shafi na talatin da shida

81 17 0
                                    

🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️🏘️

MATAN KWATAS

Kulsum Bappah
Azare
       Ummu iman

Ku bini a shafi na:
Wattpad @kulsumbappa
Facebook: @ kulsum Baffah
Gmail:ukb696354.kb@gmail.com
EMAIL: Ukb696354@email. Com

🖊️🖊️BAUCHI HAUSA WRITER'S ASSOCIATION🖊️🖊️
( BAHWA 📝)

_(Matattarar zaƙaƙurai, haziƙai, fasihai, mashahurai, kuma sanannun marubuta)👌🏻

3️⃣6️⃣

Hamdan liman khalakas-samawati wal ard,
Gaskiya baban yan uku sai godiar ubangiji, jarabawa ce,
Fatan mu Allah yasa a fito dashi lafiya,
  Yanzu awar su nawa da shiga?
   Bai cika awa ba fah ta duba agogon hannunta minti arba'in da takwass ne kar ka damu kwararru ne,
   Suna cikin tattaunawar  sai gashi tsulum a.  Kan gado ana tura shi abin tausayi hannu a nannade,
    Bilkisu ma lafiya tana kara samuwa har makewayi take zuwa da kanta,
  Ciki kuwa yana nan kamar wanda  aka manta wAni dan
   Dr wafeeya ce ta gyare gadon yaron tsaf ta kwantar dashi,
Aka basu magungunan da idan  ya farka za'a bashi don rage zogi
Ta zura mishi ido ikon Allah kenan yaro kasan kazo dunia,
   Dazu munyi waya da mutanen gida an min umurni da nasa sunan muhammad Mahmoud da Ahmad,
Masha Allah Allah ya raya su Allah yasa su dau kyawawan halaye irin na ma'aiki sallallahu alaihi wa salam,
  Ya shafa yace Ameen ya rabbi bilkisu Ke kuma Allah ya baki lafiya da ikon tarbiyartar dasu
********************
Abin dunia ya taru yama maman salima yawa tayi tayi salima t zauna a hanunta bayan dawowar ta daga gida,amma ina sai mummynta in ji ta da fadi
Sai kunata take.
  Yanzu wai laure ce muka  hada miji, kai ba don sanin shirka haramun bane wallahi da sai na farrakSu nasa mata warin jaba ,
Wata zuciyar tace   ki aiwatar kawai kya tuba daga baya,
Sai taji daya barayin na zuciar ta na cewa kul kar ki halaka kanki akan wata kishiya,kishiyar ma yar aikin ki,da kunyar kiyama ai gwanda ta dunia,kawai dai ki  ,
Ki canza hali ki rungumi mijinki da yarki,

To ni yanzu ta ina zan fara?
  Tab lalle akwai damuwa ni rabona da madafi ma na manta komai na sakankance ba abinda na iya sai kunna t.v da kallon Dstv duk series din da ake yi suna kai na,
Kai gaskiya fah na yiwa kaina lamba,
wanda idan ba na dage ba, bazan goge wannan lambar ba,
Chan ta dAuko wayarta ta bude data ta shiga whatsapp ta kutsa groups din da take da su chan ta tuna da kawarta
Hauwa garba umar wato Umm naseer cuisine
  Tai mata magana ta shafinta
    Lah ba komai bari na turo miki videos ki fara gani zuwa sati nasan zaki dauki abinda kika dauka amma fah ki sani sai kin mayar da hankali kin yi fatali da kalle kallen banza nan.
Haka dai ta kudiri aniyar canza rayuwarta
Dama wajen tsafta ba'a magana: barta da lalaci da ganda.

{ Waiwaye }
  Baban intee gaskiya motar kan nan ta tsufa  ya kamAta ka canxo mana new version, har kunya nake ji mu fita a ganni a gAbar motar nan waallahi,
baka ga yadda makocinka ki ye bane,

Burki yaja ya tsaya gefen titi,
Ya ya zayayo ya bude mata kofah to fito tinda kunya kike ji
Ga bakinta bai shiru,
Eh da sosai ma kunya nake ji,
Yo ka lura ko balkisu ya canza mata mota sau nawa,
Fita don Allah,
Abinka da marar kunya tai mirsisi,
Bayan sun sauka ne
Ta wuce daki ta kwantar da babynta. Ta dawo  zata shiga ciki,
Ya kwala mata kira,
Ina rabaki da ganin ido da shiga rayuwar wasu amma abu ya fAskara

Nikam sau nawa zan fada miki  ita da kike  son hada kai da ita samu na da na Mijinta ya banbanta ya fini samu nesa ba kusa ba,
Ya fini hanyoyin samu ya tashi cikin kudi yana kasuwanci yana aiki idan baki sani ba kawunshi shine (C G) ke bama shi ba ,kin san da cewa mahaifin wanda kike son kina hada kai da ita fah tsohon shugaban EFCC ne ( Hukumar hana ta'annati da tattalin arxikin kasa ) yau idan  mijin ta bai mata baa  fah mahaifinta zai mata don haka ki hango raatan  dake tsakaNin mu,
Naji mata kuna cewa dan mal.  shehu ko mal tukura da 'ya'yan Aunty ?
Ai kinga akwai banbanci don haka ki kiyaye ki hankalta bani da gashin su  ba zan iya kitson suba.
Yauwa na manta ban fada miki ba; an yi mata aiki an cire mata 'yan uku duk maza,

Eyyeh kace kankanba zai karu baama mata ba maza; hmmmm .
Banda abinki ina abin kankanba a haihuwa,haihuwar ma ta wahala tunda aiki akai mata haka zalika kuma dan ma sanda aka mishi aiki,

Ehhh baka san iyayenta bane zAta iya ce maka mijinta yafi na kowa iya kwanciyar  auren ma,
Ke ina raba ki da hassada wannnan matar miye bata miki a rayuwa don Allah?
To kinga wannnan hassadar da kike mata shi ke kara yaukaka mata ta ke cigaba take barin ki a baya,
Ya tashi ya fita ya barta a wajen yana mamakin babu ko dan Allah ya raaya balle ma ta tambayi yaya jikin nata.

********************
KASIMU ne zaune a  gaban ogan shi kuma sirkin shi cikin ladabi yake sauraron shi,
Ogan ya nunfasa  yace ban so hakan ba,amma dai na roki alfarmar makocinka wanda kuke manne da juna zai koma gida na gaba da nashi sai a toshe kofar shiga ta falon a fasa tsakar gidan ya zama itama tana tare da iyalin naka,na shawarci  injiniya da alhakin hakan  ya rataya yace zai yiwu, har ma yake ganin nan gaba idan an tashi za'a gina gidaje na masu iyalai da yawa; ga 'yan makullaN
Gwanin sha'awa yayi ta mishi nasiha tare da shawarwarin yadda zai dai dai ta matan shi ba tare da an samu damuwa ba,
Kuma a har kullum ina fada maka ka cigaba da neman na kanka hakan shi zai sa ka rufe ido akan kayan wani ko kayan gwabnati,
Kuma kayi kokari ka karisa gininka don muhallinka mutuncinka,
  Ko da na kasa ne.

********************
  Kai din yarda kayi da wannan iskancin ai wannan son zucia ce;sam ba zai yuwu ba ya za'ce saboda bakar gadara ya daga mu ya sa yarsa,

  ( Ba wai dagawan bane damuwAr abuBuwN da ta binne ne damuwarta domin matsafinta ya ce mata duk randa ta kuskura ta bar gidan nan to ta taabbata karfin ikonta zai ragu karshe ma zai iya karo mata kishiya,
( Anan ne tace da ai mata kishiya a rayuwarta  gwanda ya yayi ta biye biye yafi ye mata
Haka kika zaba
Ehh tabbas idan yaga dama ya zama bunsuru)
Na fada miki ki jibi zamu fara kwashe kayan,
  Tayi firgigi  a ankare ta dawo daga duniar tunani,
ya zata yi ? kuma gashi  tayi amAnna da aikin shi tamkar yankar wuka,
gashi yanxu ya koma ILLO chan iyakar nigeria da nijar daga kebbi,
Kuma ko number wayar shi bata karba ba,
Tab samm gaskia kayi musu tijara ba zaka fita ba.       
" Ni asuwa kare da  gudun layya"

Ya nuna mAta 'yan makulaye,
  Ta chafe su  tsaff zuciarta na ayyana mata yadda zatai dasu.

Ummu nasrin

MATAN QUATER'SWhere stories live. Discover now