🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘
MATAN QUATERS✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah Azare
Ummu imanFollow me on wattpad
@kulsumbappa facebook: @ukb696354.kb@gmail.com
Gmail Add @ ukb696354@gmail. Com🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻0⃣2⃣
Qasimu ya karisa shago ya tsince abinda zai yi amfani dashi
Ya dawo gidan ya share shi tsab
Yana gamawa yaji kiran sallar la'asar daga masallaci da yake can kasar layi
Suna ida wa ya mika hannu sukai musabaha da wadanda suke sahu daya kamar yadda musulunci ya tanada
Suka fito daga masallacin yasa kai yayi gaba
Da niyyar shi taلا wucewa kasuwa ya sayo katifa da zanin gado da zai jefa a dakinshi,Lawiza ce take cewa maigidanta '' baban daddy munyi bako fa''
Ke ya akayi kika sani ?
'' dazu na raka maman salima na ganshi ya fito nan nake tambayar shi ina matar shi........
Bata karisa ba ya katse ta
'' wai maman daddy ban hanaki mu'amalan nan da su maman salima ba?
Ah a ai ba ni naje ba,
Ina zaune ta isko ne
har gida kuma kasan bazan kore ta ba':
Ke kenan babu dama na hanaki abu ki hanu sai kin aikata,Wato kinfi zabar kawaye akai na,
Kai baban daddy nacce maka isko ne suke ,
To ki sani wallahi da mutunci na bazaki zubar min da mutunci ba koyaushe a cikin hada daba kike a gidanan , kice uwar daba baku da aiki sai yi da wannan kuyi da wannan kuyi da wancan, Allah ya yaye mike,
Ya raba ki da wannan dabia''
Amin
Ai kuwa maman daddy ta amsa tace ''
.
Ta cigaba da kunkuni ta wuce daki,
Tsoki yaja '' mtwssss
Saboda idan akwai abinda ya tsana a rayuwar shi to ba yaga dabi'ar matar shi ta hada daba da take yi idan ya tafi wurin aiki,Yayi iya bakin kokarinsa
Don ya hanata amma abun ya gagara,Kai har karar ta yakai wurin magabatan su sunyi sunyi abin yaci tura,
Wai tsabar rainin hankali ma ce mishi take ita Allah ya bata farin jinin mutane ne
mi zai sa ya takura mata,
Babban abinda yake daga mishi hankali shine yadda mata suke kin kula da hakkin da ya ratayu a wuyansu
Mace zata bar gidanta babu shara babu wanke wanke kai abinci ma basu damu dashi ba idan akwai mai aiki to za'a bar musu sallahu suyi yadda suke so
Bai manta ba kwanakin baya hakan sanda yayi sanadin mutuwar auren daya daga cikin makwabtan su kai harda rasa rai ma,
amma duk bai ishe su EZNAH ba
Maimakon sauran su koyi darasi da abinda ya faru akan maman ihsaanWata rana mijinta ya mata gargadi akan ta daina zuwa gidan maman daddyn nan da suke yi ranshi baya so har ce mata yayi zai dauki kwakkwaran mataki idan bata daina ba,
Da farko kamar taji ashe likimo tayi,
Ta cigaba da fitarta tanasa lantana mai aikinta yin abinci,
Wata rana maigidan yayi dawowar bazata ya tsaida motar shi can nesa ya karisa gidan bata nanKusan minti goma yayi bata dawo ba ,
Bayan dawowarshi ne a wurin aiki ya mata magana ina taje?
'' tace ba inda najee baban ihsaan,
Ko?
Eh,
Bai ci mata kala ba,
Washe gari ta kira mai aikinta lantana ta bar mata sallahu,
'' zan fita amma ba dadewa zanyi ba,
Idan kin gama shara ki dau nama a fridge ki sulala ki soya min kafin na dawo''
To Aunty,
Da manja za'a soya ko mangyada?
Manja mana,
Kinsan baban ihsaan baya cin mangyada ai,
YOU ARE READING
MATAN QUATER'S
ActionZAMA NE IRIN NA YAN BARIKI, MATA SUBAR GIDAJEN SU, BA WANKA BARE WANKI SAI GULMA DA SA IDO.