shafi na biyar

506 46 1
                                    

🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘

MATAN QUATERS

✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah Azare
Ummu iman

Follow me on wattpad
@kulsumbappa facebook: @ukb696354.kb@gmail.com
Gmail Add @ ukb696354@gmail. Com

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻
0⃣5⃣
Fadi tashi asarar mai rai,
UNAIZA yau kwanan su 2 da yin Arba'in,
Zaune suke da inna tayi mata dahuwar ciccibi tasa ta a gaba tana ci,
Yar nan gwanda ki maida hankali kici,
Mutuncin ki kenan a wurin da namiji.

UNAIZA,
ta riga da ta saba domin tun haihuwar umaima ma haka ta kintsata ta gyarata,
Cikin tana jin kunya har ta saba,
'' UNAIZA kinga mu zamaninmu bamu damu da wadan nan ciye ciye da shaye shayen ba,
Saboda muna da cima da yake gyara mana jiki,
Kinga ku kuwa kunyi watsi da kayan gargajiya a zamanin, kinga zogale nan da kike gani, zamu dafa shi tare da furen shi, sai yayi lugub sannan muyi asellen shi a hada mana da kurji yasha tumatur,
Kina ji sai kuma kabushi ( kabewa) mukan dafa tai tayi lugub tare da danyar gyada shima muci kuma muna samun yin dahuwar kaza akai akai da kifi,
Tana yatsina tana ci,

Yar bado zaki san gata nake miki,''

Inna ta kasance wayyayar uwa ce,
Bata taba daukar sirka a sirka ba a 'ya take dauka
Cikin UNAIZA tana dari dari da ita, har ya zamo ta sake da ita,
Ayanzu abu dayawa QASEEM baya sanin tsakaninsu ,
Shiyasa MAMA take ganin rashin kunyarta yayi yawa.

Tana cewa wai bata da kawaici da yake ita mama mace ce bai sababi, abin magana baya mata kadan
Inna kuwa ce mata take'' itama yata ce tunda tana auran dana. Ai kinga kuwa bazan ji kunyar abinda na haifa ba,''
Bayan ta gama cin ciccibi ne UNAIZA
ta sha ruwa sai ga musa ya shigo''
Maman umaima wai ya naga baki fara kintsa kaya bane?
Na mi kenan fah?
Na barin TANGAZA ki koma SOKOTO mana,

'' kai nakan manta wallahi,
musa nifa tsoron birnin nan nake ji,
Inna tace'' haba 'yata miye abin tsoro a ciki,
Musa ya chafe yace babu,
Ko dai kina tsoron yan gayu ne?

Maman umaima ni yanzu kayanki na nan zaki diba ko kuma yaya za'ayi?
Kai musa ai barinsu zanyi a anan zasuyi amfani idan munzo ai,
Sai dai inaga abinda na samu a sunan yan biyu da kuma dashin da zan dauka Zamu ganganda musai ko da katifa ne sai labule,
Don ance kujerun birni tsada ne dasu,
Inna tace ''a'a bazaki taba kudin kiba, gwanda ki sai abu mai amfani ko abunda zaki ajiye ko ki sayi kiwo ko kayan ajiya ta kaka'a irinsu borkono dasu tsintsiya mai laushi,
Ai wannan hakkinshi ne''
Haba inna miye amfani ina dashi ban taimaka mishi ba, inna kinsan dai yanzu ba wani kudi gareshi ba tunda kwanannan yayi hidimar suna ,
Kuma kinga ba wani kudin ya tara ba,
Kuma ai rufin asirin mune fah inna gaba daya.

Haka ne UNAIXA mazan ne wani sa'in basu da dadi sai ka kare musu bauta ka tausaya musu,
Suna samu zasu nuna maka su masu wayo ne,
Wallahi UNAIZA ba lalle ne wani ya nuna maka samun shiba,
Kinga ke baki adana naki ba,
Shi ya samu yayi kirmisisi,
Shiyasa nake cewa ki adana abunki,''
Inna ni kuwa ba ganin ido ba ai baban umaima bashi da wannan halin, adai zamana da mukai dashi,
Shi mutum ne mai Adalci,wanda bai da sa ido akan abin hannun mace,
Kinga ko dabbobi na sayar na bashi kudinfa kin karba yakeyi,
Kuma inna banga inda akace kar mace ta taimakawa miji ba musammam irinsu baban umaima masu tausayi inna ba ni matar shiba ko yayyenshi ne ya lura yaga basu da abinda zasu ci fa sai ya diba musu, ko makota,
Inna dadin dadawa bai taba raganmu da komai ba,
To amma inaga kar ki dulmiyar da kudin gaba daya , ki samu koda firijin ne ki saya ki samu na kulla kankara ruwan sayi da su sobo,
To inna,
Kinga mike tsaye ki miko min wancan budurwan langa,
Ta shimpida KHALIDA
ta dauko mata cikin girmamawa ta mika mata,
Ta fito da kudade a cikin langar musa irga min wannan ta mika mishi
''Inna dubu Ashirin da uku ne''
Yauwa miko min ukun, to,
Yauwa cire dubu goma ka mikawa UNAIZA,
Kai koma goman idan kaje birnin kasai katifah yar karama ta yan makaranta, nasan zata ishe ka kafin dan uwan naka ya dai dai ta,
Ke kuma wannan goman zaki sayi kayan. Amfanin tsakar gida irinsu kwanon abinci, bukitai dasu pilaitai su cokali,
Kinsan birni ba irin nan bane,
Ta durkusa tayi mata godia,
Haba ba komai ,
Yaushe zaki fara zumuncin arba'in ne?
''Eh inna gobe nake son naje can gabasawa na yini musu,
washe gari kuma naje gidan yayuna,
'' yauwa gwanda kiyi kam kafin ya zo don naji sunyi waya da musa yana cewa ran Alhamisuwa sai shigo ku juya ranar lahadi,

MATAN QUATER'SWhere stories live. Discover now