shafi na Ashirin da shida

92 14 0
                                    

🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘

MATAN QUATERS

✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah Azare
Ummu iman

Follow me on wattpad
@kulsumbappa facebook: @ukb696354.kb@gmail.com
Gmail Add @ ukb696354@gmail. Com

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻

بسم الله الرحمن الرحيم

2⃣6⃣

YAA SALAAAAM!
faduwa yayi,
SUJUDUSH-SHUKRI ya yi wa Allah madaukakin sarki,
Ya kara mikawa likitan hannu,
Bilkeesu kuwa godia take ta yi a zuciyarta,

lalle hukuncin ubangiji ya wuce yadda ake tsammanin,
Allah mai yin yadda yaso a lokacin da yaso,
Ta runtsa idanuwanta da ta tuno irin kalubalen da take fuskanta a wajen dangin mijinta da makotanta,
Ta tuna yadda yayar HABEEB kullum bata da zancen da ya wuce yayi aure don ya samu MAGAJI,
Amma ya yi KIRMISISI yace lokaci ne,

Gashi cikin hukuncin ubangiji Allah ya kawo lokacin,
Sunyi kusan kwana biyar ana jinya, ko kwakwkwaran motsi tayi sai ya nemi dalili,

Ya tambayeta mi take sha'awar ci,
Mirmushi bilki tayi tace '' bana bukatar komai,
Yayi ta mata magiya,
tace'' bari tai maganinshi da takurin da yake mata,

GORUBA nake son ci,

Mi sauki ne, bani minti arba'in

Hahhhhaa kasan nan ba nijeria bane?

Ina ruwanki ????
Ya fice abinshi tai dariya

Shi ko bai zarce ko ina ba sai SHAHARA MANSOOR yasan anan ne kawai zai samu kayan cii ma irinta hausawa,

Yayi sa'a kuwa ya samu a hannun wata TAKARU,
abin haushen
Ma abinda a nijeria bai fi NAIRA biyar ba
Amma anan har RIYAL Ashirin ya jido mata kusan guda Goma
Ya samu tsire da yasha kuli kuli ya saya mata
A hanyar shi ta dawo wa ne ya ya ga wani Allon talla wurin sayarda kayan yara,( SUPER MARKET) da ya shiga yayi ta jidan kayan jarirai na maza dana mata har abin dariya,

BILKI na can tana tunanin mai ya hanashi dawowa , shi da yace bazai wuce minti Arbain ba,

ta tashi ta hau leqe leqe ta taga,
fararen fata ne kawai take gani suna kaiwa da kawowa, sai kuma hadiman masallacin mai ALFARMAA suna ta share share da goge goge abin mamaki yake bata basu gajiya,
masu wankewa suna yi,motar mopping na bi ga kuma kamshi,
Allah kenan!!!
Ta shagalta matuka ta zurfafa cikin tunanin buwayar Allah, bata ji shigowarsa ba ma sai qamshin goruba taji a hancinta, tana juyuwa abin mamaki sai ta ganshi da goruba da tsire,
kamshin tsiren da ya bugeta bata san lokacin da ta ruga tayi makewayi ba sai amai nan da nan ta fita hayyacinta,
hankalin shi ya tashi,
ya kira likita yake sanar dashi,
Ya mishi dariya kar ka damu al'adace ta masu ciki,
inaga ranta ne bai so.

Ya diba ya kai madafi ya ajiye abin haushin ma harda goruba da ya sayo tace bata so,

Haka dai ba don yaso ba ya zubar da goruban a dust bin,

Can taga manyan ledoji akan gadon su, hankalinta ya koma kan su, taje ta bude
TAB INA RUWAN GANDOOKI,
kai tayi ta azizita kyan kayan,
Ranshi sai ya mishi sanyi domin ya dan shaka gaskiya ,

Saboda da kanta tace tana son cin goruba,
Sanda yasha wahala ya sayo kuma tace bata so, ( ba'a sabin ba )

Nan ya zo ya dauki dayar ledar ya zazzage akan gado,

kai masoyina baasu yi yawa ba?

Mi ma aka yi?

Ki kara warwarewa zamu haura akwai inda naga kayan babies , sai kuma cikin BIN DAWOOD suma akwai kayayaa kin LUDA( jarirai ).

MATAN QUATER'SWhere stories live. Discover now