CHAPTER I

1.5K 47 5
                                    

AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story 📖

By Malik al-Ashtar 🖋

On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485


CHAPTER 1



*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
        _(The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities)._
https://www.facebook.com/100495222137315/posts/100496042137233/?substory_index=1&sfnsn=mo

                  *[📝I.W.A📝]*

Rufe idanu Zahara ta sake yi da sa ran ko zata samu yin bacci sai dai da ta tuna fuskar matar nan sai baccin ya gagare ta. Ji take duk inda ta duba ita take gani, tana bibiyar ta duk inda tayi, har ma a cikin mafarkan ta.

Sake juyi tayi ta canza kwanci bisa gadon, wannan karon zura kanta tayi a karkashin pillow, numfashi dakyar take yin sa, amma tafi gwammacewa yin hakan idan dai har ta samu yin bacci. Kokarin yin baccin tayi karo na barkatai, amma sai kwalwar ta shigo nuno mata hoton abinda ya faru kwana biyu da suka wuce. A yammacin nan da ta fita da gudu daga gidan MAMI, bata ma samu lokacin tsayawa gaishe da fuskokin sani da tayi ta haduwa dasu a hanya ba kamar yanda ta saba yi. Ita kawai a lokacin ba abinda take so kamar ta ganta a gida, kamar gidan shi zai mata maganin mummunan mafarkin ido biyun da take yi. Abin ma dariya wani lokacin yake bata, wai ita da da take guduwa daga gida domin ta kan ji kamar an takure ta. Amma gashi a ranar ba inda take ganin ya fiye mata tsaro irin gida. Tafiya-tafiya sauri-sauri take dan kar ta jawo hankalin mutane, amma ji take kamar idanun kowa a kanta suke.

Lokacin da ta samu ta isa gida, ta tarar da Mama zaune a falo. Ba ma zata iya tunawa ta gaishe ta ba, abinda kawai ta sani ta shige dakin ta kuma ta garkame da makulli. Tayi iya kokarin ta ganin ta fahimci meke faruwa, amma kusoshin kanta sun ki su yi aiki. Ita da kullum take rokon Allah ya sauya mata yanayin da take ciki amma bata taba tunanin zata tsinci kanta cikin irin wannan yanayin marar fassaruwa ba.

Bata san lokacin da bacci ya dauke ta ba, sai bude idanu tayi taga rana na haskota ta window. Ido ta kai kan agogon dakin taga har sha biyun rana tayi. Inda Allah ya taimake ta yau ogan ta bai zuwa aiki. Tana son ta koma baccin, amma kuma ya kamata taje ta taya Mama aiki. Bayan wani dan yaki da tayi a cikin kanta, na tsakanin ta cigaba da bacci ko ta tashi, daga karshe ta mike ta shiga ban daki. Bayan ta fito ta nufi wardrobe domin daukar kayan da zata saka. Sai dai tana bude wardrobe din, wani abu ya fado kasa. Da yake kayan nata duk a wargaje suke, domin a ganin ta bata da lokacin gyara su, ta duka da niyyar dauko abinda ya fadi ta mayar. Sai dai da ganin meye ya fado a kasa, tayi cak, a hankali ta shiga yin baya baya ganin ta baro bakin wardrobe din, ta ma bar dakin gaba daya, amma tsoro ya sandarar da kafafun ta ta fadi kasa. Kyarma take kamar takarda kuma ko kalma daya mai kama da addu'a ta kasa fita daga bakin ta.

Ba komai bane ta gani face gyalen Amriya da ta bari a bakin kogi, sai dai wannan karon duk ya baci da jini. A hankali ta fara rarrafawa domin ta samu ta bar dakin. Tana son tayi ihu amma ta kasa, tana son ta tashi ta ruga amma gabobin ta sun kasa. Iya kokarin ta take ganin ta saita bugun zuciyar ta, amma ma kamar karuwa yake. Cikin ikon Allah tayi nasarar kaiwa bakin kofar dakinta dake bude, bata san ta yaya ba, hannuwan ta a jikin tawul din dake kirjin ta, a guje ta nufi dakin Mama. Mama tana tsaka da da nadin kayan Abba sai ga Zahara ta shigo a firgice ta fada jikin ta.

Hawaye ne kawai ke ta malala a fuskar ta. Mama kuwa duk ta rude bata san me ya samu 'yarta ba. Zahara ba ma zata iya tuna ranar da tayi kuka a gaban mama ba. Domin a duk lokacin da take da wata damuwar, shigewa daki take ta kulle ta shirgi kukan ta, ba tare da Kowa ya sani ba. Bata taba tunkarar mama da wata matsala ba, dan haka dole wannan karon mama ta shiga cikin tashin hankali.

AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)Where stories live. Discover now