shafi na hamsin

114 27 1
                                    

🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️
MATAN KWATAS

Kulsum Bappah
Azare
       Ummu iman

Ku bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:ukb696354.kb@gmail.com
EMAIL: Ukb696354@email. Com

🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)

_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻

5️⃣0️⃣

Sam Bata kula  abinda  indo take faɗa ba,
Ta kama hannunsu suka tafi ɓarayintta tai musu  wanka ta shafe su da mai ta kunna musu katoon suka nutsu kuwa,
   Suna tsaka da kallon ne beeba ta kira ta,
  Mikewa Ta yi ta shiga uwar dakinta,.
Ke dai bari beeba  ai na gasgata abinda naji,
Musamman indon nan maman umaima bata da lafiya fah amma sai ce min take wai jinyar karya ce"
  " To ki dai kara kula kar ki bari su tarwatsa ku,
   Haba habeeba sai kace wata yarinya,duk da ban tashi gidan kishiyoyi ba;amma ina ganin abinda dangin uba suke yi"
    Haka ne to
  Ina ango ??
     
   Angoo ya yi tafiya,
   Shine baki bishi ba; ai da kunje kunyi SHAHARIL ASAL din ku ( HONEY MOON ) ??
    Ehh haka matar shi tace,
     Ni kuma naga bata da lafiya bai dace na bishi na barta a halin da take ciki ba,.
       Yauwa Adda zuby  kinyi tunani !gwanda da kikayi hakan,
Tunda lamarin ciwo yau gare ka ne gobe ga wanin ka,
Kuma hakan zai kara miki martaba da  ƙima a idonsA,
  Ko beeba?
        Tabbas kinsan maza suna da wani Abu guda  ga abinda ransu yake so amma sai su ki fada suna son ganin gudun ruwan ka yaya  zaka yi,

   Zubaida tace haka ne kam,
Allah yasa mu dace,
  Yanzu ma Abinci nake son na daura na rana,
   Kai to bari nazo na tayaki,
Zubaida tace ai kuwa dAna ji dadi,
  Ina musa?? 

  ai kuwa ban ganshi ba,
    To sai nazo.

  Umaima zaki taya ni kwana yau??
   Tai murmushi tace ehh amma sai na tambayi mamana kar ta min fada,
   Ba zata miki fada ba ai nima maman ku ce,
  Eh haka maman mu tace,
Tace kema maman mu ce kamar ita,
Ehh haka ne,

Wajajen sha dayan rana beebalo tazo,
Suka daura sanwar dafaduka

Habeeba muje ki dubo Auntyn naki
    Oh har ta xama Auntyna kenan????
   Ehh alamun ku ya nuna akwai ayar tambaya a kanku,

Suka shiga sun sameta a zaune taɗan  jingina da filo sam bata jin karfin jikinta  ga kwaɗayi da yake damunta,
  Ganin zubaida ta shigo ta ɗan saki murmushi
" Sannu da aiki Amarya,
Sannu kadai,      
mamaN umaima ya jiki??
  Beebalo ta gaisheta yaya jikin?
  Da sauki sosai ma sai rashin karfin jiki,

  Adda fauxia tace wannan dole ne ai,
 
   Zubaida ta numfa sa tace amma kin samu kinci wani abu ko?. 

  Adda fauxia tace ta dan taba kunu kam,
Yanxu maganar da muke yi kenan,
  Wai faten shuwaka take so,
  Amma bata san inda xata samu shuwaka a unguwar nan ba,

   Beeba ta cafe lah rashin sani da na taho miki dashi,
Muna dashi a gidan mu ai

Unaiza ta zabura don manzon Allah,!!!

Gaba daya suka sa mata dariya
  Bari na kira musa ki mashi kwatancen gidan, sai yaje ya karɓo min,

  Beeba sukai dariya ita da zubaida,
Ta kuwa danna kiran musa,
Yana ganin kiranta ya kashe ya kira,

Lafiya kuwa???

  Lafiya kalau Baba musa so nake ka karbo min shuwaka
amma ga wacce zata maka kwatancen gidan su,
  Beeba ta karbi wayar
Tace UMAIMISHHH
       Yayi dariya don ya gane mai maganar
    
    Don Allah kaje gidanmu ka karbo sako zanyi waya yanzu su tsinka kafin kaje,
  Owk ba komai sai nazo,
    Unaiza tace " kun ma san juna kenan )
Tai murmushi,

MATAN QUATER'SWhere stories live. Discover now