“Ki daina motsowa haba Zahara, idan baki jin bacci. Zaki iya tashi ki samu wani abun kiyi.” Cewar Sarat cikin muryar bacci.
Tana da gaskiya, Zahara ta kasa daina juyi bisa gado, tun lokacin da suka kwanta. Ta yaya zata iya bacci? Bayan abinda ya fada mata. A lokacin shishigin Sarat ne ya kwace ta. Tazo a daidai lokacin da Kamal yace yana son ya auri Zahara.
Zahara taji kamar ta kurma ihu domin ya fitar da ita daga yanayin da take ciki. A lokacin bata san me zata yi ba, ko amsar da zata bashi. Juyawa tayi, tayi tafiyar ta ba tare da tace dashi komai ba, saidai koda suka koma daki ta fara jin haushin kanta na kin tsayawa. Domin akwai akwai tambayoyi da dama da take son amsoshin su.A lokacin hanyar daga lambun hotel din zuwa dakin da suka sauka, ba karamin tsayi yayi mata ba. Domin tasan idanun Kamal na kanta ga kuma tarin tambayoyin da Sarat take mata.
“Soyayya kuke? Amma munafuka ce ke Zahara !! Bani labari, ta yaya kuka fara soyayya ??”
“Stop please.” Zahara ta fada da sa ran ko Sarat zata yi shuru amma kamar ta manta wacece Sarat.
“Kin hanani kutsa kaina gurin Boss, ashe ke da yayan shi kike soyayya. Amma kar ki damu na fahimce ki, ba wanda zai iya tsallake charm din su. Abun mamakin, yanda kika yi, kika iya shiga wurin shi, duk da miskilancin sa. Come on Zahara, fada mini meye sirrin?”
Haka Sarat tayi ta maganganun ta, ba tare da Zahara ta tanka ta ba, dolen ta tayi shuru da ta gaji. Zahara na tunanin ma Sarat fushi tayi, amma ita wannan ba shi bane a gaban ta.
“Zahara kina takura min, kin hana ni bacci.” Sarat ta sake maimaitawa alhali ita Zahara juwa kwanciyar ta ne tayi wannan karon ba tare da tayi wani kwakwaran motsi ba.
Tashi Zahara tayi daga kan gadon, ta fito ta kofar bayan hotel din. Sanyin da ake dan rurawa yayi mata dadi. Nadamar kin zuwa da Kur'anin ta take. Domin ta lura lokaci ne mai kyau yanzu na karatu da nazari. Idan da tayi hakan kuwa, da ta samu dan sauki har ta iya yanke shawara mai kyau. Domin a halin yanzu, a cikin confusion take. Ta yaya zai iya zuwa a gaban ta yace yana son ya aure ta, alhali basu wani san juna ba. Wannan hujja ce da ke nuna ya dauke ta sakarya, yana tunanin zata yarda da wannan shirmen? Ita kuma yanzu take kara jin haushin kanta, na da bata jefa masa wayar shi ba.
“Kema kin kasa baccin koh?”
Muryar Mr. Ammar ce ta dawo da ita daga duniyar tunani. Yana zaune bisa daya daga bencinan dake cikin lambun hotel din. Tayi nisa sosai a cikin tunanin har yasa bata lura da shi ba a wurin. Murmushi tayi masa, amma babu tabbacin yaga murmushin da yake akwai dan duhu a wurin.“Ko zaki taya ni zama ne?” Ya tambaye ta.
Bata yi gardama ba taje ta zauna kusa da shi. Hirar aiki suka fara, hakan kuwa yasa ta dan manta halin da take ciki shima haka domin ya nuna mata bayan wasu mintuna.
“Ban yi tunanin haka ba, amma hirar aiki da muke yi a wannan lokacin ya dan yaye mini damuwar da nake ciki.”
“Nima hakan.” Cewar Zahara.
“Da gaske?” Ya fada. “Wani abu na damun ki ne?”
Ba zata iya fada masa abinda ke faruwa tsakanin ta da dan uwan sa ba.
“Dalilin brother na ne koh?” Ya tambaye ta.
Ta yaya ya sani? Yanda ta waro idanu cike da mamaki ne ya bashi dariya. Sai da yayi dariya mai isar sa kafin yace
“Idan da kinga yanda fuskar ki tayi, da sai cikin ki yayi ciwo dan dariya.”
“Ta yaya.. yaya aka yi kasan da wannan zancen?”
“Shi ya fada min.” Ya fada da dan murmushi.
Zahara ta rasa me zata yi tsabar kunyar sa da ta kama ta.
YOU ARE READING
AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)
HorrorLabarin wata hatsabibiya kuma fitinanniyar aljana da ta yi bayyanar bazata ga wata budurwa Zahara cikin wani irin salo na almara. Zahara tayi arba da Amriya cikin suffan mutane, har ta kwatanta mata gidansu, kuma zahara ta tafi gidan inda ta iske la...