shafi na sha daya

379 46 0
                                    

🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘

MATAN QUATERS

✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah Azare
Ummu iman

Follow me on wattpad
@kulsumbappa facebook: @ukb696354.kb@gmail.com
Gmail Add @ ukb696354@gmail. Com

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻

بسم الله الرحمن الرحيم

KARIN MAGANAR MU TA YAU

اذا كان الكلام من الفضة فالسكوت من الذهب.

KOMAI DADIN KIDA SHIRU YA FISHI

1⃣1⃣

Alh ismail Bagudo da kanshi ya kawo ziyarar bazata a BAGUDO BUSINESS CENTER & PRINTING PRESS
Hakan ya samo asali ne tun lokacin tsohon manager da yayi RUF DA CIKI DA BABA KE RE akan abinda ake samu a Business center,

Alh samaila bai damu da sa ido akan abinda yake gudana ba, duk da cewa ana yawon kawo mishi SUKA da SARA na manager amma bai dauki kowani irin mataki ba ana shi tunanin hassada ce irin ta mutane da basu kaunar suga ana zaman lafiya,

Ko kuma rashin son cigaba,
Lokaci guda ya fuskanci irin tabargazar da managern shi yayi mishi,
ko wata naura ce ta baci yakan ajiye ta gefe guda,
a haka har ta ida lalacewa a sai wata,
bayan kwana biyu ya saidata,

ba tare da bata lokaci ba ya sallami wannan manager NASHI,

Shiyasa baya cikakken satin biyu bai kawo irin wannan ziyarar ta bazata ba,
Yakan zo su zauna su tattauna matsalolin da yake damun wurin kuma cikin ikon Allah baya wasa nan da nan za'a magance matsalar saboda kubutar da wurin daga dakushewa saboda yana daya daga cikin abinda yake kawo mishi hanyoyin shiga a rayuwar shi bai yarda da cin hakkin wani ba balle kuma hakkin office,

Dukkan ma'aikatan Sun qeve a cikin ofishin chairman don su tattauna kamar yadda aka saba,

Alhamdulillah na fahimci cigaba kashi kashi a cikin wannan masana'anta, naji dadin haka,

kamar kullum bazan fasa fada muku ba,

''AMANA DAYA CE,NA DAUKI AMANATA NA DAN KA MUKU SABODA YARDA,
KU SANI BABU ABINDA YAKE SAURIN KAWOWA MUTUM CIGABA DA DAUKAKA. IRIN RIKO DA AMANA DA KUMA GASKIYA, NA GODE KUMA INA MUKU ALBISHIR DA CEWA YAU RANAR LAHADI SHA BIYAR GA WATA NA KARA MUKU ALBASHI AKAN WANDA NAKE BIYA DA''

Idan akwai mai TSOKACI to bismillah ya mike

Manager *QASEEM* ya mike hanu,
Ba tare da bata lokaci ba aka bashi dama,
_RANKA YA DADE NA TASHI NE DOMIN NA BADA SHAWARA BA TSOKACI BA,
KASANCEWAR BAGUDO ( B .C.&.P.P ) YA SAMU DAUKAKA DA DARAJA A WANNAN JIHA KUMA ALHAMDULILLAH ANA SAMUN CIGABA INAGA MIZAI HANA RANKA YA DADE KA HADE MANA WANNAN FILIN DA YAKE BAYAN MU A SAMAR MANA DA BAGUDO PURE WATER,
DUBA DA YADDA HARKAR RUWA TAKE MATUKAR KAWOWA, TUNDA DOLE DA SHI AKE RAYUWA,
KUMA HANYA CE DA WANNAN MASANA'ANTA ZATA KARA BUNKASA DOMIN ZA'A SAMU KARIN WANDA ZASU NA CIN ABINCI A KARKASHINTA,
NAGODE''
_
Alhamdulillah kafin nace komai miye shawarinku sauran ma'aikata,

Dukkansu suka ce suna tare da manager,

. Alh samaila yace

'' ba tare da bata lokaci ba wannnan shawarar ta karbu da fatan Allah zai tabbatar mana da Alheri insha Allahu zan tuntubi NAFDAC su zo su duba mana wurin,
su kuma bamu dama kafin mu fara shirye shirye,
Kuma ina muku Albishir bazan kawo ma'aikacin ruwa ko daya da hannu na ba,

Cikin ku idan kuna da kanne ko 'ya'yan 'yan uwa ku kawo mana takardunsu insha
Allahu zamu basu aiki,

Sukai ta mishi godia,

MATAN QUATER'SWhere stories live. Discover now