CHAPTER 7

1.3K 30 0
                                    

Hajiya Karima matar  Yusuf cike da samun nutsuwa. Daman ko ba dade ko ba jima tanada kudirin raba alakar tsakanin danta da wacce yake ikirarin yana so amma abinda yarinyar nan ta fada mata yanzu, bata bukatar hade sama da kasa ganin ta kawo karshen wannan soyayyar. A ranta tace wata kila dan nata bai san da wannan ba, da bai nemi ya aure ta ba. Wani namiji ne zai so auren "Yar gantali"? Kuma koda ma ya amince da wannan alakar, Hajiya Karima ba zata taba yarda ba, haka ma mahaifin sa Alhaji Yusuf.
Kowacce uwa zata so abun kwarai ga danta kuma tasan yar aminiyar ta ita ce wacce ta dace da Ammar. Duk da dan rawan kanta amma yarinya ce da ta samu tarbiya mai kyau daga mahaifiyar ta kuma tasan ba zata taba bada kanta ga namiji ba kafin aure.

“Zan samu baccin kirki ne kadai idan Ammar ya aure ta.” Ta fada a zuciyar ta.
Saukowa tayi daga kan stairs ta shiga neman Salmah. Bata ko bi ta kan bakin da ke kokarin gaishe ta ba. A cewar ta tanada abinda yafi wannan. Iya saurin raba danta da wannan yarinyar iya saurin samun sukunin ta.
Kusan ko'ina na wajen taron ta duba amma bata ga alamar Salmah ba. Ganin mahaifiyar shi daga nesa da alamun tana neman wani, Ammar Yusuf ya nufo inda take.
“Mama, koh Kamal kike nema? Ina tunanin har yanzu yana sama. Ya kai Fatima dan ta huta. Yanzu ma nake cewa naje na ganta.” Cewar Ammar ga mahaifiyar tashi da bata daina waige-waigen neman Salmah ba.

“Ina budurwar ka?” Mahaifiyar tashi ta tambaye shi, shi kuwa a take zuciyar sa ta wani buga.
Me yasa take neman Salmah? Ya tambayi kanshi, ganin yanda ran mahaifiyar tashi yake kamar a bace, ba idea bace mai kyau ya barta taga Salmah.
“Mama kin mini alkawarin fah ba zaki yi komai ba, a wajen walimar nan.” Dan nata yayi mata tuni cikin sigar lallaba.
“Rabu da ni..! Ka fada mini kawai idan ka ganta.”
“Nasan abinda tayi bata kyauta ba, amma nayi miki alkawarin zata baiwa Zahara hakuri, idan ta dawo hayyacin ta. Na rantse miki tayi nadama.”
“Ba zaka fada min inda yarinyar nan take bane?” Ta fada da dan daga murya wanda hakan yayi silar janyo hankalin wasu daga cikin bakin.

Ganin haka yasa Ammar ya yiwa Mahaifiyar sa jagora inda Salmah take ba dan yaso ba. Lokacin da Hajiya Karima taga Salmah kwance kan gadon danta kamar wata matar shi, dandanan yanayin fuskarta ya sauya kamar wacce aljanu suka shafa.
Salmah koda jin kofa ta bude da karfi, tayi sauri ta mike daga kan gadon. Tsoro ya dabaibaye ta ganin mahaifiyar saurayin ta. Jikin ta ya shiga rawa, ta kasa yin tsayuwa kuma ta kasa komawa ta kwanta.
Juyawa tayi ta kalli saurayin nata ko Allah yasa akwai wani taimako da zai yi mata, saidai shima duk a rude yake. Ya kasa fahimtar dalilin da yasa mahaifiyar sa ke ta duk wannan alhali tayi masa alkawarin ba zata yi wani abu ba wajen walimar shi. Addu'a yake tayi a ransa, kar ta yiwa Salmah wani abun. Sai dai ya makaro.

“Eh ai dole ki zo kiyi rashe-rashe kan gado, tinda a gidan ku kike ko a dakin mijin ki...!” Cewar Hajiya Karima rai a bace.
A rikice, Ammar ya kama hannun mahaifiyar sa, ya dan jata gefe dan suyi magana a nutse amma Hajiya Karima ta fizge hannun ta ta dumfaro inda Salmah take, da tuni ita ta fahimci lallai wannan matar ba son auren su take ba. Tuni taji kunci ya mamaye ta, a ranta tace me tayi da ta cancanci irin wannan tsana ga mahaifiyar Ammar. Tasan idan har bata amince da auren su ba, toh ba zasu taba samun kwanciyar hankali ba bayan sun yi auren.
Zuciya na mata zugi, jikin ta na rawa ta duka ta kwashi takalmin ta da nufin barin gidan baki daya.

Saidai ba wannan bane Hajiya Karima take so, bata gama magana ba.

“Ina zaki je? Ban gama magana ba da ke. Yau za'a yita ta kare. Ina son idan kika bar gidan nan, ki sa a kanki ba zan taba amincewa ba dana ya aure ki. Ta yaya kike tunanin zan amince da ke a matsayin matar dana bayan kin gama yawo a hotels din garin nan. Daina kallo na da wannan idanun naki, gaskiya ce na fada. Kin dauka ba wanda zai san da wannan danyen aikin? Duniyar nan karama ce yarinya, kar ki yi abu da tunanin wai wani ba zai sani ba.”

“Mama, dan Allah.. ki daina...”

Ammar a sanyaye yake kokarin dakatar da mahaifiyar sa, saidai ita sai da ta tabbatar da ta juye duk abinda ke ranta.

AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)Место, где живут истории. Откройте их для себя