🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️
MATAN KWATASKulsum Bappah
Azare
Ummu imanKu bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:ukb696354.kb@gmail.com
EMAIL: Ukb696354@email. Com🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻
4️⃣4️⃣
KASIMU yace " wannan shine karin magana da larabawa suke cewa " AL MAR'ATU SHAKAA'EKIL AKWAAM"
Yau shikam ya gaskata don unaiza kan ta cancanci a kira ta da ~KALLABI CE~ ~TSAKANIN~ ~RAWUNA~
don ba ko wace mace ce zata iya hakan ba, sai GAWURTAC-CIYA shi yana jin labarin irin hakan amma bai tabbatar ana samu ba sai da abin yazo kanshi, musamman indai namiji zai kara aure shi da zaman lafiya sunyi hannun rigaa, baya manta Babban yayansu lokacin da zai kara aure, uwargidan shi hauka ne kawai bata yiba,
Domin hatta kayan Amaryar da zai aurah sanda ta cinna mishi wuta, lefen da ba'a kai ba kenan,
Haukan bai ma tashi tuburan ba sai randa aka kawo Amarya ranar kam *TURU* ne kawai ba'a sata ba,
ko nace *MARI*kai shikam ba don kar ace son kai ba sai yace duk iya fadin labarin masu aure da yake ji bai taba jin irin na UNAIZA ba,
Ya shiga abin shi ko ya kula da indaa akwatuna suke,
Ya wuce dakin unaiza inda inna take ya gaisheta,
Umaima kice wa maman ki na dawo, ta kawo min abinci nan; don yunwa nake ji yau kam,
Inna tace" yanzu nan fah muna palo da ita, to ko madafi ta shiga, ne?
A'a baban umaima ka dawo ne? Ehh yanzu nake aika umaima ki kawo min abincin nan,
"Ayya mun cike maka can din da akwatuna ko?
Kai!! ban ma lura ba,
( Wai nan shi basarwa yake yi bai son ace yana zakalkalewa akan idonta,
Domin zai iya sosa mata rai, shi kuma yayi Alkawarin duk abinda zai bata wa unaizar shi rai, kai bai ma ga abin ba da ikon Allah )
Ai kuwa zamu je jaje ne da yan office din mu wani staff din mune gidan shi ya kone,
Yaa subhanallahi, inna tace"
wannnan abin girkin naku ko?
a'a inaga kamar lantarki ce,
To Allah ya maida mishi Alheri,Ameen
Ai kuwa da na ajiye kayan ne kana zuwa ka gani don gaskiya ina son idan zamu tafi anjima yi musu jaje mu tafi dashi,
ai kuwa hanzari nake yi ki dai kaishi daki idan na dawo zan gani a nutse,
Yanzu mi kike yi ne?
Sanwa na daura na dare da yake da masu aiki a gidan abincin bai ishe mu ba,
sam,
Ayyah sannu da kokari, Allah ya biyaki,
Hmmmm Kasimu ai idan kaga abin nan da yarinyar nan tayi ma dole ka jinjina mata ka kuma kara ninka godiarka a gareta,?
Ko inna???
Ka bari kawai sai ka dawo, amma gaskiya kasimu irin halarcin da yarinyar nan tayi ba kowace mace ce take hakan ba,
Kuma ina maka tgargadi da tbabbar murya yarinyar nan ba kashin yadawa bace, ko bayan raina ka mata butulci Allah ban yafe maka ba, kuma Allah bazai gyaleka ba,
Ya ajiye cokalin,
Wai inna miya faru ne kam,
Kike irin wannan kakkausar maganar?
Sannin halayen maza da irin butulci da juya baya da kuke yiwa matayenku nake yi,
( Ita ko tana chan baiwar Allah bata san wainar da ake tuyawa ba,)
Ya amsa wayar abokanshi a gaggauce ya sha ruwa ya tafi
Inna kice mata na tafi,
To Allah ya tsare ya kaika lafiya.Yana abin hawa ne amma yana ta nazarin kalaman inna,ikon Allah yanzu ashe akwai namijin da za'a mishi hallaci ya butulce daga baya,TIR kuwa da masu wannan halayen
***************************
M salima tana kicin tayi
Kaca kaca da ko inah wai ala tilas zata gwada CHOP ONE da taga recipee din a zee world cikin shirin " OUR DISHIES"
da kyar ta sha,
ba laifi yayi kyau kam, abinda ya tsaya mata araifa bai wuce kintsa wurin da gyaran shi ba, ta tsani wanki wanke a rayuwarta musamman ma yadda tai daka daka da wurin,
Ko tsaka bazata gwada mata tsuka ba domin ta yita ba adadi ,
Ta ajiye mishi nashi akan tebur har da sa wani ganye tai ado dashi ina ruwan renon indiyawa,
Lauratu da salima sun tafi kitso makota an yarfa musu kanana salima tana dawowa kan uwar tayi mama yunwaa nake ji,
Je ki madafi zaki ganshi a cikin bowl din nan,
Laure ta fito falo da BEADS a hannunta zo na sa miki,
Aunty yunwa nake ji sai naci abincin tukunna, Aunty muje kicin ki bani abinci inajin yunwa wai momina ta gaji,
Tun daga kicin suka fara cin chop one din maman salima don Allah yaya sunan wannan abun?
Salima tai zubur tace FISH ROLL,
laure tace wannnan ba kifi bane nama ne,
Uhmmmm salima ai shi fish roll da kifi ake yi kifin ma soyayye baki ganin wannan da nama akayi dasu kabeji,
" Kai M Salima yayi dadi wallahi naso ace a idona kika yi,
YOU ARE READING
MATAN QUATER'S
ActionZAMA NE IRIN NA YAN BARIKI, MATA SUBAR GIDAJEN SU, BA WANKA BARE WANKI SAI GULMA DA SA IDO.