shafi na tara

399 48 0
                                    

🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘
 
MATAN QUATERS

✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
     Kulsum Bappah Azare
       Ummu iman

Follow me on wattpad
@kulsumbappa facebook: @ukb696354.kb@gmail.com
Gmail Add @ ukb696354@gmail. Com

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻

مهما طال اليل سيظهر الفجر.
  
Komai nisan dare gari zai waye

0⃣9⃣

  ....... Musa na tsaye a kofar gida ya fito shan iska,
abinka da mutum gida bai saba da zaman gidan ba
  Kwatsam sai yaga wulgawarta kuma lalle ya fahimci itace matar da suka shigo gidansu dazu,

  Yanayin furucin da take yi kamar ba mai kwakwalwa ba,
Ana shi tunanin bai ganta tare da kowa ba amma yaji tana surutai marassa kan gado,

Kai yanayin tafiyar ma ba ta masu nutsuwa bane,
Amma a hakan suke kawo sukar wata
Ina!
Ba matar girki bace

   Innalillahi wa inna ilaihir rajiun!!!
  Maman daddy lafiya??
'' na fada muku,ku ka min musu jikina ya bani wallahi jikina ya bani Allah ya tsinewa inna dije ke hadiza ma yau,
 
Ke maman Auwal wai miye haka don Allah dai dai ta numfashin ki,

  Kiga kina ta uban haki,

   Baban Auwal ya aure tsohuwar masoyiyarsa,

Eyyeh!!!
Ban gane mi kike nufi ba?
       Nace miki baban Auwal tafiyar da yayi. Shema Aure suka mishi da tsohuwar budurwarshi,

  ''Babban bala'ie!!!
  Aure maman Auwal?
innalillahi wa inna
ilaihir rajiun yau wannan labarin da mi yayi kama ni zainabu?
Yau kuma larabar ta muce,

Kinga zauna kwantar da hankalinki,
Bani nutsuwarki
Shi yake fada miki yayi aure??
   Tayi yake wanda hausawa suka ce yafi kuka ciwo

Zanjen da nake miki Amarya tana cikin gidana

Eyyeh DURUN UWATA INJI MATSORACI
da gaske?
  Ke na shigo su,

Maman daddy miye abinyi??

Don Allah miye abinyi shawarar ki nake jira,
Zuciyata tana bani kawai naje na tattara kayana na kara gaba don wannan bakar ranar bazan iya budar ido nagan shi tare da wata ba don zan iya kashe ta

a'a babu inda zaki kuma babu zancen kisa zama daram haba AI FADUWAR GABA ASARAR NAMIJI,

Asiya har akwai matar da zata tsorata ki,

  Karya ce sam ki nutsu idan muka sata a gaba don ubanta da kafarata zata koma inda ta fito,

Maman Auwal kar ki bani kunya mana kina babbar mace mai yanci wanda mijin ma ya barki ya kyale balle wata matar shi

  yanzu maman daddy mi kike gani don wallahi bazan bari ko numfashin kirki tana shaka ba

Ai wannan mai sauki ne yanzu dai ki koma gidanki

Ki ga da me tazo kinsan yanzu haka sun bata abinda zata barbada a gidan saboda ta mallake ku,
Kuma kin taho kin barta,

    Zan shigo zuwa yamma,
amma abinda nake so ki nitsu da farko,

Shegiya kinga kyawunta kuwa. Kamar Aljana take tsabar kyau,
  Mi sauki ne

Ki dai tafi
zamu bata fuskar ai,
  Ta fice sai gida.
dama maman daddy Allah Allah take ta tafi saboda sunyi waya T.J  zai zo.

. maman hanifa ce da kanta ta shigo da kwandon jiya a hanunta shiyasa UNAIZA tai saurin ganeta cikin mutunci da girmamawa ta karbi kwandon
Aunty sannu da shigowa,

MATAN QUATER'SWhere stories live. Discover now