🏘🏘🏘🏘🏘🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘🏘🏘
MATAN QUATERS✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah Azare
Ummu imanFollow me on wattpad
@kulsumbappa facebook: @ukb696354.kb@gmail.com
Gmail Add @ ukb696354@gmail. Com🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻2️⃣8️⃣
HASBINALLAHU WA NIE'MAL WAKEEL!!!
Allah ka bani mafita!
Yanzu ni dai Alkawari ne tsakanina da UNAIZA ba boye boye ba rufah rufah tsakanin mu,
Amma kuwa anya zan iya fada mata wannan kuwa?Sai ya tuno girman Alkawari, da hukunci da Allah ya tanada wa mai saba Alkawari,
Yayi dogon ajiyar zuciya ya tura babur dinshi ya shiga gida,
Yar halak ya gani zaune tana ma KHALEEDA kitso da yake rikitacciya ce bata son a taba mata kai sai ta kwanta bacci ake mata,
Ta yi zubur ta mike ta karbi abin hanun shi ,
Baban umaima yau baka dawo da wuri ba,.inata tunanin ko lafiya?
Har na daga waya da zummar zan kira ka sai naga ashe kati na ya kare,Amma nai tunanin tunda oga na gari hala kuna tare,
Bari na dumama maka miya don gaskiya na dade da yinta yau ina gama sanwar rana. Na daura,
UNAIZA ki hakura da dumamen nan kar ki damu zanci haka,
Ah haba kar ka damu nasan bazaka ci abincin yadda kake so ba idan da sanyi haba minti nawa ne,
Kafin ya ankara har ta zari ashana ta fita madafi,Jikin shi ya kara sanyi,
Duk abinda zatayi don ta faranta mishi rai shi take yi,
Hmmmmm Ta mayar dani tamkar dan lili, ko dan sarki,
Yana ta sake sake a zuciyar shi,
Har ta kawo ta zuba ta kawo mishi ruwan wanke hannu,sai ta tuno bata kawo mishi yajin haihuwa ba, don shi mutum ne mai matukar son gargajiya,
A hanyarta ta komawa madafi ne, ta lura da sauye sauyen da QASEEM ya shigo dashi jikinta ya bata mijinta tattare yake da damuwa,
amma bari dai yaci abinci, ta tambaye shi,Hadiyar abincin yake amma zuciyar shi na tsaro mishi yadda zai tunkari UNAIZA kan wannan batun,
don gaskiya bazai fara rufarta da wannan maganar ba,
idan bai manta ba abinda ya jawo gagarumin matsala kenan gidan yayan shi kasancewar ya boye wa uwargidan labarin auren shiyasa har yanzu zaman lafiya ya gagara tana ganin anci amanarta ne,
shiyasa " take cewa zaman daduru suke yi; -- *WA IYAZU BILLAH* ---
ko da yake bazai hada jahilcin matan yaya da UNAIZA ba domin yanayin halin su sam ba daya ba ne, kuma Tarbiyar da UNAIZA ta samu kwatankwacin sa basu samu ba,
shiyasa suke zuba jahilcin su da rashin hankalinsu idan suna hira fah kai kace MAGUZAWAN KANO ne tsabar Ashariya,
Baban umaima abincin dai ya kare,
Naga kamar yau baka walwala inji dai lafiya ????Don yanayinka ya nuna akwai abinda ke damunka,
Ki dai bari,,
Haka abin yake amma dama ina da niyyar yanzu idan naci abinci zan sanar dake,
To ubangiji Allah yasa dai lafiya,,Wato dama Alhaji ne ya dora min wani nauyi mai wuyar dauka,
Wanda anawa tunanin wuya na kamar bazai iya dauka ba,
A haba baban umaima ban katse ka ba; yanzu har akwai abinda Alhaji zai nema a gare ka ka gagara mishi, irin kauna da yarda da aminci da ya baka,
Inaga gaskiya a shawarce ko abin yafi karfin ka,
ya kamata kayi ta maza ka daure ka jajirce ka karbi wannan abin hannu bibbiyu, iya kacin sakayyar da zaka mishi kenan don baka da abinda zaka biya shi dashi,,
YOU ARE READING
MATAN QUATER'S
ActionZAMA NE IRIN NA YAN BARIKI, MATA SUBAR GIDAJEN SU, BA WANKA BARE WANKI SAI GULMA DA SA IDO.