🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘لق
🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻Fati Nijar ''
# uwa mai gyara yarta nayi godiya gare ki mahaifiyata##Sadaukar wa ne ga
Haj jummai Bappah
Azare
Allah ya ja kwana tare da karuwar imani,0⃣1⃣
( GARIN SOKOTO)
Gari ne da tarihi bazai taba mantawa dashi ba,
Mazauna garin sun kasance suna da wayewa irin ta addini hakan ya samo asali ne daga tushe
Duba da yadda ya kasance mahaifa ta FAKIHIN malami shehun shehuna, shehu usmanu bini fodio dan salihu,
Dan haruna dan muhamMadu dan gurudu dan jibbo dan muhammad sambo,
Dan Ayuba, dan ma'asaran dan baba,dan musa jakoluFakihin malamin ya kasance ya fito daga tsatson fulanin na kabilar *FUTA TORO* da suka fito daga *HIJAZZ*
Suka gangaro suka zauna a kasar gobir
Aka haifi shaikh usman
Ya tashi cikin ilimin Islama mahaifanshi suna koyar dashi karatu
Na littattafan addini ,
Ya tashi cikin gwagwarmayar ganin musulunci ya kafu
Ya kubutar da mutane daga duhun zalunci zuwa haskeN islama,
Bai cimma burinshi ba sai da akayi yake yake
Ya rabawa daliban shi Tuta ,
Ya sallame sU suka nufi garuruwansu da wannan TUTAR
Daga cikin Almajiranshi akwai
Yakubun Bauchi, modibbo Adama: Adamawa,
Malam zaki: Azare
Buba yero: gombe
Mal dunde nufe, ummarun dallaje: katsina
Mal musa :zariada sauransu,
A dalilin haka ne sokoto ta zama mazaunar sarakunan musulunci,
~SEAT OF THE CALIPHATE~
Sokoto ta samu yancin zama Jiha a shekara ta 1975
Gari ne mai tsananin zafi idan lokacin zafi yayi yakan kai dikon digiri talatin da tara zuwa arba'in 39°c - 40°c
Haka zalika idan lokacin sanyi ne shima ba sauki
Saboda rairayi ne sahara ne,TANGAZA dayace daga kananan hukumokin da yake kewaye da birnin shehu,
UNAIZA tana zaune a tsakar gida tana tankade garin tuwo sai ga ALQASEEM ya shigo fuskar shi dauke da farin ciki,Àssalamu Alaikum,
Wa'alaikumus salam,
a'a har ka dawo kenan?
Eh
Ya zauna a gefen tabarmar, ta debo ruwa a kwanon sha. Ta kawo mai ya karba ya shanye kuwa tas saboda ana tsananin rana,
Mai gida yau daga ganin huskar ka akwai abinda ya sanyaka nishadi,Ke dai bari kawai ,
Tayani murna na samu chanjin aiki zuwa birni, kai Alhamdulillah kace zamu zama matan birni ikon Allah kenan,
Eh amma sai naje na gano tukunna, ina tsammanin zasu bamu gidajen zama a cikin jerin gidajen ma'aikatan gwamnatin tarayya, To Allah yasa mu dace
Kuma can dinma koyarwa ne? a'a
Ai na bar harkar malunta ke ko shekara biyar ina harkan malunta
Teacher uban karatu,
Eh yanzu kam ma'aikaci ne ni cikakke na gwamnatin tarayya karkashin ma'akatar sadarwa kinga yanzu zan koma asalin layi na kenan na INFORMATION TECHNOLOGY,
Alhamdulillah Allah ya kara dauka ka da cigaba,
Wai yau miyar mi kike mana ne?
Yau alaiyaho da sure nake mana.
Kin sa kabushi ? ( kabewa)Eh
Da sauran man shanun nan kuwa?
Eh da sauran ragowa,
Madalla
Bari na tashi na shiga zan huta kahin nan kin ida abinci,
Ina son shiga cikin gida na sanar musu,
Ta mike da kyar tana dingisa kafar ta,
Baban umaima nauyi cikin ga yake min,
Wayassani ko tawaye ne ( tagwaye)?
kai baban umaima ka tausaya min mana,
Dayan ma yaya munka kare dashi bare biyu,
Allah dai ya raba lahiya'' tace amin,Wai shin ina umaima ta tai ne?. Zannura ce ta tai da ita kofar su,
Kinsan bani son yawo ko,
Haba baban umaima ai naga gidan wanka ne,
Duk da haka UNAIZA wallahi ban son yaro ya ringa shige shigen ga a haka suke debo wata irin tarbiyar kinfa san gidan yaya akwai matsalar rashin tarbiya na kasa baya ganin girman na sama dashi,
To za'a kiyaye.
YOU ARE READING
MATAN QUATER'S
ActionZAMA NE IRIN NA YAN BARIKI, MATA SUBAR GIDAJEN SU, BA WANKA BARE WANKI SAI GULMA DA SA IDO.