🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️
MATAN KWATASKulsum Bappah
Azare
Ummu imanKu bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:ukb696354.kb@gmail.com
EMAIL: Ukb696354@email. Com🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻
4️⃣3️⃣
Maman inti fah ta faso gari sai dagawa take yiwa makotanta,
Bilkisu har ta gaji da karanta STATUS dinta,
Ba wanda ya bata dariya ma irin " ina kewar ki Aminiyata,,
dayan kuma,
"Aminiyata nayi rashin ki a kusa dani"
Ta karantawa Baba,
Baba mai take yi banda dariya,
Bilkee haka dunia musamman a zamanin nan,mutum ba zai so ka ba; sai don wani abin hannunka,
Wafeeya tace" to miyasa mutane suke haka ne?
Duk da mu nan ba ruwan mu da hakan kowa ma harkar gaban shi yake yi,
Hmmmm to kinsan ita wannnan dinfa hada kai take da bilkisu gashi mijin nata ba laifi yana mata dai dai gwargwado amma sai hangen nesa,.
Bilkisu tace" kuma mijin nata yana fada mata gaskiya fah
Baba tace ba don ma irin zuciyar su bilkin bane bama ai idan wata ce ba abin da zata bataa,
Hmmmm Babah kenan kinsan mutuniyata ce ai....
a'a ke dai samun irin ki sai anbtuna,
Yauwa kunga ta kara saa wani "
Baka sanin mutum masoyinka ne sai ya nisanta da kai"
Wafeeya tayi dariya tace " itama irin mutanen nan ce da basu wasa da STATUS ko miye sai sun rubuta, Tabbas haka maman inti take;
Kinsan miye wafeeya? nifa ina son karanta STATUS din mutane , saboda na kan sha dariya,
Ba wanda suke bani dariya ma irin masu ''' _ZAGE_ _ZAGE_ duk dunia sai tasan kayi fada baka shiri da wannan baka shiri da wancan,,
Yoo Aunty Bilki nima ina kullum abin yana damuna, nace to idan wanda akai domin shi ko domin ta bata gani ba fah, ko ace bata da DATA ,
Baba tasa dariya ina ruwan ~HUHUN MA'A HU~ , ko kuma abinda hausawa suke fadin "~BAN SAN~ ~ANA YIBA KUNU~ ~A WANI GIDA~"
Wafeeya tace tunda ba kamshi yake yi ba,
Ummin su wafeeya ce ta shigoo,
Ya kamata kuje wurin gyaran gashin nan fah?
Kunsa jibi ne kuma da safe ne haflar,
'yan nigeria ma sun sauka don yanzu mukai waya da wafeek yace min jirgin ya sauka,
Wuuu bari na shiga wanka kafin su iso,Wafeeya ta zaburaa ummi dama yanzu nake son idan na gama nazo na same ki,
Kinsan Allah nayi nayi da Aunty bilki kar tasa Atampa a wajen hafla amma ta dage,,
Wai ita bari ta nuna musu AL'ADARTA wai tace ITACE KIMARTA" kin min dai dai Bilkisu, mu hausawa kullum sai kwaikwayo aka san mu dashi,
Kin burge ne,
sa Atampar ki, ki rangada dauri dama ga ki gwana,
Baba tace " haba ummi an kawo kara kuma kin gwasale ta kin goyi a bayan bilki,
Ah toh nima ko don yar gargajiya ce shiyasa nake ganin ba abinda yafi kyau wa bahaushiya irin ta sha Atamfarta Riga da zani tasha daurin kallabinta....... a'a baba zani kuma nifa ban san yaya ake daurin zani bama ,
Bilki tace zaki koya ai ba dai bahaushe zaki auraa ba? Allah yasa ki samu dan gargajiya,
Nikam ba kince min iyayen shi yan AZARE bane?
To kisa a ranki keda atampha kin kulla don na sansu yan boko ne sosai amma basu wasa da gargajiyarsu,
Ta kara zumbura bakin,
*********************
inno ta watsa mata wani mummunan kallo,
Ta shige abinta
Maman Auwal yankewar zuciyarta biyu ne, ga tsagoron masifa da take gani a kwayar idon inno ga canza war da maryama tayi sai shike take kamar zarahh a cikin taurari ta cika ta baatse,
Ga abinda boka ya bata,
ta yar yafa a dakin maryama kafin ta dawo,
Eto gashi sun mata ba zata yanzu yaya zata yi?Maman Auwal ji take kamar ta koma gidan maman daddy ta zauna domin tasan yau sai ta kwashi kashinta a hannun, duk da tasan bata da damuwa da mustapha ta gama rufe mishi baki dama uwarsa ce tafi karfinta........muryar maman daddy taji tana ce mata" mutuniyar miye abin ye???
Kamar kinsan tunanin da nike kenan,
Ke don Allah kiyi mirsisi ki kyaleta nasan sababi ne zaki sha kuma kin saba sai mi? Ke da B Auwal dai nan gani nan bari FUREN TUNFAFIYA
ta dan karfafa mata gwiwa,
Suka rabu, amma zuciyarta na bugawa akai akai
Inno ce tasa mustapha a gaba tana surfe shi ,"ka ga gidan nan don Allah kamar gidan kabilu tsabar kazanta ka ga yadda ka koma kamar wani karmami ba dadin gani,
YOU ARE READING
MATAN QUATER'S
ActionZAMA NE IRIN NA YAN BARIKI, MATA SUBAR GIDAJEN SU, BA WANKA BARE WANKI SAI GULMA DA SA IDO.