🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️
MATAN KWATASKulsum Bappah
Azare
Ummu imanKu bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:ukb696354.kb@gmail.com
EMAIL: Ukb696354@email. Com🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻
5️⃣6️⃣
Bayan kammala wayar unaiza da mahaifiyar zubaida suka ci gaba da tattaunawa akan yananin zamantakewa ita dai zubaida da yake bata faye azarbabin magana ba,
ita kuma unaiza a kowani lokaci so take tana dan janta a jiki saboda ta sake jikinta.
Indo tana tsakani ta gagara samun wuri a wajen zubaida tayi iya kokarinta ta samu fuska amma abu yaci tura
Ana fara kiraye kirayen sallar magariba zubaida tai sashinta don ta gabatar da sallar Almuru
Indo tai sallama wa unaiza
Maman umaima dama so nake muyi magana da fatan zaki bani hadin kanki,
Unaiza ta ce ina saurarenki
Yauwa dama dazu naji kuna magana da iyayen zubaida akan yaranki suje musu hutu to idan ke baki son su mu mana son su,
a wani dalili zasu ce suje musu hutu, salon a barbade mana su a basu shashatau,
Su kangare miki,
To gaskiya ki hana su duk salon munafurci ne,
Kinga idan suka fara jan 'ya'yanki a jiki sai ki sakankance kiga su masu son ki ne tunda suna son 'ya'yanki to a gaskiya ki kiyaye
Dabara suke son su miki
" Kin gama?? Nace kin gama to ki saurare ni da kyau ina baki girmanki da mutunci albarkacin nasan kin girme mi ne, duk wani kullace kullace da kuke yi ke dah bello dasu maman daddy ba wanda ban sani ba shiyasaTo sai sun jen ; idan baki sani ba duk cikin fadin garin nan na birnin shehu wato sokoto bayan mijina da abokiyar zamana zubaida da kuma Aminiyata maman hanifah bani da wanda suka fiye min kusanci irin iyayenta don mutane ne masu mutunci dattako da yakanah, ba abinda zai sa su cutar mun da 'ya'ya a haka kawai baku da aiki sai kin son zaman lafiya, a rayuwarku baku son kuga ana zaman lafiya to ba magani za su musu ba ko shanye jinin su idan ya so su watsar da gawar su; ke nan har wani son su umaiman kuke yi,kar ki manta duk wata kutungwilar da kuke hadawa ke da dan uwanki Bello na sani kai kasimun ma baku so shi da zuciya daya ba inaga yaranshi,??
Lalle unaiza kar ki gayamin maganar banza mana fi mu son yaya kasimun kikai da zaki ce bamu kaunarshi to sannu tattabara uwar soyayya da ma bamu san asalin ki bane naga ina mahaifinki ne ya cusa mishi ke ya binciko a sihirce sihircen nashi taurarin ya kasimu masu haske ne, ya hada auren ku don ya samu hanyar mallake shi da juya shi wata rana
Alhamdulillah kinga kuwa hadi yayi kyau tunda har yanzu daram ina nan cikin birnin zuciyar shi bai gaji da zama dani ya sallame ni na koma gidan mu na daga musu hankali na hana matan yayu nah da matar ubana sakewa ba
Indo ta yunkura kenan sai ga MuSA ya shigo dakin" haba Aunty unaiza miyasa zaki biye mutumin da kinsan matsayinsa dama
" Musa kar ka kuskura ka fadamin magana idan ba haka ba nasa Bello ya min kasa kasa da kai,
Bismillah Aunty indo baki san da da yanzu akwai banbanci ba ko,
Baba musa ba mutuncinka bane sa in sa da itaba ai ko ba komai yar uwarkace ni kuwa bare ce a cikin ku,
Nayi imani da Allah ba zan bari ki shiga tsakanina da mutanen kirki ba ba su ba ma tunda yarsu tazo gidan nan banga wani abin kaico a tare da ita ba balle iyayenta
Kuma yara in sha Allah sun je an gama,
Ita kuwa zubaida ashe tun farkon fara maganganun indon duk a kunnuwanta tana idar da sallah ta manta da karamar wayarta a dakin unaiza,
Da yake sabon shiga jin wadan nan abubuwan ne ta koma daki sai kuka take yi an dora wa iyayenta kazafi,
Bata san kadann ta jiba indai sharrance sharancen dangin miji ne ta gode Allah ma da unaizan basu da matsala da ita,
YOU ARE READING
MATAN QUATER'S
AcciónZAMA NE IRIN NA YAN BARIKI, MATA SUBAR GIDAJEN SU, BA WANKA BARE WANKI SAI GULMA DA SA IDO.