🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️
MATAN KWATASKulsum Bappah
Azare
Ummu imanKu bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:ukb696354.kb@gmail.com
EMAIL: Ukb696354@email. Com🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻
5️⃣2️⃣
RASHIN SANI YAFI DARE DUHU
da'ace maman Auwal ta san abinda fitar ta zai haifar mata na raShin neman ixinin inno ba da bata yi baa,Domin cikin sanɗa ta fice daga gidan, ta nufi gidansu,
Da yake inno tai bacci mai nauyi ta gaji,
Wajajen kiran la'assar ya tashe ta,
Taga wayam ba kowa a gidan ta leka madafi ba kowa nan ma.
Tai sallah
Ta shiga makotah ta kira ikilimah kanwar maryamah ta daura mata girki,
Da yake yarinya ce mai hankali, har kaye kayen madafin tayi,
Ta kara gyara mata dakin yayi fes,
Inno tace " da ni take zancen"
K.S.A
Wato MAMLAKATUL ARABIYYATUS- SA'UDIYYABaba ce riƙe da mahmoud,
Ahmed da muhammaed suna bacci
Shi kuma rikitacce ne bai baccin rana da sauran suke yi barshi da kuka da shan nono,
kullum nono na bakin shi,
Idan ba nono kuwa sai kuka bilkisu duk tabi ta kare ta lalace ba wai a rashin ji da sha ba,
Tsabar ɗanƙwaaara ce ko abinci aka kawo mata bata da nutsuwar da zata ji ya tsirga mata
Don ma da iyayenta suka xo suna sun bar mata Anisaa ba karamin taimakonsu take ba musamman girki,Abincin dai take ci amma kukan yana tsaye a ranta,
Ta mike da zummar zata karbe shi a wajen Babah" Allah bilkisu zauna ki karisa kar ki biye shi,
Idan baki koshen ba ta ina zai samu nonon da zai zuƙan?Nace maki ki cire kukan nashi a ranki duk da cewa ke mahaifiya ce baza ki so kiji hakan ba duk da kinsan lafiyar shi kalau haka halitar shi yake ina ganin zai yi ilimi ne,
Anisa tace " ilimi kuma ??
Da kukan ??" Tabbass "
Bilkisu tace haka dai naji ana cewa nima amma ta yaya??
Baba tace nasha ji a redio a wurin malaman musulunci da masana kiwon lafiya na zamani suna bayanin amfanin kuka ga kwakwalwar jariri yakan bubbuɗe da karfafa jijiyoyin kwakwalwa kuma yaro yakan zama haxiki jajir tacce,
Mai zafin nama da kuzari maimakon yaron da kullum basu da aiki sai bacci sukan zama lusuraye malalata
Ta shafa kan mahmoud shiyasa kika ga kukan shi bai damunaa,
Kai gaskiya babah iyaye suna kokari,
Baba tai dariya tace tukunna ma,
Da saura ai sai sun fara miki al'alar hakuri da sauransu.
Ke dai Allah ya baki lafiyar shayarwa
Suka Amsaa da" Ameen ""
Suna ta kokarin janta da hira domin ta dan sake dasu amma ita tana ta harkarta dasu Khalida da umaima,
Umaima ta cewa maman ta" Mama yauma a dakin Aunty zan kwana."
a'a yau kam ai babanki ya dawo ko. Mamana ? anan zaki kwantaa kinga gobe ma da boko gwanda ki kwantaa
zubaida tace a'a tare zamu kwana ko umaimah?
Kar ki damu,
Zo nan kwanta idan na tashi na dauke ki,
Da yake bata da wuyar bacci nan da nan tai baccin,
Ku bani hankalinku ina so nai muku yar nasiha akan zamantakewar
Unaiza kice babba da ke zan faraa,
Duk da na san halayyarki ta hakuri da jajircewa da kau da kai akan lamurra to yanzu ma inason ki kaara akan wanda kike dashi ki kau da kai kice babba, ki ce mai jan ragamar gidan nan kin fi kowa sannin waye ni,
Duk wacce zata zo a bayanki lalube zatai cikin duhu kafin ta fahimci yanayin gidan da kuma sanin waye ne,
Don haka ki rike girman ki,
Ki dauka cewa zubaida kanwa take. A gare ki idan kika ga tai kuskure ko tai abinda ba dai dai ba ki haneta akai,
Bata san komai gameda da tsarin gidan nan ba kice jagora kice zaki nuna mata hakan matukar ta kwantar da hankalinta akan hakan
Yayi mata nasiha da tunasarwa sosai,
Karshe ya rufe da cewa duk dan adam ajizi ne idan kika ga na sauka hanya don Allah kiyi hakuri ki zungure ni don na dawo kan hanya da yawa a zamantakewar malam bahaushe miji ne matarshi zatai ta mishi laifi,
ko kuskure sai ya kyaleta maimakon ya ankarar da ita ta gane ta rabauta, sai yasa mata ido ya barta tana tabka kuskure wanda daga karshe idan abin yakai makura yana son ya tan kwarata bazata tankwaro ba, saboda ta zama gagaruma tana ganin iko da isarta ne ya hana mijin dakatar da ita,
daga karshe sai ya kai ta ya baro ta,
Domin kuwa ya rabata da hanyar Aljannar ta
Ko kuma ki ga macen ce miji yana rashin adalci a tsakanin matan shi tana cutuwa amma sai taki ta ankarar dashi tai ta shiga damuwa alhali idan ta zaunar dashi ta nuna mishi ba dai dai bane zai iya kyarawa matukar ta fishi gaskiya domin dan adam ajizancin shi yafi gaban haka,
Misali zan kawo muku akan wannnan
Unaiza kice kina da yara uku zubaida bata da ko ɗaya a ajizanci irin ta mutum sai idan na kawo muku sabulu ko omo ko kwai na kawo muku bai ɗaya alhalin ke nake zai iya kareewa albarkCin kuna da yawa.
To kinga babu adalci a ciki dole a banbanta.
To wata matar bazata nuna hakan ya dameta ba sai tace ta barshi da Allah,
AL KAMMALU LILLAHI RABBIL ALAMIN
Ke kuma zubaida kice karama
Ban auro ki saboda bana son matata ta gida ba ina sonta ,
Ina matukar kaunarta
Saboda biyayyarta juriyarta da kuma hakuri,.
Komai mukaddari ne daga rabbi Allah ya hada ku a karkShin tafarkina
Aure ibada ce babba,
Wanda dole cikinshi akwal kalubale iri iri,
Ina da yara kanana bazan yarda da tozarci ba ko ranar girkin ki kike tashi ki daura abin karyawa
da wuri don ba naki bane wato su zauna da yunwa,
bazan lamunta ba
YOU ARE READING
MATAN QUATER'S
ActionZAMA NE IRIN NA YAN BARIKI, MATA SUBAR GIDAJEN SU, BA WANKA BARE WANKI SAI GULMA DA SA IDO.