🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️
MATAN KWATASKulsum Bappah
Azare
Ummu imanKu bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:ukb696354.kb@gmail.com
EMAIL: Ukb696354@email. Com🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻
Wannan shafin sadaukarwa ne na musamman
Wa Amarya
HAUWA'U BAPPAH AZARE ( UMAIMA)
DA
ANGONTA
SALMAN MUSA SHAFA
( HAUSAL 2022 👩❤️👨 )
ALLAH YA SANYA ALHERI YA BASU HAKURIN ZAMA🅿️
5️⃣5️⃣
Zubaida ce kwance saman gadonta na Alfarma samfurin kirar jordan tsadadde ne amma bashi da wani tarkace ko rakacaniya da zai rage wa mai kallo sha'awar kallon,
fari ne kal yasha lallausan kayan shimfidu ruwan bulu amma bulun mai duhu wanda turawa suke kira da " navy Blue ko Blue Black " tana ta karanto "wasikar jaki" wato tunani,
Tare da nazarin halayya irinta mijinta ( kasimu) a a farkon lamarin tayi tunanin ko so yake ta huta daga gajiyar biiki amma taga abin ya wuce wannan tunanin ,
Ta kara juyawa ta daya hannun ta yanke shawara a ranta cewa kawaici ne kawai yake damun shi,
Sautin NANCY AQRAM cikin zazzakar muryarta da take rero wakar NAZRAL OUYUN ta yanke mata tunani,
ta lalubo wayarta da take kasan filonta,Assalamu Alaikum ya Ammi!!!
Gaisuwa ta wanzu a tsakaninsu cikin girma mawa tare da tambayar babanta,
Ta can bangaren kuma Amminta ce itama tana tambayar maigidan da abokiyar zamanta tare da yaranta," Zubaidatu yaya zamantakewar taki take da ke da abokiyar zamanki? Ina fatan ba matsala??
Ai Ammi kamar yadda kika fada tun farko ne gaskiya bata da matsala a yanzu dai;amma ban san nan gaba ba, duk da ba fatan matsalar ake yi ba.
Ammi ta tare ta da cewa " Zannu lil mu'uminina khaira"
wato kayi ma wa mumini tsammanin Alkhairi"Kamar yadda na ganta mai far far din nan zai yi wuya ta sauya,
To wai Ammi miyasa ko da yaushe kike cewa mutum mai far far matsalar shi kadan ce??
Ehh a mafiya yawan lokuta mutani masu far far ko surutu ko fada basu fiye matsala ba; kuma zai yi wuya ki same su da munafurci ko nunkufurci saboda komai nashi a bayyane yake kina mishi ba dai dai ba zai nuna miki ko ya furta ko yayi fishi ko ma ya fito gaba da gaba yace an mishi ba dai dai ba,kuma irinsu sunfi dadin sha'ani da dadin zama sabanin mutum mai shiru yana da wuyar sha'ani ba'a faye gani inda ya sa gaba Ba, saboda ko bata mishi rai akayi ba zaai nuna ba ma balle mutum yasan ya bata mishi ya gyara,
Kuma kinga Allah ne masani "Allamul guyub" masanin gaibu shi yasan abinda yake boyewa a zuciyarshi,
To sau tari gwanda zama da mai magana,
ammafa wannan duk hasashe ne ba rubutatac-ce bani,
Wai shin zubaida ina umaima da kannenta ne bani jin duriyarsu idaan muna waya ko baki sake musu fuska ne,?
Ko kina cikin jerin matan da za'a so uba amma za'a ki 'ya'yanshi??Haba Ammi sun tai islamiya ne, kawwai dai rashin dace ake yi yawanci idan muna wayar basu nan.
Kuma nima muna gama wayar zan shiga na duba mamansu kinsan bata ji dadi ba,
"" Ash-sha subhanallahi Allah ya bata lafiya ki gaisheta kin hada mu idan kin karisa,
Kuma ki tambaya mana kasimun idan an samu hutun karshen mako yan biyu su zo mana kwana biyu,
In sha Allahu Ammi agaida gidaLaure tana ta fama da matsalar ciki,
Laulayi ya taso ta a gaba bata son cin komai ga amai ga yawu,
Ita yawun ma yafi daga mata hankali,
Domin shi aman ba kasafai take yiba sai ta jiyu kamshin girki, ko kuma ta ji kamshin turaren Imran ba abinda ta tsana irin taji kamshin turaren nan,
a saboda haka ne gaba daya ya koma wajen maman salimah din din din ya sauke makaman yakin shi akanta,
Bai so diramar ta kare da wuri ba,
Ya so ace ya koya mata hankali sosai ; ba wai don baya sonta ba sai don ya koya mata hankali ta gane Annabi ya faku,
Duk da cewa ya fahimci bata ma san yana yi ba duk bakin cikin da yake guma mata ko a jikinta
Allah ya hore mata juriya da Kau da kai ba kowani abu bane yake dagula mata lissafi ba,
Takan dauki komai da sauki musamman da ta fahimci akwai ganganci a cikin hidimar shi,
dan sh-sharewar da take yiwa lauren ma ta daina don yanzu tausayi ma take bata tsabar yadda taga take wahala;
Itama ta wahala a cikin salima amma ba kamar na lauratu ba,
abinda ya kara bawa imran mamaki yadda yaga maman salima bata da lokacin kanta sai na farantawa laure duk wani abinda take so shi akeyi
YOU ARE READING
MATAN QUATER'S
ActionZAMA NE IRIN NA YAN BARIKI, MATA SUBAR GIDAJEN SU, BA WANKA BARE WANKI SAI GULMA DA SA IDO.