shafi na shida

416 54 1
                                    

🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘
 
MATAN QUATERS

✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
     Kulsum Bappah Azare
       Ummu iman

Follow me on wattpad
@kulsumbappa facebook: @ukb696354.kb@gmail.com
Gmail Add @ ukb696354@gmail. Com

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻
بسم االله الرحمن الرحيم
Na sadaukar da shafin nan ga surkata ,
Haj Aishatu Gwoggo Allah yaja kwana, ya jikan Bappah,

0⃣6⃣
Kafin ya ankara jini ya wanke mishi fuska,
Ganin jinin bai sa ta saduda ba ta yunkuro zata sake kwada masa  kenan yayi ta maza ya damke hannunta,
'' ka saki ne,
zama da kai ya kare,
mayaudari fasiki,
Mazinaci''
Yau maman daddy ni kike cewa mazinaci, sharrin da zaki min kenan
Haba maman daddy idan kuwa zargi na kike yi akan haka kin cutar dani,
Duba wannan,nace duba kaga idan har sharri na maka,
Ta mika mishi wayar ya fara duba hotunan tun daga nan abin ya bashi mamaki wani makirin ne yake bibiyar shi,
Haba maman daddy akan wannan kika  zargi na
Kamar baki san sharrin social media ba
Ai kina ganin wannan kinsan hadawa akayi,
haba wannan duk yadda akayi so ake a hadamu  fada dake, ke kuma kika yarda,haba ya lallabata yayi ta mata dadin baki da yaudara,
Irin ta gogaggun maza yan bariki tuni ta aminci
Ta fara bashi hakuri,
Namiji kenan!! Dan babansa, ta nemo tsumma da ruwan ta goge mishi idan yayi raunin,
Yanzu kuma idan gari ya waye naje chemist mi kike so nace musu gameda ciwon,
Ta kwantar da murya,
''Sai kace musu wuta aka dauke kana laluben daukar fitila ce kai karo da wardrobe,
Yace mata '' shikenan kin kawo shawara ya lallabata har sanda tai bacci,
ya mike ya dau wayar yana son yaga ubanda ya turo ,sai yaga an rubuta maman salima, tsab ya dauki number yayi saving, ya koma ya kwanta jira yake gari ya waye,

Yayi magana da matar
Gari na wayewa,
Yayi shiri ya fita,
Ita kuwa maman daddy har ta zari gyale zata tafi gidan maman salima sai ta fasa,
Yin hakan da zatayi tonan asiri ne a gareta duk da cewa ta yarda da tsarin da baban daddyn ya mata a nata tunanin maman salima ce take son  ta hadata fada da maigidan nata tunda so take hala ta rama abinda sukai mata,

Gogan  kuwa sanda ya biya chemist akai mashi dressing,

ya wuce office bayan nutsuwar shi a office
Ya dauko number yayi dialling number  shiru ba'a dauka ba,ya kara kira sannan aka dauka
  assalamu Alaikum

Ya amsa
'' wa'alaikumus-salam
Ko zan iya sanin da wa nake magana?

'' tace wani irin tambaya ce wannan ka kira ni kuma ga tambaye ni waye?
Lalle kana da rainin hankali,

''Eh naga kamar an rubuta maman salima,

'oh dama kasani kake tambayata,
Don Allah a ina kika samu hoto na har kika turawa matata?

A inda kake yawon ta zubar aanan nasamu kuma naga yana da kyau maman daddy ta sani tunda na chan tana barbada mazajen wasu itama bata san abinda nata yake yiba kenan wallahi tunda ta sa na tunkari mijina yana  wajen aiki ba don oganshi ya bashi hakuri ba nasan da yanzu haka ina gidan iyaye nah,
Shiyasa na tura mata tagani kafin na bazawa matan  unguwar nan  su gani,

Dariya yayi yace''
To hakar  ki bata cimma ruwa ba saboda hankalin matata a kwance yake  tasan makirci ne irin na mutanen yanzu da basu da sana'ar da ta wuce SA IDO sana'ar banza,
Sa ido kuwa ya wuce na matarka da bata da aiki sai hada daba da dandali da gulmace gulmace,
To bari na shaida maka idan kace matar  ka tasan sherin zamani da social media da yake kwakwalwar kifi ce da ita,
to bani kadai naje ba harda kawayenta shakikan kawayenta, tundaga saukar ka a kofar gidansu NGOZI, har tafiyarka duk akan idon mu, to ki fita harkata ko na hada ki da maigidanki,
Sai mi ko yanzu ka hadani dashi buri na ya cika , ta katse wayar kit,
Wato bibiyar shi ake yi,
Oho dai tunda na shawo kan matsalar ai shikenan,

MATAN QUATER'SWhere stories live. Discover now