar shi,
Na sani akwai shirin akan su amma kai zumumci zaka duba uba daaya ba wasa bane,kar ka kuskura rashin hankalinsu ya rabaku,
Sannnan ina so ka sanya ido sosai akanshi ,
Kar ka kuskura ya samu ya shish shige ma ta saboda shi munafiki da ka gane ko dakin uwar ka ya riga ka shiga sai ka gane a fuskaa,
Kar ka kuskura.
Ya kira yo unaiza yake sanar mata tara sanwa gobe masu gini zasu zo,
Tace to ba damuwa amma nama ya kare,
Dazu na duba,
To ki ma wa musa magana kafin ya fita sai ya sayo anan wurin mahaucin bakin gate,
kinsan wata yayi nisa,
Bayan gama cin abincin ne unaiza ta fito mishi ka kayayyakin Alheri da ta samu,
Har ranshi yaji dadi yasan cewa unaiza ta chancanci abinda yafi haka,
Musa ina na Babana???
" Sai wani sati zan karbo mana,muma namun ruwan sararin samaniyya ne,
Ah to nima kalar zan dinka sai muyi anko ranar daurin aure.
*********************Ammi dinkunan sunyi kyau sosai sai yanzu nake yanin kyan leshin nan ,
Eh sunyi kyau,
Turo min akwatin maman 'yan biyu naga nata dunkunan;
sunyi kyau
Anjima ki shirya muje saayayyan yaran naku ni bazan gane size dinsu ba,
Ina son nan da jibi ma akai mata kayanta,
kinsan Allah Ammi yadda yake bani labarin matar nan bata da matsalaa har sai na fara tunanin anya zan iyah shiga ranshi kuwa?
Sosai zaki iya shiga ranshi sosai amma ta hanyar kyakyakyawan halin ki,
Ta mata karatu sosai irin wanda uwa ta gari ya kamata tayi wa yarta,
Ba irin iyayen yanzu da suke kissima wa yaransu yadda zasu raba miji da mata da yaran shi ma,
" Matukar kika so matar shi kika so 'ya'yan shi kin gama dashi,don hauka ce da rashin hankali ka wari mutum kace shi kake so,baka son iyalan shi,suma mazan karya ne ace ana sonka amma ana kin abinda ka haifahh,
Sannan girki yana daga cikin abinda yake daga darajar mace;
Sai tsafta hakuri kau da kai,tare da fahimtar juna,
Nasan ba ki da jaye jayen kawaye,to ki kara kiyayewa,
Yauwa bani kunnenki sosai kiji,
Ban sani ba ko yana da dangi a garin nan,
Ki kiyaye su,
Tare kika kansu da matar shi,duk wani kauna da soyayya da zasu nuna miki duk ta karya ceKi fara lura tukunna yaya suke,
Yaya maganar fatar bakin su take,
Kar wani ko wata yazo ya zagi 'yar uwarki ki nuna jin dadinki,
Gobe naki zai kai,kuma daga nan ne ake fara samu cece kuce ance kince nace,ki kiyaye,ba ruwanki,
Kuma ba ruwanki da makotai,indai ba gaisuwar jinya barkar haihuwa,hakan ma ku tafi tare banda waran jiki ki tafi,
Kuma idan kuna Hakan kun toshe kofar tsegumi da gulma,Ki kula da kyau ba ruwan ki da wannan damuwar,sannnan banda rainako kinsan dama mijin ki ba karfi ne dashi ba banda gadara banda gori,banda nuna isa,
Tai mata huduba sosai,
Washe gari maman hanifa ta shigo dama ta turo abin karin kumallo,
Sun suka sha hirar su sosai,
Chan ta nunawa unaiza waayarta, kinga kawata ta bude wurin koyar da dinki dasu bed sheet fulalluka saka girke girke,
To shine na mata magana duk da dai ban fada miki ba,
Inna tai caraf tace gwanda ki koya na yarje miki,suka sa dariya,
Kuma a kyauta za'a ta miki,
Inna tace" gaskiya hakan yamin dadi koyan sana'ar yana da amfani zaki ta hidimar ki kuma idan kina da sana'a mantawa zaki da wata kishia saboda sabgar gabanki tafi miki damuwar nan,
Sukai godia ta rakata suka tsaya suka zanta,
Anyi sa'a kasimu bai hanata maman hanifa ta dauke ta suka biya kasuwa ta saya musu kayan amfanin yadi,Allura satin su fiber,Karfe tara ne zuwa dayan rana,
Inna ta kara lokacin tafiyarta saboda ta samu ta na rike mata yaran,duk da tasan ga M hanifa tasan zata rike mata su.*********************
Gaba daaya maman hydar ta canza rayuwarta,wato dama zancen hausawa ne da suka ce idan kaji mutum yace bai iya kuka ba uwarsa ce bata mutu ba,
A hankali rayuwar ta canza kuma ba dole ta samu nutsuwa sosai gidanta ya gyaru zamantakewar ta da mijin ya dai dai ta,
ZAi fita yace mata tuwon alkama nake son ci da miyar kalkashi,
Ta zaroo ido waje alkama???
" Ehhh"
To subhanallahi kasan ban taba yi ba,
Ummm to kiji gidan kasimu mana ta gwada miki,
Ko???
To ba damuwa,
Sai dai anyi rashin sa'a bata nan tace subhanallahi banso haka ba,ta kira mijinta a gaban inna wai bata nan ta tafi center koyan sana'a,
Har ta miki zata tafi,
Inna ce tace "" baiwar AllH lafiya??
" Lafiya ni makociyarta ce nazo ne dama ta gwada min yadda zanyi tuwon alkama,
Ah kar ki damu ta gwada mata yadda zatai,
Sannan ta gwada mata miyar kalkashin tai ta godia ta tafi cikin nasara kuwa tai yayi kyau da yake yar halak ce tuwon ta zuba a kwanuka zata kai wa inna
Zata shiga gidan kenan sukai ido biyu da M daddy,
M hydar kuwa ta watsa mata harara ta juya kanta ta cigaba da kwankwasa kofar unaiza aka bude,
M daddy abin ya kone ta har wani har sunyi shakuwar dA zasu fara musanyar abinci lalle,
Ta shiga tsakar gida ta fara kuzAA ashar don su jiyo da yake ana jin komai,
Su kuwa ma suna falo ba jiyo ta suke ba,
Ta samu unaiza tana ta dinki fulallukan kujera irin kaananan nan da zare da alluraa,
Ta mika wa unaiza gwandon abinci. Gashi ki mikawa Baba, dazu nazo ai baki nan"
Oh dama kice kika zo?
Tana ta min kwatance ban gane ba,
amma nima da baban hydar zai yarda da na shiga wurin koyan sana'ar nan?
Ki gwada tambyar shi mana ai komai da nutsuwa da dabara ake yi ki,
Musamman namiji idan kinga yana walwala ya cika tumbin shi,to zaki iya bijiro mishi da damuwaer ki,
" Haka ne?
Ey kinsan akwai lokacin da zaki ga namiji a birkice an tunzura shi a wajen aiki,
Ko kuma dare yayi yana jin bacci,duk ba lokacin da zaki bukaci wani abu bane,
Tai ta mata bayani dalla dalla,Ta tafi duniar tunani ashe da tayi hauka iya bata bijiro mishi da bukata ma sai suna tsaka da auratayya ya mata alkawari a lokacin kuma ya kasa cikawa daya baYa,
Ta ja dogon numfashi
Tace"" Allah ya yafemu."
Ina baba take ne??
Ina son na mAta godia,
Ta fita tattaki yanzu wai ta gAji da zama ba aikin nan ba motsa jiki,
To ki mata godia don Allah,
Zan tafi kar ya dawo bana nan,
Ta rakata kofa ta jiyo,
Ai kuwa tare suka shiga gida da hubbyn nata,
Wanka zaka fara yi ko abinci ,
Yace " yunwa dai,
Nan da nan ta hada komai harda ruwan wanke hannu a roba abinda bata taba yi ba kenan sai dai ya wanko hannunshi daga madafi,
Da yake mai saurin daukan abu ne ,lura tayi.a gidan unaiza a can gefe tirin abincin kasimu ne harda ruwa wanke hannu a roba,
Shine ta nadaa itama a kwakwalwarta,
Bayan ta kwashe kwanukan ne yasha ruwan sanyi sai ya dauki remote ya canza zuwa tashar kwallon kafa da yake ma:abocin kallon kwallo ne,
Nikam mi ya malaman islamiyar nan suke kin taso yaaran nan ne,kiga yadda hadiri ya taso nan da nan amma shiru basu tashi suba"
Nima abinda nake kissima wa kenan a rAina,
Ya kamata ayi musu magana kam sai ruwa ya duke su mura ta kwAntar dasu ace ayi hakuri,
Baban hydar ni kuwa don Allah ina son na tambayeka abu amma ban san yadda zaka dauka ba,kar kace na fiye ganin kai,ko daga zuwa koyon tuwo na yo ganin kai"
Ina jinki ya juyo gaba daya ya bata nutsuwar shi,.
" Amma kinsan tuwon nan yayi dadi sosai ga danko da yayi kuma miyar ma tayi yaukin sosai ko dai kin kai ne suka miki???
Ko kadan maman shi ce ma na samu ita unaizar bata nan,
Kai dama tare suke da maman shi ce??
a'a bana tsammanin inaga tazo ne kawai,
To ina sauraronki......
Ta fara murza ya tsun hannunta ta fara mishi kame kame....
Kinya don Allah fito kai tsaye ki yi min baayani kinsan bana son dungu,,
Dama unaiza ce naje na samu tana ta dinka abubuwa da zAre da Allura ta ce min. Center take zuwa ta fitar min da takardar wurin abin sha'awa ana koyar da dinki saka kwalliya girke girke,
Shine nace bari nima na nemi izini ko zaka barni na shiga,Wannnan ai kyaky-kyawar shawara ce yana da kyau neman dogaro da kai ne,
Mi ita kawar taki ta zaba
Tace dinki ne ita da kuma dangogin su zanin gado
To kinsan mi za kiyi ke???
Tai saurin girgixa kanta
Ke dauki fannin girke girke sai ya zama kun sha baanban da kawar kin,
Kinga ita dinki ke girki ina ruwan CHEF NA'IMA
Ta sa dariya
Ki yi min kwatancen wurin zanje naje yaya zamuyi.
Tai ta kwararo mishi godia,
Yaji dadi lalle an samu sauyi ,
bari naje islAmiyar yaran nan hala a bani Su kiga yadda gari yayi baki kirin ga samiha da pnumonia.
Allah ya tsare yasa a dace.
Ta daka tsalle gashi bata da lambar unaiza da ta mata busharaa
YOU ARE READING
MATAN QUATER'S
ActionZAMA NE IRIN NA YAN BARIKI, MATA SUBAR GIDAJEN SU, BA WANKA BARE WANKI SAI GULMA DA SA IDO.