🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️
MATAN KWATASKulsum Bappah
Azare
Ummu imanKu bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:ukb696354.kb@gmail.com
EMAIL: Ukb696354@email. Com🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻
5️⃣7️⃣
An kai ruwa rana kafin aka samu inno ta sauko ,
Ta hanyar dabarbaru da nasiha maryama ta tausashi innon,
Alhamdulillah maman Auwal ta zubda hawayenta ta nemi yafiyar inno da maryama kai har ma da mai gayya mai aiki wato mijinta mustapha kuma ta kara jinjinawa maryama bisa ga kokarin da tayi nab shawo mata kan surkuwarsu,
Tayi imani da Allah ba kowacce kishia bace zata iya jajircewa ta tsaya kai da fata ta hana a saki yar uwar zamanta ,
Tuunda wasu dama jira suke yi su samu damar,
" Inno ki gafarta miñ wallahi duk abin nan da kika gani sharrin shaidan ne da kuma biyewa zuciya,
nuna min kiyayya da kika yi na kin aure na tun farko da baban Auwal shi ya sa na zama karkacec-ciya a gidan aure na maimakon na zama mai kyautatawa a gare ki da juriya wata kila kiyayyar ba zata yi nisa ba,
Zai sa ki sauko daga wasar da kike min Amma duk da haka kiyi hakuri ki gafarce ni in sha Allahu zan sauya kuma nace na sauya,
" Inno tace Allah ya yafemu gaba daya,
Allah ya muku Albarka ya baku zaman lafiya ya hada kanku gaba daya
Kaima mustapha nagode Allah da ya kasance mai hakuri mai kau da kai,
Yanzu mustapha ka je ka roki malam ya karya sihirin da ya koma kan mahaifiyar ta ta ai ko ba komai an zama daya tunda an hada jini da ita."In sha Allahu zanyi kokari,
" Ke kuma ki tashi ki tafi wurin mahaifiyar taki ki nusar da ita ta yarda tai amfani da maganin Allah ya yafe mu gaba daya.
Ah baba umaima yau fah girkin zubaidatu ce ta yaya zaka zo kana lalume lalume nah gaskiya ban yi tsammanin ka a haka ba,
Rashin Adalci ne tsantsa kuma ka sani wallahi bazan yarda ba saboda nima haka zaka ringa kai mata kwana na,
wanda kasan yin haka haramun ne,"" Wai ke kullum sai kin ma wa mutum wa'azi ai na san haka yaya zanyi haba unaizatu yaya kike so nayi?
ni ba maxinace bane ko so kike na fara fita na neme wasu?
saboda kullum ke kice baki da lafiya kina bed rest ita kuma lalura yana damunta
Yaya kike so nayi? ya kai makura cikin shauki,
Baban umaima ba zan taba biye maka na shiga hakkin da ba nawa ba; idan har hakan kake so to sai ka tai wurinta ta yar je ke maka
Tukunna
haka musulunci yace.
Ya rasa yadda zai tunkare ta da maganan kuma yana jin nauyi ya fadawa unaiza abinda yake faruwa haka zalika yaje wajen zubaida ya nemi izini kuma zai zama kamar cin fuska ne,
To ina mafita ?
Miye abinyi?
Yasan dai barin kashi a ciki bai maganin yunwa dole a samu mafita dai.Unaiza ta samu dama ta kwace kanta wanda har yayi kokari ya yi nasara rabata da shimin da take jikinta,
Tana kokarin mai da shimin nata yaga fa kamar kara karkada su take yi,
Ina!!!! Ya yi kasa da muryaa kimin hakuri don Allah, don Allah" Na riga dana fada maka sai ka tambayo izinin zubaida,
Ya koma bakin gado ya zauna unaiza bazan iya fuskantar zubaida da wannan maganar ba zai zama kamar na tozarta ta ne, unaiza Allah yaga zucia bazan fada miki maganar nan saboda cin mutunci ba ko cin fuskar zubaida tunda na aureta yau watan mu uku ban taba kusantar taba,
Ba kuma na fada miki saboda tozarci ba a'a na fada miki ke ne a matsayin ke abokiyar rayuwata ce wacce kika nuna min duk halin da na shiga na farin ciki ne ko na bakin ciki ne duk ya shafe ki,
Na rasa ma wanda zan fada domin da nauyi ace ma tunkari iyayenta ko aboki,
Kullum nai kokariQn kusantarta wani bacci mai nauyi ne yake zuwa mata,
Sannan kuma......
Haka dai abin mamaki, yayi niyyar ya fada mata shafewar amma sai yayi shiru,
Unaiza tace subhanallahi
Amma miyasa baka fada da wuri ba,
Ai wannan sharrrin shaidanu ne da ka fada bari na kira baba malam na fada mishi ai kasan yana bada maganin hakan,
" Wallahi zubaida na manta shaf kai na ya daure ne,
Amma tunda haka ne kira woshi na mishi bayanin muji miye abinyi,
Ta kuwa dauko waya ta kira mahaifinta suka gaisa ta dan fara mishi shimfida kamin ta mika wa kasimun
Ta tashi ta nufi dakin yaranta
Tayi hakan ne don ta bashi dama ya sake ya mishi bayani sosai
Kar ka damu zan turo maka sako in sha Allah idan sakon ya iso sai muyi waya na maka bayani dalla dalla Allah yasa a dace,
YOU ARE READING
MATAN QUATER'S
ActionZAMA NE IRIN NA YAN BARIKI, MATA SUBAR GIDAJEN SU, BA WANKA BARE WANKI SAI GULMA DA SA IDO.