🏘🏘🏘🏘🏘🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️
MATAN QUATERS✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah Azare
Ummu imanKu bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:ukb696354.kb@gmail.com
EMAIL: Ukb696354@email. Com🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI,3️⃣1️⃣
Shirye shirye ya kankama a bangaren Amarya LAURATU, duk da cewa babu wani abinda zata yi,
so take tayi aure mai albarka," LAURATU jiran ki fa nake yi, kin tsaya kina ta suku suku kinsan wahalar da muka sha jiya a kasuwar nan yau ma kina so mu maimata ko?
"Ki yi hakuri Aunty gani nan hijabi kawai zan sanya,
Yauwa Aunty zamu fara bin shagon dinkin nan ko?Tsoron mi kike yi LAURATU?
bayan munyi dashi zai kawo mana har gida idan ya kammala," Aunty ai basu da tabbas ne telolin,
Kwantar da hankalinki, banyi tsammanin ya fara tsiyar nan ta teloli ba, shidai idan ki ka bashi kudin shi to angama, ko cewa kikai zuwa dare kike bukata zaki amso abinki,
Zai fi kyau mu fara zuwa kasuwa mu gama da masu labulayen nan.
BAHIJJA tana ganin ikon Allah, wai ace mutum bashi da aiki sai kallo da tabe taben waya, kwanan ta uku a gidan yayar tata dai dai da Cokali bata ga ta kawar ba,
Damuwarta kallo da Bacci da waya,
Abin da ya ke kara daure mata kayi yadda bata da lokacin kulawa da IMRAN da tilon diyar su SALIMAH,
Ita dai sheda ce kullum babarsu sai ta mata fada akan sakaci da rashin kulan da take yi, amma ko a jikinta bata ma san anayi ba,SALIMA ce ta katse mata tunanin
" Aunty BAHIJJA zo ki wanke min kashi,Ki je wurin mamanki ta wanke miki;
Baki ga ina gyaran kayan miya bane?To zai miki yaji kinji,
Ammi na tace ki wanke min tana kallo neMtwssss
Ranta ya kara baci lalle kuwa zata fadawa Babarsu,
Halin dai yana nan.ARKILLA
Wai in kasan na fada baka san na mayarwa ba!
illahirin su maman Auwal da maman hydar sun fahimci inda zancen UNAIZA ya dosa, kasancewar sun san alakar dake tsakanin MUBARAKA da baban daddyn, amma da yake kawancen ba don Allah bane ko da wasa babu wanda ya taba sanar da ita,
Don ~IDAN DA AMANA RUWA BAZAI TABA DAFA KIFI BA~
MAMAN DADDY kuwa ko a ~jikinta WAI AN TSABIRI KAKKAUSA~ bata ma san da ita ake ba," Ku zo mu shiga ciki ~, IDAN KIRE NA YAWO ZABUWA NA YAWO ZA SU HADU~ wannan kiran da Baban umaima ya mata bai min dadi ba,
To ko ya ji mune?MAMAN HYDAR
tace a'a inaga bai ji ba gaskiya,
Suka yi ido ita da MAMAN AUWAL tai mata isharan da su tafi,
SHUGABA zamu ce sai zuwa gobe idan Allah ya kaimu, magariba ta gabato,Haka ne nima nasan yanzu Baban Daddy yana dab da isowa,
Ke MAMAN AUWAL yaushe ULCERN gidan ki zata tafi ne??ai tafi karfin ULCER wannan,
Gobe zasu wuce ita da wannan matar,
Wace mata kuma MAMAN AUWAL ??
" Matar ubansu mana, yadda na tsani mutuwata haka na tsani matan,
Wai zata tafi haihuwa gida hmmmmm,
Kice gobe dabar a gidan ki take,
" Tabbas shi zai kaisu ma,
UMMA TA GAI DA AISHA cewar MAMAN HYDAR
Ki godewa Allah, ba don kema kina da cikin nan ba; da ban san sanaben da zatai miki ba,
YOU ARE READING
MATAN QUATER'S
ActionZAMA NE IRIN NA YAN BARIKI, MATA SUBAR GIDAJEN SU, BA WANKA BARE WANKI SAI GULMA DA SA IDO.