shafi na talatin da bakwai

82 15 0
                                    

🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️
MATAN KWATAS

Kulsum Bappah
Azare
       Ummu iman

Ku bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:ukb696354.kb@gmail.com
EMAIL: Ukb696354@email. Com

🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)

_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻

3️⃣7️⃣

Baban Auwal na cikin rudani abinda zai ci ya gagare shi,
Kullum taliya da manja,macaroni shinkafa da wake,
Ga fitinar inna tace sai maryama tayi arbain kafin ta dawo,
Yanzu sati na biyu kenan suke ciki amma duk weekend acan yake yi inna tai  mai tuwon dawa ko na alkama mai masifar gardi da dadi
  Yau  ma ya gama ci kenan ya karkace
Miye ka tsura min ido fadi damuwarka
"inna da kin hakura mun tafi......
Ina???
Na banu.
Yarinya ta haihu bata samu kula ba sati biyu Fah kawai da ma ace matar ka kin tsatsiya ce  zata iya daukan dawainiyar ta to;
Kai ma da hakkinta ya zama dole ya duro mata akanta bata kula ba balle wata kishiya sam,ina!!
Dubi fuskar ka har wanii kashi ne ya fito maka a gefen idonka tsabar horon yunwa,
Duk ka kekashe ka kode kamar wani wanda baka cefani a gidanka, ba don ina zuwa ba da sai nace kana cikin ragwayen mazan da baka iya shiga da leda gidan ka,
   Maryama taji tijarar yake karewa, ta fito daga kuryar daki, dauke da farhanah, ta miko mishi,
Har Allah Allah yake ya hada hannayen shi da nata yadda fAtar ta tayi luwi luwi ta cika tam fatar ta sai wani sheke take yi,
Bakin ta mai kama dana tarwadan nan ya kara haske,
Kugunta ya tsuke yayinda cinyoyinta suka kara fadada,
  To ka amsheta mana ka zura mata idanu kamar jikan Goje,
Muryar inna ce ke kwararo mishi tijara,
  Tai maza ta koma daki kafin a  haura mata itama.
   Ya rike ta kam, kamar mai niyyar mai data ciki,
ga wani sassanyar kamshi,dake tashi
Ya kamata kaje ka duba baffanka da yake shema bai ji dadi ba,
   To insha Allahu zan ne mi ishiyaku ya rakani,
  Ba laifi,
Yauwa kasan an sa bikin 'yarshi ma ko? Bai sanar dani ba kuwa,
  Kasan shi da kunya da kawaici,
Idan ka samu hali duk da cewa kayi hidimar suna ,ka dan sa mishi hannu ko gado kai mata,
In dai da halin hakan,
  Lah babu damuwa yaushe ne ake cin kasuwa malumfashi ? da sai a saya kawai allah barshi idan lokacin yayi sai. Bashi; yakan kAi nawa ne?
Tace hawa hawa ne amma  dai ka biya mana ka tambayo,
Ko kuma  ka sa umaroji ya tambaya maka  farashin domin kana zuwa zasu fahimci kai bako ne su zabga maka kudi,
  To shi kenan inna hakan za'A yi.
*********************
Kai dannan ashe abin ya matso shine sai yau kake sanar dani,yaya ita unAizar ina dai ba komai?
   "Wallahi koh kadan bata daga hankalinta ba"
Allah ya shi mata Albarka, kuma nima insha ALLAHU zuwa jibi zan taho, yanxu haka ma gidansu unaizar zan tafi na sanar musu suji daga gare mu,kar su jiyo a gari, Allah ya muku Albarka.
Ta kashe wayar.
Batai kasa a gwiwa ba ta zari maaya fi ta nufi dakin mama take sanar da ita Auren kasimu ya matso makonni biyu masu zuwa.........
   Ayyurirriii
Kai abin nan ya min dadi cewar Indoo
Haba mata sai kissa da iyayi da ladabin ganin ido, nagode da yaya kasimu ya gane da ma wannan uban nata ko yAushe naje wucewa zaki ganshi zaune kan buzu yana kafar da yaranshi, anyi ittifaki a duk fadin tangazA bai taba aurar da  yarshi ta dawo gida ba,
   Bello ne ya kutso kai,
kai tun daga kofar gida nake jin amonki ko lafiya???
  Uwardakin ka yar masu kudi tai kusan zuwa,,,
Eyyehhh wannan ai albishir ya kamata kiiyi min domin kusa a ranku yanxu ne yaya kasimu zai yi aure, kuma dukkan alamu  ya nuna unaiza karshenta yazo bata isa tayi kishi da yar masu kudi ba duk da maluntar ubanta.......
  Inno ta katse shi,
Ku kuwa na rasa mi unaiza tai muku yarinya mai kunya da kawaici da son mutane da mutuntatawa....
Tab ina!!!! A da kennan baki zauna da ita ba   ne ai tunda taje birni  idonta ya bude take rashin mutunci shi kanshi yaya kasimu hakuri yake da ita,
Indo ta chafe....
Yooo idan ba dole ba mi zai kaishi kara aure innoo?
   Nan mama ta amsaa ku daina kushe mata yar gwal gani take tafi kowa 'sa'ar surka,shiyasa idan matan wanku suna fada tai ta kadifiri har tana ce musu suna koyi da unaiza,,to yanxu ne zaki san asalin halin surkuwar taki,
Ehee
Ni Allah yasa ma ingarma zai aura tai maganin uwar iyayi ta hanata sakat a gidan,
  Inno tace ku sha kuruminku Kowa da halinshi zai zauna,
  Ni na tafi nasan zan iskee malam a zaure.
  Mama tace shashasha ke indo idan kun tafi biki acan za kiyi zamanki,
Kuma ina son ki haddasa musu matsala a cikin gidan ladabi iya ladabi ki mata sannan kiyi kokarin  rabata da musa
Kar ta kuskura taga mutuncin shi,
  Sannan kai ma bello ......
Ba sAi kin fada ba ni kuma kamar ba jinin zuriar kuba,
  Ku da aka ce tsuntsuwa ma idan taxo wucewa matukar kun sa mata yami sai ta fadoo,
To ki tabbata sai na sa unaiza zaman gidan nan ya gagareta;
Wai kinsan abin haushin nan wannan sAkaryan musa  kamar ya mata sujadda don biyayya kiri kiri take nuna min 'yan ubanci,
   Kar dai ka faasa cin ubanta
Kai ni hutun ma ya kare zan koma jibi jibin nan ki hada min tsArabar uwar dakina da aminanta.
Allah sarki maman daddy ta washi unaiza shiysa nake son ta.
Malam ne ya shigo zai kama ruwa,,
Yace kai dai kaji kunya har abin naka ya kai ka tozarta matan dAn uwanka,to bari ka sani duk sokoto baka da wacce ta fita don ko kasimu ba da shi kake zama ba,dole amincewarta ne yasa kake zaune
Ya nuna mama da charbi wallahi ina guje miki,ace baki da aiki sai sa 'ya'ya a gaba kina musu hudubar tsiya.
Ya nuna indo yanxu wannan bata ishe ki ishara ba tun tana karamarta kika koya mata rashin mutunci kina murna kina ganin taya wulakanta abokiyar zamanki,yau gashi an wayi gari aure ya gagareta duk inda taje sai ta fito kuce asiri ne wallahi idan baku canza ba dunia ta isheku,
    ya shure takalmansa yayi makewayi,
   Bello ya sheke da daria yace kuji don Allah shi dai kullum babatu an tabo matar gwal inno.

*********************
Salima ta dawo ammafa ala dole taki zaman dakin mahaifiyarta sai wurin laure,ango yana son ragi zafi yarinya ta kasa ta  tsare, dole sai dare suke fakon ta su dan shanah,
    Kwanaki ukun su ya kare,girki zai dawo hannun uwargida sarautar mata,
    Zuciyarta sai yankewa take idan ta tuno da shiga maadafi ga  shi dai dole ne tayi tunda yanxu laure matar gida ce,
   Tana wannan nazarin ya shigo yana so ya kAranci yanayin fuskarta, to dai ba yabo ba fallasa ta gai dashi, yadan zolayeta da yake ma'abocin zolayar ne ta dan biye mishi,
   To na dawo gare ki mi kika tanada mana??
  Kamar na mi?
  Zata cigaba da abincin ne ko zaki karba kinsan yanzu "dodo daya kuke wa tsafi"ya kamata  tana samun hutu itamah,
Oh ta nan ka bullo to barni na yi aikin ladar nima,
Shi kanshi bai so fada mata hakan ba amma yasAn hakan zai iya sa mata kishin tayin,
   Mi kake son ci??
Uhummm nasAn ba zai wuce talia da mai zaki iya dafawa ba,

Ko?
Haka kace?  Ko dai shi kake son ci ??
Nasan abinda zaki iya dafawa kenan,
Nan taji ranta ya baci amma ta daure,
To shikenan Allah. Yasa na iya dAfawan,
Ya mika mata kudin cefanin,
ta karba,amma don Allah inason ka ajiye ne a kasuwa bani da kayan kamshi a madafi na

To har wani kayan kamshi kika sani ; to bari dai na barki kar kice na hanaki dauko mayafin ki muje,
   Abin  mamaki sai ganin ta yayi ta  biya dakin laure tana ta sallama amma hayaniyar laure da salima bai barsu sun jiyo ba,
Sai ta dan  tsaya kadan tana nazarin  lauren  tana ta sharholiya da yarinya karama, gashi ita da ta haifi 'yar bata iya jure dawainiyarta amma ita ta jure ko a jikinta,

Sai taji wani sanyi a ranta ko ba komai taci albarkacin wannan shi kuwa mai takanas din duk abinda zai mata da zummar bacin rai zata shammace shi,
Auntyn salima kin biye mata ina ta sallama baku ji ba zan shiga kasuwa,
To mummy adawo lafiya salima kuwa ko a jikinta,
Ta rako ta har bakin kofa ta juya da saLima a hannunta,tare da mamakin saurin saukowar uwargijiyar tata.
Tofah manya zasu shigA madafi
  Ko wace kwama calar za'a dafa???

MATAN QUATER'SWhere stories live. Discover now