shafi na talatin da takwas

103 14 1
                                    

🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️
MATAN KWATAS

Kulsum Bappah
Azare
Ummu iman

Ku bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:ukb696354.kb@gmail.com
EMAIL: Ukb696354@email. Com

🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)

_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻

3️⃣8️⃣

INNO A ARKILLA

Bata sha wahala sosai ba da yake da bello suka taho,
Haba murna a wajen su ba'a magana babban farin cikin inno yadda taga unaiza ta murje ta goge bata sa tashin hankalin karin auren kasimu a ranta ba ga jikokinta fess tunda ta sauka umaima ta makale mata,
Abinda ya bata mamaki bai wuce maganar da umaiman tayi mata ba,
Miya sa kika dawo da Baffah Bello kullum sai yana zare mana idanu yana rankwashe na wai ina da gwala gwalan idon irin na mamana,
Kaka miye mayu?
Mayu sune masu manyan idanu?
Ke haba duk kin cikata da surutu don Allah ki barta ta huta mana,
Kin fiye magana wallahi maza zo ki dauki zige-gen maman su hanifa ki kai mata kice mata kaka ta iso lafiya,
Daudawa ce mai kyau irin ta BUNGUDU mai zaki da kamshi, sai su kubewa kuka kifi banda harda man shanu,
Kai unaiza kayan bai mata yawa ba??
Ki bawa Bello mana ai ya mata yawa,
Uhmmmm ban ki bama idAn musa ya dawo Bello kam bai zuwa gidan
To bata marar nauyin ta kai mata,
Hala ita ce maman daddy??
'a'a wannan fa matar faruku ne dan Dauran nan wacce nake baki labarin tana min sare sare kayan sayarwa,
Ohooo kice min wanda sukai makaranta tare,
" Kwarai itace"
To shi kuma wannan wa ya samu wai maman daddy tun tasowar mu naji yake mata waya,
Uhmmm irin mutanen shine.
Kar ki damu kita hakuri dasu,dama ba'a bata girma haka siddan ba sai an samu kalubale ta kowacce irin siga ki xama mai hakuri yanzu ne zaki kara sanin masoyinki da makiyinki, kar ki kuskura ki zubda girman ki da martabanki, ki tafi akan halayenki da kika taso dAshi ki kara jajircewa shi kanshi kasimun sai kinyi hakuri don ba waliyyin Allah bane ba kuma ba mahasumi bane,

Ba ruwan ki da daukar zugar kawaye ba ruwanki da hidimar kawaye ba ruwan ki da makota duk da cewa ba sabo kikai dasu ba amma ki kara dagewa yanzu ne zaki gamu da mai sonki da marar sonki,
Kar ki ga zai auro 'yar manya sai kin so ki zubda kanki ki bada kanki,
Ki rike girmanki kar ki kuskura kiiyi abinda zata raina ki, kice babba kice kika san waye kasimu, Kinsan abinda yake so kinsan wanda baya so, kuma abinda kike so yayi shi zai yi matukar kika rike kanki,
Ta zaro takarda ga shi wannan addu'o'i ne nasa a rubuta miki kina karantawa, in sha Allah indai kina yi ba zai ga ya ke ba kullum ganin ki zai yi kamar wata daren sha biyar hungo amshi karanta.
Tai murmushi tasa hannu ta karba ta duba taka dai addua ce da gaske ta sanya kauna da nutsuwa tsaKanin ma'aurata,
A ina kika samu wannan inno?
Saifullahi dan kawata da yayi a karatu a jami'ar musulunci ta madina shi naasa rubuta miki,
Tai ta godiya iya kauna kenan da inno zata nuna mata Allah sarki ko mahaifiyarta nada rai iya abinda zatai mata kenan,
Bata yanke daa al'amarin inno ba sai da ta ga kaya hilimi guda a gabanta,
Dauki wannan ki dunka wa umaima da khaleeda wannnan leshin da atampar ma naki ne,
Yauwa ki duba rigar nan ko ta miki tsarabar saifullahi ne ya kawo mana ni da mamar shi amma na gwada naga ya min yawa kuma na zamani ne wannan duwatsun sai ku yara,
Haba unaiza sai murna wallahi wancan satin naga irinsu a Algazaru amma kinsan mai tsada ce fah sosai,
Eh to yar nan abu daga garin ma'aiki kam ai dole yayi tsada,
Dauko wancan galan din tsumi ne dan chadi kurba ki ji dandanon shi,
to da yake unaizar ta saba kuma ta dauke ta tamkar uwarta ko a jikinta kai ai kuwa ya sha hadi,
Ki adana shi a firiji,
Wannnan kuma chukwi ne,
Ga shi malam yace a baki dubu goman nan kiiyi dinki,
Kai Allah sarki Allah ya biya ya jikan mahaifaa,
Nagode sosai,
Ta kintsa na kintsawa zannuwa da kudin ta ajiye sai kasimu ya dawo ta nuna mishi,
Chan ma shagon hoto na Baba musa wata amarya da ango sun zo hoton aure yaga wata shadda da aka hada da lace ya mishi kyau bai yi kasa a gwiwa ba ya tambayeta inda akai mata dinki,
Ta mika mishi katin shagon a ma'ajiyarta amma tace mishi haka ta saaya a dinke sai dai idan yaje shagon zai gansu iri da kala,wanda yake so,
Yana rufe shago kuwa bai zarce ko ina ba sai kasuwar shehu shagari yabi kwatancen tsab ya gane wurin,
Wai har ya rasa kalan da zai tsaba mata chan ya hango wata ruwan sararin samania da aka mata ratsi da leshi ruwan toka,
Abinda ya kara burgeshi harda na tsaran umaima a gefe,
Ya ja kaya gaskiya don da yayi niyar saya mata zannuwa kamar kala uku haka masu kyau amma yasan wannan ko ina ne zata shiga dasu da yuyuyu gwanda daya kwakwkwara,
Nan shima ya zabi shadda iri daya da khaleed yace an dinka musu zuwa wani sati,
ya ciro ATM ya mika musu suka zari kudinsu da zummar nasu sai yazo karban dinki zai basu kuma sun amince,

MATAN QUATER'SWhere stories live. Discover now