shafi na talatin da biyar

96 15 0
                                    

🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘

MATAN QUATERS

✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah Azare
Ummu iman

Follow me on wattpad
@kulsumbappa facebook: @ukb696354.kb@gmail.com
Gmail Add @ ukb696354@gmail. Com

🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)

_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻

3️⃣5️⃣

Kina nufin kice min ta koma dakinta,
Kuma maman umaima ce ta rakata,
Na shiga uku shikenan ta kwashe sirrin mu
ta fada mata hmmmmm
  Aunty kenan wai wannnan mamar umaima har ce min take wai na fada miki ramin karya kurarre ne,kuma yanzu suka fara hadin kai da maman hydar,
Ke kyale ne don Allah zan ci ubanta a nutse ina mijinta ma aure zai yi na dau Alwashi?
ita da zaman lafiya da samun kwanciyar hankali har abada sai na barbarce kishiyar na sata a hanyata na hanasu zaman lafiya,
Aunty ance yar masu akwai ce ko?
Ehh haka ne yar BAGUDO ce fah;waye bai san shi ba a garin nan,
Ohh Aunty na rasa mi yarinyar ta gani ma a wurin shi ga talauchi.
Ba talauci bane yana da wasu abubuwa a jikin shi da zai iya jan hankali mace dasu.
Ko da yake da fari ne fah ba karamin kyau ne dashi ba, Aunty kenan
  Bari na tashi saloon nake son zuwa ayi min kitson

Don Allah kar ki sa wannnan Mai ruwan kasan; asa miki bakin kawai wancan kalar yakan mai dake kamar wata kabila,
   Hmmmmm Aunty nifa ba don inplanon ya xubar min gashi ba ma da ba ruwa na da gashin doki,
    Yo dama ai ba gashin ne dake sosai ba mubaraka,

********************
Cikin hukunci ubangiji maryama ta santalo yarta mace kamaar an tsaga kara an raba ita da inno (wato kakarta ta wajen uba )
Abin yayiwa inno dadi dama gashi ana son uwarta ga kama kuma a take tace a mai da mata sunanta
Hafsatu " kuma bana son a canza mata suna,
Haba inno fadar sunan kuma haka gatsau ai rashin kunya ne,
To ni dai ban son sunan zamanin nan wai ya ma sunan  takwarata yar gidan zuwaira  nan??
  Wai fanka ko farka?
Kai inno
  FARHA fah,
To ki ji fah miye amfanin sunan don Allah ?
Lah ai mai farin ciki kenan.

Wayar maryama ce ta hau kara
Lahh 'yar halak wai kin ki ambato
  To gulmata ake kenan??
  Eh gulmarki muke yi da inno
Tai mata barka da fatan Allah ya raya zuria,
  In sha Allahu muna nan tafe,
Allah ya kawo ki lafiya yy dinkin mu angama kuwa,?
Bude whatsapp na turo miki,
Wai yaya sunan yarinyar
Sunan inno ce
Kai kai ashe uwata ce  to ko dole na kara shiga kasuwa,

Ko ?

Ki ce FARHA tayi takwara don Allah ace mata FARHANA
Wuuu ga inno yanzu take kashedi wai kar asa mata inkiya
   Bata son farka
Bani ita kawai,  gwanin sha'a wa inno ta gaisa da autarta,
    Suka ce gaba da tadin su har aka zo kan sunan  takwarar tata
  FARKAN a'a rabani itama  takin hafsatun don ubanta ne ya rada mata  shiyasa na kyale amma da ke ce da tuni nasa ba miki,
Haba inno zamani ya canza fah,
Bari na kira ya mustaphan?
   To naga mustaphan ma bai isa ya tsallake umurni na ba,
Ta kashe wayar nan sababi ya dawo kan maryama
Kamar itace ta kar zomon
Maryam dai dake tasan hali ko a jikinta.

********************

   Hanifah kawo min ruwa mai sanyi yau katin mu ne ya kare ga baban umaima suna meeting,
Kari so dakin UNAIZA

  To,

UNAIZA ta watso mata bayani tsaf har maganar da sukai da baba musa,
    Ehhh gaskiya ki kwantar da hankalinki gaskiyar baba musa ne ba'a shaidar mutum musamman a zamanin nan da mutum ya zama abin tsoro, amma kuma alamar karfi ai yana ga mai kiba,
Amma kamar kullum nakan fada miki ki dage da addu'a kina kama sunanta insha Allahu bazata zama mai tayar miki da hankali ba,
Ina yi Aunty insha Allahu zan cigaba
Zan cen kaya kuma ba gazawa kikai ba
Yanzu kudin kin ciro a bankin ne?

MATAN QUATER'SWhere stories live. Discover now