🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘
MATAN QUATERS
✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah Azare
Ummu imanFollow me on wattpad
@kulsumbappa facebook: @ukb696354.kb@gmail.com
Gmail Add @ ukb696354@gmail. Com🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻1⃣6⃣
Hmmmm yanzu Aunty ba don kin gani ba da shikenan ya cuce ni na rasa ko?
Baka da hakin shi shiyasa Allah ya bayyana maka ba tare da ansha wahala ba
,
Baba Musa
Ba don na ga idon ka ba a zamanin nan da wuya a samu matashi mai hakuri da hangen nesa uwa uba biyayya wa na gaba da shi irinka,To duk wanda ya hada wadan nan abubuwa kuwa karyar wani bawa ya cutar dashi,
Sai dai kuma idan jarabawa ce daga ubangiji,Baba musa
Na'am maman umaima'
da ace zamu na kiyaye hakkokin Allah yadda yace mu zauna da kowa zuciya daya yadda Allah ya umurta,
makota mu basu hakkinsu,abokan zama da Allah ya hada mu zauna dasu zuciya daya, da abin zai mana sauki,Uhmmmm haka ne Aunty,
Wallahi ina mamakin mutane Aunty,
a rayuwa miye ribar ka cutar da mutum ne bare dan uwanka,
wanda duk duniyan nan ba yashi kusanci,Baba musa ka gode wa Allah da har aka fara maka hassadar,
Kasan hassada kuwa?Wallahi mai hassada da yasan yadda hassada take daukaka wanda ake mishi hassada to da wa kanshi zaiyi,
Saboda ya samu ya ci gaba shima ,
Tashi mu bar wurin kafin su dawo, ka gyara wajen sosai kar ma ya gane,
To,
Maza maza musa ya gyara wurin ya wanke hannun shi ya dankawa maman umaima yace gashi ajiyi a wurin ki gobe insha Allahu zan wuce dashi,
Ah to shiyasa fa nace wa yayanka ya ajiyi a dakin shi ya kasa ganewa,
Eh toh Aunty ai bazai gane ba kinsan gani yake kamar duk daya ne bai san cewa yan ubanci yake son yana nunawa ba,
Hmmm baba musa na rasa mi umaima ta mishi?
Musa yace ''
Wallahi ba abin da ta mishi Aunty''Wai baki san idan ana son a kuntatawa uwa sai a taba danta ba,
UNAIZA tace ''
To ai yayi a banza tunda a nawa tunanin inaga umaima ai yar shi ce halak malak,Wauta ce ke damun shi ai Aunty da kuma zugar mahaifiyar shi,
Wallahi ko a jikina domin a kanshi yake yi,
Kuma Aunty naji dadi da baki sanar wa yaya kasimu abinda yake yi,
Kinsan yaya bai iya fushi ba idan an tabo shi,Haba baba musa sai kace wata yarinya,
Abinda baka sani bane santsin takalmin shi zai kadashi da ganshi,
Ai banga ribar hada dan uwa da dan uwa ba ,A JURI ZUWA RAFI NA TABBATA WATARANA TULUN ZAI FASHE,
Tabbas maman umaima,
AI IDAN KERE NA YAWO ZABO NA YAWO ZA'A HADE''
Sosai ma inji musa
Allah ya rufa asiri,
Amma kasan indai yamin rashin kunya bazan kyale shiba,
wannan ma saboda yar shi ce shiyasa bana tanka mishi,
YOU ARE READING
MATAN QUATER'S
ActionZAMA NE IRIN NA YAN BARIKI, MATA SUBAR GIDAJEN SU, BA WANKA BARE WANKI SAI GULMA DA SA IDO.