shafi na Ashirin da uku

95 12 0
                                    

🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘
 
MATAN QUATERS

✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
     Kulsum Bappah Azare
       Ummu iman

Follow me on wattpad
@kulsumbappa facebook: @ukb696354.kb@gmail.com
Gmail Add @ ukb696354@gmail. Com

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻 
بسم الله الرحمن الرحيم

Wannan shafin sadaukar wane ga
HAJ NANA BAPPAH AZARE,
na samu karuwa da tayi Allah ya raya BABY,
Allah ya sauki yan baya lafiya irinsu:

Matar iro,
Matar Àssalis
Matar Ahmed garba
Matar ALH UMARU
matar sani yana
Yar gidan salisu musa😜😜😜😜😜😜

2⃣3⃣

Yaja gauron numfashi ya fesar,
yana da yakinin bazai samu matsala da UNAIZA ba,

amma ynzu yadda gizo yake sakar shine, kasantuwar yarinyar yar manya ce, ta ina zai fara tunkararta,
Kuma yasan zaiyi wuya irinsu su auri masu mata,

Tunda shi kanshi mahaifinta mace daya  gare shi,

Da kyar ya samu ya kau da wannan SOKI  BURUTSUN DAKE ADDABAR ZUCIYAR SHI.

maman salima ki tashi kinsan yau lahadi ce ta karshen wata ranar shiga kasuwa muyi sayayya amma kin kwanta kina bacci,

'' baban salima kaina yake min ciwo'
Ta juya ta cigaba da baccinta ,
  To  ya kike son ayi ynzu?

Ina takardar list din?

Wallahi banyi ba, kai don Allah dauki laure ku tafi kasuwan ai tasan abinda ake saya kowani wata,
   Kuma ta shirya salima ku tafi tare''

Ta ja bargo ta rufe fuska,
To amma mmn slim......
Haba baban salima so kake barcin nan ya tafi, kayi hakuri don Allah''

Ya mike ya samu laure a madafi tana damawa salima cereal dinta,
Abin sha'awa duk motsin da laure  zatayi salima na binta,
Laure na biye mata tana ta gwalabenta na koyan magana,

Laure idan kin bata kunun tasha ki shiryata zamuje kasuwa,

maman salima tace min kinsan abubuwan da ake sayowa ko?

   Zuciyarta cike da farin ciki amma bata nuna ba,

  Tace eh nasan wasun,

  Ya wuce ita ko murna don Allah Allah take ta samu dama ta samu karbuwa a zuciyar baban salima, saboda yana bata tausayi,
namiji ne har namiji sai rashin mata,
Mace bata da aiki sai bacci,
sai lalaci dai dai da gajerin wando da shimi mai aiki ne take wankewa,
ina! Allah ya wadaran naka ya lalace RAKUMIN  DAWA YAGA NA GIDA,

ta shirya tsaf ita da salima sai dai saboda tsaro batayi  kwalliya ba a  fuskarta,

   Namiji dan babansa! tsabar yadda laure take tafiyar da abinta  cikin nutsuwa da kaffa kaffa da salima,

sai abin yake bashi sha'wa, sun biya
SUPER MARKET sayyayyan kayan lashe lashe da tande tande na salima,

Nan laure take bashi shawaran a rage saya mata kayan zaki saboda yana cutar da  lafiyar yara,

Har cikin ranshi yaji dadi domin wannan kulawar mahaifiyarta ce ya dace ace tana mata,
amma ina!! ta fififta son jiki akan hidimar yarta,

   Aka zo fannin kayan sawa yaga ta zaba mata kaya na gani na fada, wanda ko shi dan boko iya zaben da zai yi kenan,

Laure!!!

Ya kirata,

Kin iya zabe, a ina kika  san kaya masu kyau ne  haka?

MATAN QUATER'SWhere stories live. Discover now