shafi na takwas

419 52 4
                                    

🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘
 
MATAN QUATERS

✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
     Kulsum Bappah Azare
       Ummu iman

Follow me on wattpad
@kulsumbappa facebook: @ukb696354.kb@gmail.com
Gmail Add @ ukb696354@gmail. Com

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, Outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻

0⃣8⃣

ليس الخبر كالمعاينة
GANI YA KORI  JI

A gaskiya wannan hadin kan naku yayi ai haka yana da kyau,
Ba matsala sha kuruminki,
Kuma na gode,

amma inane gidan maman hanipa ne kam ta aiko min da abinci, kin ganshi can a kwando,

Hmmmmmm
lalle wannan matar ne har ta aiko miki abinci?
lalle kin cire tutah!
   Ko?
eh mana matar da bata kula kowa a unguwar nan,
Haba?

ai bata harka da kowa a QUATER'S dinnan,
'' to miyasa?
Na shige su;

a'a gani take mu duk jahilai ne,
tunda bamuyi jami'a munyi bautar kasa ba, tsaganinmu da ita mukam sai kallo, hakan ma na banza shiyasa mu kuma muka ware kanmu a matsayin mu na wanda take kyama muke  hidimar mu da ita,
  UNAIZA dai sauraronta take yi,ta nazarin kalaman maman daddy da kuma abinda baban umaina yace mata
'' mata ce mai mutunci mai sanin ya kamata''
amma kuma taji akasin hakan a wurin yar unguwar,
Hmmmm kina nazari ko?
a'a
ai idan kika ganta ma zakiyi tsammanin  mutuniyar kirki ce,
Idan taga ke ba kalar ta bace  ta watsar da ke,
Ikon Allah,
Maman daddy taci gaba Allah ya hore mata girman kai,
Kuma gani take yi kamar duk duniya babu wanda tayi sa'ar miji sai ita,
Ke!!
Allah kuwa ke bari dai kiga na shiga gida,
Idan wani abin ma sai matan QUATER'S sun shigo
      to ba damuwa ina sauraronku

Baban umaima suka  dawo katifar babban gado  ya sayo da fridge da yake falon akwai tyles bashi da damuwar leda ko kafet musa ya gaji tili$

''to rago yaya akayi na ganka haka?
Aunty na gaji wallahi,
Ayya sannu   da gajiya  tunda muka iso ba hutu,
Gashi yanzu za'a kira sallar magariba,
Wallahi bari naje nasa katifar a daki sai na shimpida zanin gadon kafin a kira sallar ko zan samu ma nayi wankan?

To
  Ta shigar da kayayyakin amfani madafi su kayan abinci risho kalanzir omo harda soson wanke tukunya  ta killace su tsaf,
   Ta wanke kwanukan maman hanifa,. Da zummar idan akayi magariba zata bawa musa ya kai,
  Ana kabbara sallah QASEEMU ya kira MUSA suka tafi masallaci,

Da kyar UNAIZA ta samu tayi sallar magariba saboda KHALID da KHALIDA sai kuka suke mata, bayan da ta idar ne tace laifi na ne ban baku bakin zanyi tafiya ba

To nan gidanku ne ba bakunta muka zo ba,

Umaima mai shekara biyar tace mama keda wa kike magana?

da kannenki,

ana sallar isha suka dawo daga masallaci  sun samu yan biyu suna ta kuka
wai UNAIZA miya same su ne?.
wallahi baban umaima ban sani ba ko gajiya ne,
can musa yace

'' kin kuwa fada musu zaku yi tafiya?

Ina kuwa sai yanzu abin ya fado min, nake fada musu,

QASEEM yace musu''  wai musa har kai rike chamfin ne dakai,?.

yo yaya ba chamfi gaskiya ce,
ai ko unguwa ce ka fita baka fada musu ba sun ringa kuka kenan,
Amma matukar ka basu baki kafin fitar
lafiya kalau za'a fita a dawo,

Mtswwww to nidai ban yarda ba musa zaman gida ne kaima ya sa kayi riko da wannan chamfe chamfen,

   yauwa musa don Allah ga kwanukan makociyar mu nan zo ka kai mata,

MATAN QUATER'SWhere stories live. Discover now