shafi na Arbain da shida

137 22 4
                                    

🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️
MATAN KWATAS

Kulsum Bappah
Azare
       Ummu iman

Ku bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:ukb696354.kb@gmail.com
EMAIL: Ukb696354@email. Com

🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)

_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻

4️⃣6️⃣
  
Wannan shafin sadaukarwa ne ga Margayiya haj Hauwa Abdulkadeer ( mummy Hauwa)
اللهم اغفر لها ورحمها،.

Ba tare da bata lokaci ba suka gano kofar gidansu ISA sulaiman,
Sun same su  a  zaune  shida abokan shi amma kana ganin abokan kasan sai a hankali duk irinsu daya ne amma shi Isa nashi da dama dama ko don yana da ilimi ne bazai yi abinda zai cutar dashi ba,
Ya tashi ya tarbi musa,
" Yaane Babah? An hau mataki na gaba ne ( Mota ) na ganka kazo da mai kafa hudu ne lalle sana'an hoton tana kawo maka citta, ko kawai nima nazo mu cure ne?
Musa yayi murmushi, duba can ga mai motar,
  idan bazaka damu ba mu shiga motar  mana zamu yi wata magana,
ya leka motar yaga mace ce a mazaunin driver tana danne danne wayar ta,
" Badai ka kawo min katin auren ka bane ?? na gan ka da wata Beb,
  Musa da yake ba mai yawan son surutu bane  yace " muje kawai,

'abokanshi suka ce,'" kai wani irin katobara ne zaka yadda ka shiga mota, ko baka san halinda ake ciki bane? na garkuwa da mutane,

Isa ya juya yace musu " ba yawa old friend dina ne"

   Suka mishi chau chau alamar jinjina da yake suna girmama shi tunda yana da sana'a basu rasa na sayan abin afawar,
  Gidan baya suka bude mishi ya shiga shima musan ya shiga,
  Beeba ta ajiyi waya ta juyo suka gaisa,
Ta gama nazarin shi ,
Musa ya gabatar da beeba da yanayin aikinta,
" Yauwa Babah nayi mamaki
Kai da ba sauraron bebs kake yi ba amma sai na ganka da wannan,

   musa Ya  mishi bayanin dalilin zuwan su
Da yake mayen karatu ne
Ya nuna farin cikin shi sosai,

Kana nufin kace zan cigaba da karatuna
Na gama na tallafi iyayena?
Beeba tace" kana da damar hakan;
amma  kuma banga alamar hakan a tattare da kai ba,

Duba da yanayin da na ganka a ciki,

Gaskiya musa abokinka bashi da r'ayin karatu,

Kai aradun Allah ina soo,
Ki tambayi musa mana,
Musa yace"
Eh Isa yanayin da ta ganka. A ciki ne take tunanin baka shirya komawa makaranta ba,
  Don bazai yiwu ga hada karatu da harkan nan ba,

Kaga dama yanzu zata hada ka da kungiyar su ne,
Suna da lauyoyi da zasu kwata maka 'yancinka, zasu je su samu mahaifin yarinyar da tai sanadiyyar korar ka,.dayyy ya tsaya kai da fata a sama maka wata makarantar ko kuma ka koma daga  aji biyu kamar yadda yake kasancewa idan an kama mutum da malpractice ,a mishi canjin course a mai dashi aji biyu,

Ai  Ni musa ko aji daya ne ma a mai dani ina so,

To tunda kana so fah to ba'a hada gudu da suSa duwaiwai,

  Wallahi zan bari ko kuma nace na bari ma daga yanzu,

Ni dama abinda ya jefani. a waNnan halin shine rashin bacci tsabar damuwa da tunanin yaya zanyi shi ya kai ne don DEPRESSION sosai fah ya kamani na fara tunanin ka she kaina,
Tace subhanallahi
To kai ina TAWAKKALIN don Allah?
Tai ta mishi nasiha tare da fahimtar dashi illolin shaye shaye,
Tai ta kawo mishi hadisai,
Jikin shi yayi sanyi, musa yace ba wannan ba ya nuna abokanshi, ya zakayi da wadancan,

MATAN QUATER'SWhere stories live. Discover now