shafi na sha tara

369 41 0
                                    

🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘

MATAN QUATERS

✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah Azare
Ummu iman

Follow me on wattpad
@kulsumbappa facebook: @ukb696354.kb@gmail.com
Gmail Add @ ukb696354@gmail. Com

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻

Na sadaukar da wannan shafin ga HARUNA Admin na beneficial writers ngde sosai,

1⃣9⃣

HASBUNALLAHU WA NI'EMAL WAKIL,
Maryama ta ambata jin haka mustapha ya fito daga daki yace

''Maryama lafya?
Miya faru?

Ka ga zo kaga abinda na gani?

SUBHANALLAH!!
Jini kuma maryama?
Eh
Dama kina jin ciwo ne ko ko?

','ni dai lafiya klau na fito zan sha ruwa fitar da zanyi kawai sai naji mara ta ta murda da kyar na zauna akan kujera shine naji abu na biyowa kafata,,

Shiga ki cire kayan baccin nan muje Asibiti,

Baban Auwal lafiya kuke tsaye chirko chirko?

Lafiya klau maryama ce jini ya balle mata shine nake shirin kaita Asibiti,

Asibiti kuma a wannan talatinin daren bazaka bare gari ya waye ba?

Baka tsoron wani abu ya same ku a hanya?

Maryama kuwa har ta fito sanye da hijabinta da jallabiyar shi hannunta ya karbi rigar yace '' ta koma ta dauko mashi dan makullin shi,

Amma dai maman Asiya kinsan bazan barta haka jini yana zuba ba'asan miye dalilin ba

' to ni dama baban Auwal ina jiye maka fitar dare ne,
da hakurin kayi idan yaso gari na wayewa sai ku tafi,

Ke maryama zo mu tafi,

Ya wuce ya fita maryama tasa kai kenan sai taji maman Auwal tana cewa

Ai wannan cikin sai dai yabi shadda ba dai ya zama mutum ba
Ta fashe da dariya

Maryama ta jiyo ta kalleta,

Bata ce mata kala ba ta wuce suka tafi,

Sun isa Asibitin sunyi sa'a akwai likita ON CALL maza maza ya karbesu yana jin bayanin ya ce ta kwanta ayi scanning a duba aga miye matsaallar,

Likita yace ranka ya dade sakamakon ya nuna ba komai sai dai zai iya kasancewa ko rashin hutu ne,

Ya rubuta magani,
Ya mika mishi

ga wannan ka saya amma da sharudda ka dan nisanceta na kwana biyu,sannan banda aiki mai wahala ,kamar daukar abu mai nauyi, a kiyaye insha Allahu babu abinda zai taba cikin,

Suka koma gida abin mamaki maman Auwal idonta biyu

Yace mata ya naganki a zaune ne?

Eh wallahi dama jiranku nake yi ka dawo nasan ita zasu rike ta,

'' basu riketa ba gata nan mun dawo,
Kuma mi suka ce?

Gata nan tambyeta?

Umm mi suka ce??

Take dabara ta fadowa maryama'' Sunce ya zube gobe naje ayi wankin ciki,

Nan da nan farin ciki da murna suka bayyana mata,

ba maryama ba har mustapha sanda ya gane,

Maryama ta wuce daki ta barta a tsaye daga baya shima ya bita dakin ,

MATAN QUATER'SWhere stories live. Discover now