🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️
MATAN KWATASKulsum Bappah
Azare
Ummu imanKu bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:ukb696354.kb@gmail.com
EMAIL: Ukb696354@email. Com🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻
5️⃣8️⃣
Indo na cikin daki a zaune ta ringa jiyowa kaurin hayaki yana tashi ta fito ta bi inda take jin kaurin sai ta lura a dakin zubaida ne,
Ta karisa har cikin falon don ta tabbatar ai kuwa a dakin ne; zubaida take ta turara su habba mai hadin tafarnuwa da hulba da jan miski,
Ta leka
" ki ce ?
to sannu da aiki ta fita cikin sassarfa ta nufi wajen unaiza da hanzarinta tai ta kwada mata sallama To ki fito na fada miki kin karyatani har kina neman ki ci mun mutunci to fito ki ga zubaida hayake hayake take ta bangawa a gidan nan,
A hakan kike kokarin tura yaranki gidansu su shanye su da asiri da tsafi,
Baki ji wari yana ta tashi ba,
Wallahi zo muje ki gani???
Yaya kasimu ya aurowa kanshi bala'i a masifar son kudin shi, da rana a tsaka ake hayake hayake
Sai ganin kasimu tayi ya fito daga dakin unaiza a tsammaninta ya dade da ficewa wajen aiki tunda sha daya ake nema,
Ta kideme ta hau kame kame ya.. ya... Ina... Kw...ina kwana????
Ashe kana ciki??
" Ina nan indoo, zuciyar shi na azalzala sai ya boye damuwarshi,
Muje wurin zubaidan ashe yanzu har ta samu wurin da zata fara min banke banken hayaki a gidana,
Unaiza muje domin ki zama. Shaidaa,
Rashin hankali cutar mai rayi
Jikinta na rawa tai hanyar dakin zubaidan harda hanzarintaa,
Ita kuwa hankalinta a kwance
Ta fito daga dakin
Ta amsa musu sallama,
A can gefe kuwa ga burner hayaki na tashi." Indo ce tazo mana da labari wai kina ta hayaki zaki mallake mu,
Indo maimata mana bayaninki,
Dama ina daki ne na jiyo kaurin nayi tsammanin ko abu ne yake konewa ashe magani ne???
To maganin miye indo zayyane mana??A'a mu ai bakon Al'amari ka zo har cikin gida kana irin wannan hayake hayaken,
" To indo bude kunnuwanki kiji,Wannan maganin da hayaki da kike gani ni ne na kawo mata da hannuna kuma Alhamdulillah;
Ke wai ma ina ruwanki a ciki idan ma mallakar mun zata yi,?Naji kina zancen 'ya,'ya na to ahir din ki ba zaki zo ki tayar min da hankali yadda kika hana matan yaya Bilyaminu zaman lafiya ba,
Kun zama bakin ganga duk inda aka buga zaki,
To ki shirya ya fito da kudin mota ya mika mata,
Mun gode da zumunci Allah ya saka da Alheri dama baba tun wancan satin ya min waya ya umurci ne da na baki kudin mota ki koma saboda gudun irin haka ashe ya fini gaskiya" Yaya don Allah kayi hakuri sharrin shaidan ne yace " sharrin shaidan ne ko??
Wai miyasa mutanen dunia sai kun gama yin damuwarku sai kuce aikin shaidan ne?a'a ke gane indo matsayin ki daban a waje na haka zalika matsayinsu daban : ke jini na ce kanwata ce babu ruwan da zai wanke wannan zumuncin,
Su kuma na auro su ina sonsu, na rabo su da gatan su wato iyayensu Allah ya dora min nauyin kula dasu dawainiyya dasu, kinga kuwa suma ba abin walakantawa bane,
Wai don Allah na tambaye ki mana" Mi yake sa kullum tsakin kannen miji da matan yayyensu basu da zaman lafiya ne kam?
Sai sharrance sharrance idan kuka hadu da marrasa hankali ayi ta iye ana kai ruwa rana,
To ina gargadinki ba nan bama ko matan yaya bilyaminu da kika mai dasu tamkar karnuka ki ka hana su zaman lafiya a tsakani ki kiyaye saboda kinsan dai dole ne mu yi aure mu zauna dasu ba zamu aure ku ba,
Don Allah bai halasta hakan ba kinga kuwa ya zama wajibi ku kau da idonku akan matayen mu ,
YOU ARE READING
MATAN QUATER'S
ActionZAMA NE IRIN NA YAN BARIKI, MATA SUBAR GIDAJEN SU, BA WANKA BARE WANKI SAI GULMA DA SA IDO.