🏘🏘🏘🏘🏘🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️
MATAN QUATERS✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah Azare
Ummu imanKu bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:ukb696354.kb@gmail.com
EMAIL: Ukb696354@email. Com🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻
3️⃣3️⃣Suka hada baki
gaba dayan su Daya biyu uku aka da ga BILKISU daga gadon da aka mata aikin zuwa gadob da ake tura marassa lafiya,
Daki ne na musamman aka ware mata
Da taimakon majin yatan AKa ciccibeta aka kwantar da ita
akan gadon majin yata,
Suka gargade ta da kada ta motsa kanta kuma kar tA yawaita magana sai bayan awanni shida,
Yin hakan zai iya sabbaba miki ciwon kai mai tsanani
Cewar likitiyar,
yayinda haseena take mata tafinta,
Likitar ta zaro wayarta ta dauki yaran a hoto domin yauce rana ta farko a tarihin kafuwar asibitin da aka cire 'yan uku rus,
Yanzu haka ofishinta zata wuce zatai rubuce rubuce zata tura wa gwabnatin kasar don akwai " HIDAYA " kyauta ta musamman da gwabnatin kasar saudiyya take warewa wa mahaifan da su kansu iyayen baki daya.
Har likitan ta fita sai ta juyo ta sanarwa
HASEENA baban yan ukun ya zama cikin shiri a ko yaushe wakilan gwabnativ za'asu iya neman shi domin tattaunawa, dashi.
HASEENA ta rakata har ofishinta, tana mata godiar kulawa ta musamman tare da taya ta murnan samun nasaran aikin da akayi.Yauwa inna zaku iya shigowa ku da maijegon amma banda hayaniya,Aunty ki shigo kema,
Nan take sanar da baban 'yan uku sakon likitar.
To wai miye hakan yake nufi ? So suke yi su san yaya na kwanta da ita har aka same su ko yaya???HASEENA ta kyalkyalce da dariya kai zaka kashe mutum wallahi
Yoo to miye suke son sani??
Kaga saurara kwantar da hankalinka.
Mu kasan gwabnatin mu mai adalci ce da tausayin talakawa,
Ka gane gwabnati ce zata turo wakilan ta zasu maka tambayoyi.
To akan mi kenan?Eh suna so su san zaka iya rike 'ya'yan ne?
Kana da sana'ar da zaaka iya daukar al'alarsu, na game da ci da sha, da sutura tare da nema musu lfy idan hakan ta taso?
Kai hatta da muhallinka fa sai sunje sun gani,
Idan kana da hali to
Idan babu kuma za'a gina maka gida da wadatattun dakuna
Cike da kayan more rayuwa,
Dadin daadawa suturarsu da kayan sa wansu duk su zasu dauke maka,
Idan kuwa baka aiki ka tabbata zasu baka aiki........To da aiki na ma nikam,
Ekuma nasan ina da wadatar da in sha Allah zan wadatar dasu na ciyar dasu,Kai dai ka saurare su kawai,
SUBHANALLAHI!!!
Aunty B mi nake gani?
Ta ina jinin nan yake zubowa?
Tai maza ta dannan na'uran da aka tanada a kowani daki yayin neman taimakon gaggawa nan da nan ta hau tsuwa tana cewa " AN-NAJDA AN NAJDA""
kafin kiftawar ido likitoci sun cika gadon balkisu,
sun fara bata dauki na gaggauwa.
Yara kuma suna cikin gadajensu na jarirai da aka tanadar musu.A gida nigeria kuwa mata ne sukai dandazo a cikin jerin gidajen zama na kananan ma'aikata na ARKILLA,
Maman DADDY ce akan gaba ita da tawagarta tana jiran isowar mai girma gwabna don tace ba makawa ba wanda ya isa ya hanata ganawa da mai girma!
gefen ta kuwa MUBARAKA CE tana ta wani taunar jin kam,
Ga wani makeken tabarau da ya cika mata rabin fuska
Irin na rikakkun 'yan Bariki,
Rashin hankali cutar mai rayi,!!
Wai hakan MAMAN DADDY ce ta sa ta tayi wannan shigar ko zata ja hankalin gwabnan ko wani na kusa da shi a cewarta kakarsu ta yanke saka,
Tun suna marmarin tsayuwar har suka fara gajiya can sai ga dan sako,
Ya sanar da rashin damar hallatan mai girma gwabna saboda wasu baki da suka halar ce shi.
Tab nan hantar cikin MAMAN HYDAR ta kada
Karfe hudu na rana ake nema ko abin karyawa ba ta yiwa maigidan ba. gashi shi mutum ne mai zuciya,
Kuma ya washi alakarsu da su maman Daddy,
Gaba daya hankalin ta ya tashi gashi gwabnan bai zo ba bare ta sa ran abin zai zo mata da sauki, tunda maman Daddy ta musu Alkawarin kudi mai myawa zasu samu daga wurin shi,
Hankalinta a tashe yake amma da ta ga fuskar MUBARAKA yadda su fandishin da eye shado suka chakube mata a fuska zuffa duk ta jika mata hammata bata san sanda ta dara ba.
Maman Auwal da yake muguwa ce tace
"Aunty Mubaraka gaskiya adon nan bai kamata ya tashi a iska ba ya kamata ki biya ta shagon hoton a baki flAsher don tarihi,"
Ita kuwa M Daddy tsabar ranta ya baci bala'ei ta fara surfawa ga yunwa ga gajiya ga kuma rashin biyar bukata, ke kira mana (T.J ) ki dan rage mana zafi don yau na sa a raina sai naci Dankwaleliyar kaza,
Amma gaskiya unty sai na je gida nayi wanka na ci abinci,
To Allah yasa Daddy ya yi girkin da kyau,
Ummm maman Hydar ya dai naga kamar baki cikin nutsuwa???
Hmmmmm bari dai kawai yau kam sai ta Allah ni da maigidan,
Hmmmmm.
Kar ki bada mata don Allah,
Mu fa isassun mata ne masu 'yanci idan yace zai bude miki ido ba sai ki tsats-tsayar mishi ba,
Ko dama ke baiwa ce??
Ni matan hausawa kuna bani mamaki kun kallafawa ranku tsoron maaza idan zaku canza gwanda ku canza nan tai ta musu famfo da zuga har maman hydar ta ke jin komai ta fanjama fanjam. Domin maganganun shugabarsu yayi mata tasiri.
Haka dai har suka karisa shiyarsu kowa ta kama gabanta,
zuciyar maman hydar ce ta tsinke ganinshi a tsaye a kofar gida.
Fuskar nan kamar wanda akai hatsarin jirgi sama dashi tsabar rashin annuri,
Duk da haka ta matse ta cije kamar Ba komai ta wuce shi zata shige cikin gida, wata irin firgitarciyar tsawa ya daka mata sanda hantar cikinta ta kaada,
Jikinta ya fara rawa,
Ya nuna mata inda ta fito,
Ki koma inda kika fito,
Mi na rage ki dashi da zaki fara yawon siyasa.
Wa yace maka yawon siyasa naje?
wai ita tana son ta baasaar, haka dai rigima ta kara habbaka har ta kai ga ya furta abin da ba'a son,
Kai mata kennan ga rauni ga shagala,
Nan da nan ta zama abin tausayi ta zube gwiwoyi tana mishi magiya
"Don Allah ka rufa min asiri,
Ina kake so naje?
Iyayena basu da karfi inda zan tsuguna ma kasan basu dashi tunda su ma ta kansu suke yi,,,,,
Yanzu kika san haka?
bani da damuwa duk inda zaki je kije ya shiga ya banko kofa,
Kuka take wiwi, taki barin wajen,
Har ya fito zuwa masallacin sallar magariba tana wajen a rakube,
Nan duk wanda yazo wuciwa sai ya gane akwai matSala
A haka aka je aka tseguntawa shugaba sai gata tazo,
abin nema ya samu,yar masu tsegumi tayi cikin ershege
Tai ta mata farfaganda har akai sallan isha ya dawo,
Wai don tsabar iyayi itace mai tsara baban hydar tana bashi hakuri,
YOU ARE READING
MATAN QUATER'S
ActionZAMA NE IRIN NA YAN BARIKI, MATA SUBAR GIDAJEN SU, BA WANKA BARE WANKI SAI GULMA DA SA IDO.