shafi na arbain da daya

128 21 2
                                    

🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️
MATAN KWATAS

Kulsum Bappah
Azare
       Ummu iman

Ku bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:ukb696354.kb@gmail.com
EMAIL: Ukb696354@email. Com

🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)

_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻

4️⃣1️⃣

Hasbunallahu wa ni'emal wakeel!
Wa lahaula wala kuwwata illa billahil Aliyuul azeem,
Abinda Alhaji yake ta maimaitawa kenan,

   Ya kasa tsaye ya kasa zaune, ya ci gaba da ambaton INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR-RAJIUN,
Ya fita kenan da niyyar zuwa asibiti  sai yaji an  fara kiran sallar magariba,....

Da ba don kar Ya rasa sallah ba da asibiti ya nufa,amma kasancewar ba halin shi bane rashin yin sallah a jam'ei ba, ya  shiga masallacin kofar gidan shi,
Bayan sun sallame  sallan ne  ya ke cewa liman "" a sa mu a addua,"

Sun sha mamaki domin kowa yasan Alhaji sai anyi sallar isha yake shiga gida.

Bai tsaya a ko ina ba sai H.M.C,
ya sameta tana kuka akan sallaya ,
Haba hauwa'u yanzu kukan magani ne?
Yaya abin ya kasance?
A dai dai ina ne kuma?

  Da kyar ta kwashe abinda ya faru ta fada mishi ,
Yace masu GARKUWA DA MUTANE ne tabbass,
YA HAYYU YA KAYYUM  BI RAHMATIKA ASTAKISUU ASLIHLI SHA'ANI KULLUHU LA ILAHA ILLA ANTA!!
likitar ce  ta shigo ta  karisa mata Alluran,
Alhaji  ya ce  " ya akai kika kawo kanki asibiti?
Ta nuna mishi  wacce ta kawo ta wannan  ce, kuma maman ta ce likitan nan"
Ya musu godia,

Ya kama hannunta suka nufi police station don su bada report,
An gama dauka report suka dunguma sai A.A SOKOTO,
Suna sa ran Abin zai zo da sauki tunda akwai na'urar  C.C.T.V by camera da take leki a mashigar  kuma komai ya faru tana nadewa,
DETECTIVE MU'AZU  ya kwantar musu da hankali bayan sun gama ganawa da ENGINEER mai kula sashen Camerar.
Ya mika mishi kundin ajiye ajiye wato ( FLASH )
Ya tura mishi komai tas rangadadass

Dare yayi Alhaji kuyi hakuri ku tafi  gida in sha Allahu komai zai zo da sauki"
Duk da sun rufe fuskar su da MASK  amma gobe in sha Allahu zamu tafi V.I.O'S zasu binciko mana mammalakin motar,
Yanzu gida zamu tafi kenan ?
Mu barta a hannunsu,
Kawai ta fashe da  kuka
 
Hauwa yaya zamuyi ?,
Ina muka san zamu fara neman ta,
Adddu'ace mafita kawai,
zata dauki wayarta ta kira yan uwanta ashe jakar ma sukutum ta manta a asibiti,
Wayar shi tana aljihu yaji karar ta
Ya juya ya kalleta "ke ce fah kike kira na",
Na manta Wayar a asibiti,

  Assalamu Alaikum ,
Ey yanzu take fadamin,
Ya musu  kwatancen gidan,

  Basu sha wuya ba suka gano gidan,

ya tara ma'aikatan gidan da limamin yana musu bayanin abinda ya faru da Tilon 'yar shi Zubaida,
Wayar shi ce tai kara yana dubawa yaga lambar haj hauwa da alama sun iso kenan,
Ya umurci mai gadi da ya bude musu gate motoci biyu ne suka shigo,
Yaa salam sai lokacin ya farga bai ga motar ta ba,
Suka shigo harda maigidan su,
   Ah ahaaa Alhaji (Bagudo ) dama 'yar kace
Ikon Allah ai ni mai dakina ce take min bayani marar lafiya da Habeeba ta kai mata ita, kuma aka manta motar
Subhanallahi!!! Allah ya kubutar da ita,Allah yasa tana hannu na gari,
Ya ce " anyi report ne ??
" Eh mun je POlICE STATION "
bari na kira kanina S.S ne dan sandan farin kayaa,
Ya mishi baayanin dole sai sun je C.I.D OFFICE
Kai tsaye ANTI TERRORIST S2AURD suka nufa,bangaren manyan laifuffuka da kasa ta haramta
Sashin KIDNAP,
Bayan daukar bayanan ne suka koma gida inda suka iske DETECTIVE SADEEK TAHEER WURNO ya iso,
Matan suka haura sama don yin sallah
Hajia da kyar ta karisa dasu sama dakinta,
ta nuna musu make wayi suka shiga sukai sallah,
Hotunanta ne kaca kaca a kewaye a gidan,

MATAN QUATER'SWhere stories live. Discover now