shafi na Arbain

115 20 0
                                    

🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️
MATAN KWATAS

Kulsum Bappah
Azare
       Ummu iman

Ku bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:ukb696354.kb@gmail.com
EMAIL: Ukb696354@email. Com

🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)

_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻

4️⃣0️⃣

Washe gari baban hydar bai yi kasa a gwiwa ba ya gane kwatancen wurin mai taken AMIBISH TAILORING & CUISINE
cikin mutuntawa da martaba aka karbe shi mamallakiyar wurin haj Amina kyaky-kyawar bafulatana doguwa mai yalwar fara'a ta karbe shi,tai mishi bayanin abubuwan da suke koyarwa,.
Ta bashi menu dinsu ya karanta ya zaba mata fannin girki,
Duk da cewa da tsada amma haka ya biya, akan washe gari zai fara kai ta
Yallabai " na manta zaka hado da kananan hotuna guda biyu"
  Yace ".In sha Allah !
Nagode kwarai"

*********************
  
Lauratu ce a falo ita da 'yarta tana koya  mata sayyidul istigfari sai ta jiyo sallama baki ta rarumi hijabinta suka gaisa  ta miki don ta  kawo musu ruwa ,
Sai taji suna cewa ," oh kiga har rungumar 'yarta tayi abin tausayi ta rike ta zuciya daya; amma ita neman haukata ta take yi,
Ita ko ta rabe don taji mi suke cewa,
Sai taji dayar tana cewa " mamAn Auwal Allah yasa ta bamu hadin kai, mu yi amfani da ita taci uban ta, kinsan bana manta rashin mutuncin da tai mana,
har yanzu fa fuskar Mubaraka akwai tabon igiyar wuta"
   Kar ki damu maman daddy bari ta shigo dai,
    Wuf tai ta shigo musu da ruwa
Da zobo
Ta zauna sai dai ban gane kuba??
"Ehh gaskiya bazaki gane mu ba makotan kune ta chan baaya mun kasance munyi zama da abiyar zamanki a baya da yake mijinku mai son mutane ne ya nuna yana son kanwata ta shiga ta ci mana mutunci don tun kafin nan ma na hana kanwata suyi soyayya duba da yadda muke dA ita,
Tazo tai mata duka da har yanzu ta bar mata tabo a fuska,
Ba'a dade ba ta bishi wurin aiki ta tsinka shi a cikin mutane,
To yanzu ma abinda ya kawo mu wurinki
Jiya ne suka hadu da makociyar nan tawa  wannan  ( ta nuna maman Auwal). abin mamaki sai wannan taji uwargidanki na neman yadda zata samu hatsabibin boka da zai haukata ki,
Shine ita kuma ta kasa hakuri ta zo ta samen,
To gaskiya bamu sanki ba; amma kirkin mijinki yasa muka zo mu kubutar daki,
  Laure kuwa tai kasake tana sauraronsu,

Yadda dai take maganar kamar gaske,
amma in dai bata manta jiy a maman salima ko gate bata leka ba, saboda M.P take fama dashi,kuma ita dai tun da tasan halin uwargijiyarta bata yadda da tsubbu ba balle boka kai idan har  zata mata adalci ko maganin mata da mata suke sha bata sha, barta dai da son jiki da son hutu,
Kuma shi din ma a sama ta dauka,

Tana hankalce dasu sukai signal sunga ta tafi duniyar tunani chan tayi nazari bari na kawo muku ragowar  kayan
Biki,

Tace musu "" biri yayi kama da mutum"
Ai kuwa naji tana waya kus kus bayan ta dawo dani take zancen; domin indai zancen  biye biye ne gidan tazo don ni ubana kullum yana kan buzuu,.
   Ku jira ne dai....
  "" Ke maman daddy ta yarda"
  Hahhhhaaa nice fah,
    ke bata ma   da wayo
Fah kiga harda fada mana waye ubanta,
Ke dai bar shashasha,
Ita kuwa dakin M salimah ta tafi ta same ta da Pad a hannunta zata shiga bandaki, jikinta ya bace da yake haka yake mata wannan haukan,
Ta jiyo salima na cewa Aunty momy tayi fitsarin jini,"
Ke ba fitsari ta yiba,
Zobo ne  ya zube mata,
Nan ta bata labarin bakin da sukai,
Amma ina son kizo muje  don ni ban san su bama,
Amma kinji kinji.......
  " Hmmmnn kai musu abin bikin ina zuwa,"
Ta kewaya bandaki don ta gyara jikinta,
 
Sukai ta zuba mata karyaa tana  ta nada a waaya,
  Ita ko sai biye mu su take chan sai ga M salima
Uban mi ya kawo ku gidan nan??.

MATAN QUATER'SWhere stories live. Discover now