shafi na Arbain da tara

108 17 0
                                    

🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️
MATAN KWATAS

Kulsum Bappah
Azare
       Ummu iman

Ku bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:ukb696354.kb@gmail.com
EMAIL: Ukb696354@email. Com

🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)

_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻

4️⃣9️⃣

SURAYYA DEE  ina miki murnar kammala littafin HALIN RAYUWA,sannu da kokari,
   UMMU ASGAR kema ina miki murnan fara labari mai kayatarwa KADDARAR  MUTUM
Allah yasa a gama lafiya
.

Yakai karfe biyun dare idon shi biyu yana ta sake sake,

To dama yaudaran shi iyayenta sukayi kenan ?
sun san ba ta da lafiya suka ha'ince shi,
Ko da yake wannan kan ma MAR'ATUL MURTAJILAH ce ( MATA MAZA)
Wa zai fara tunkara da wannan matsalar iyayenta ko ita,
Shin tasan haka taken ne,
Ko kuwa?
Kai ina ganin suna sane hala shiyasa ma sukai ta haɗani da sha tara ta arziki,

Idan kuwa haka ne sunci amanata,
Ba kadan ba,
Ina ruwa na  da dukiyarsu,

Wato na rufa musu asiri,
Ya ja dogon tsukAa

Ya waiga yaga tana bacci a nutse ko a jikinta,
  Haka dai yayi ta saƙe saƙe
Ga tafiya a gaban shi,
Yanzu yace zai tafi wajen unaiza ta kawar mishi da bukata zata  fahimci akwai damuwa

   Ya kara jan tsaki sai ya lura yaga kamar tana murmushi da kyar ya kwanta bacci ya dauke shi. 
Da asuba ya tashi musa ya kai shi tasha,
Bayan dawowar shine Bello ke tambayar musan ina yaya kasimu yaje?
 
    Abuja ya tafi,
Mi ya tafi yi kenan?
Allahu a'alamu amma ka kira shi mana kaji,
A'a nami??
Ya cigaba da baccin shi
Shi kuwa ya hau shirin fita,

Inno naga kina ta shirye shirye ba dai kinyi azama bane?
Ai kuwa maryama kin tuna akwai bikin 'yar wajen aminin mijinki satin nan,
 
a'a aha! Ai kuwa na sha'afahh
    Kuma ya kamata ace dayar ku taje,

Ehh inaga maman Auwal ce ya kamata taje ,
  
Uhmmmm, gani kikai tana son zuwan?wai ace mutum da mahaifar shi amma yana gudunta, duk don gudun tsoron talauci,
Amma tsabar rashin hankali bazata rungumi gidan mijin tan ba sai gantali,

"Inno wata ran zata daina de,
  Kar ma ta daina duniya ce ta fi gaba ruwa jiima,
Kema na dawo kanki na kyale ki ne naga gudun ruwanki, tunda muka dawo kin ki komawa dakinki,
Miye dalilinki????
   Gudun shi kike ne ko mi???
  Gabanta yayi Rassss,
   Ba haka bane inno------- to miye?
    Tsoro nake inno kinga yaki sam mu tsara taxarar iyalin nan.......
" La ha'ila ha illallahu muhammada salallahu alaihi wa sallam.
Tazaran haihuwa maryamaaa???na banu,,!!
    Haba ke kuwa a wani dalili kike son yi ??
    a matsayin kina wahala idan kika zo haihuwa ko kuma shi yace miki bashi da halin da zai kula da 'ya'yan shi,
   Eyyeh maryama ??
" a'a ba haka bane inno tsoron gwarnai nake kawai,
   To kar na kara ji wannnan maganar daga bakin ki,,

    Yahudawa sun kawo muku abu kun runguma ance maki lafiya ce,
Su yi ta cutar da ku suna illata muku lafiyarku amma tsabar dakikanci irin na malam bahaushe kun ara kun yafaaa kuna jayayya da fadin Allah ,
  "" Kada ku kashe 'ya'yanku saboda tsoron  talauce, mu ke axurtaku.......""
   a haba shiyasa bini bini kike sauraran shin ALBISHIRINKU, na garin BAKESO
To ahir ba gwarnai ba ko yau kika haihu gobe ki karA muna soo,
    Mustapha ya shigo,
Ya ga inno nata sababi,

A zuciar shi yace inno iyayen jidali yau kuma har 'yar gwal dintan ma,

  Inno lafiya kuwa??

Kalau nake kawai magana muke akan tazaran haihuwa,
    Ya samu wuri ya zauna

MATAN QUATER'SWhere stories live. Discover now