shafi na Ashirin da daya

724 67 20
                                    

🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘

MATAN QUATERS

✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah Azare
Ummu iman

Follow me on wattpad
@kulsumbappa facebook: @ukb696354.kb@gmail.com
Gmail Add @ ukb696354@gmail. Com

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻

ALHAMDULILLAH muna godia ga Allah madaukakin sarki,sarki da bashi da abokin tarayya cikin mulkinshi,Allah ya karbi ibadunmu da muka aiwatar na ramadana,
Inai muku barka da Allah,Allah ya maimaita mana,
Ina neman Afuwa na jina shiru da akayi.

بسم الله الرحمن الرحيم

2⃣1⃣

Maman Auwal hankalinta ya tashi,
Iyakar tashi,
Tashin hankali wanda hausawa suke cewa ba'a sa masa rana!

Da na sani qeya ce,

'' yanzu ya zanyi ni 'yaasu
Haka ne fah mugunta fitsarin fago ne gashi zai gangaro min abina,

kai nima dai da fitina nake,
Koda yake Allah ya nuna min isharar shi ne,
na hana miji kar ya sadu da ita, sai ga ciki Allah ya nuna min,

to amma dama maman daddy yaudarata tayi kenan ta kaini gidan wannan mata?

Kai inah na yarda da bayanin ta domin naga Alamon rashin nutsuwa a tare dasu,

To ni anya ma cikin baban Auwal ne a jikinya?.
Saboda bokanya bazata min karya ba tace zata toro mata bakin Aljani ya shige ta idan yazo zai kusanceta ya sabbaba musu fitina yaji ya washe ta,

Kai dole na samu baban Auwal ma na fahimtat dashi,
ba cikin shi bane maryama take dauke daashi,
Zumbur ta miki, haka za'ayi
Ta kira wayar MUSTAPHAN
Ina da magana da kai idan ka dawo,

Lafiya ko?

Eh lafiya amma yana da muhimmanci,

To sai ki jira sai na dawon,

Ya kashe wayar yasan fitinarta,

Yaja tsuka yace'' ke kenan kullum sababi da fita Allah yasa ki gane maman Auwal!

kai ina zuwa maman intisar?

Barni baban inti zanje na sanar da ita namu kujerun sun iso ?

Ba kya bari ta shigo da kanta ta gani ba?

Ina bazan bari ba! ina so tasan muhimmancin ka tasan cewa mijina ba rago bane, ba mijinta bane kawai ya iya sayayya wa iyalan shiba,

Sai na dawo yayi dariya ya bita da kallo
Hoo
BILKI! BILKI !
KO sallama
babu tsabar zumudi

Sannun da zuwa'' mai mai aikinta ta amsa ai bata nan sun tahi federal sectreteriat,

To da wuri haka,
Eh kamar wai sunje canza ko E.passport,

saboda jiya ina yan share share na naji uncle na cewa za su tafi umrah sai da tasani na dauko mata abin cikin durowa ashe yayi expire shine suka tafi canza shi,

Nan da nan fuskar maman inti ya canza,

Ita ko mai aiki ta lura
da hakan hasalima da gangan ta koro mata bayani domin abin takaice yake bata ace mutum bashi da aiki sai ganin kai,

Kin tafi ne maman inti,
oh eh ban miki sallama sauri nake baban inti zai fita,

Miya faru kuma naga kin dawo jikin ki a sanyaye?

Ba komai. Ban sameta bane wai umrah zasu taje canza pasfo,

Nan da nan baban inti ya sha jinin jikin shi,
Owk kwarai kuwa dazu na muka je sallar Asuba yana cewa liman ya taya shi da Addu'a zai kai matar shi ganin likita saudi germany
Domin juya ce,

MATAN QUATER'SWhere stories live. Discover now