CHAPTER 21

212 29 7
                                    

Komawa Khadija tayi ciki tana murmushi tare da tambayar Kamal ko zata kara tsayawa domin taya shi hira.

“Waye yazo?” Kamal ya tambaye ta.

“Zahara ce.”

Da mamaki Kamal ya kalle ta jin Zahara tazo har gida neman shi. Gashi daman ya jima rabon shi da ita sakamakon halin da gidan su yake ciki ga kuma zanen da wani kamfani na kasar Malaysia suka bashi da zai gama shi da gaggawa.  Ga kuma rashin lafiyar da yake fama da ita kwana biyu. Yayi kewar ta sosai, yana da tunanin da ya samu sauki yaje gidan su. Sai gashi cikin sa'a tazo, ba karamin dadi yaji ba.

“Tana ina? Ce mata ta shigo."

“A'a tayi tafiyar ta."

“Kamar ya ta tafi?”

“Na fada mata kana nan kuma tana iya shigowa amma tace min wucewa zata yi. Nasan ko sauri take.”

“A'a, ba gaskiya bane abinda kike fada. Idan da tana sauri ne ba zata zo nan ba. Kuma koda tazo nan ba zata ki shigowa ba. Me kika ce mata?”

“A'a komai kawai nace mata baka da lafiya ne kuma ni ke kula da kai.”

“Me kake yi haka? Me yasa ka tashi?” Ta tambaye shi tana mai nufo shi da sauri shi kuwa yana kokarin sauka daga bisa gadon da kyar.

“Tambayar ka nake, ina zaka je?”

“Zan je na ganta ne, na tabbatar tayi wani tunani ne a kanmu.”.

“Kamar ya tayi wani tunani, bata yarda da kai bane ko me? Baka da karfin jikin da zaka fita yanzu, ka kira ta wani lokacin sai ka yi mata bayanin babu wani abu tsakanin mu. Ni zan iya zuwa na ganta saboda kai.”

“No, kar ki damu nafi son naje da kaina.”

Cikin wardrobe din sa ya bincika ya dauko bakin jeans da t-shirt ita ma baka. Duk da yana jin babu kwari jikin sa amma dole sai yaje domin baya son Zahara tayi wani tunani. Haka Zahara take, dandanan karamin abu ya juya mata tunani. Ya fada a ransa. Baya son tayi tunanin yana wasa da hankalin ta ne idan ba haka ba zai sha wuya kafin ya sake samun yardar ta. Sai da aka dauki lokaci sosai kafin ta fara sakewa da shi. Ba zai so ya rasa komai ba saboda yar karamar rashin fahimta.

“Toh ni zan tuka ka, please kar ka tafi a haka. Zan damu.”

“Da gaske kina son taimaka min?" Ya tambaye ta.

“Yes of course, ni fa na tambaye ka."

“Ki kula min gidan, ba zan jima ba zan dawo. Nayi miki alkawari.”

“Amma.."

“Please kar ki ce komai, ba jimawa ba zan yi.”

Ya fada kafin ya saka takalmin sa. Duk da abinda yace mata sai da ta taimaka masa ya shiga mota. Tayar da motar yayi da tabbacin Zahara gida ta wuce. Wajen karfe tara ne na dare, baya tunanin tana wajen aiki. Duk da haka yayi kokarin kiran ta a waya amma tana ta ringing ba'a daga ba. Kuma ya tabbatar da gangan taki daga kiran.

Yasan hakan zata faru. Ba zai ga laifin ta ba. Har yanzu akwai kuruciya a tattare da ita, idan tasa abu a kanta yana wahala a iya canza mata ra'ayi. Hakan yana dan bata masa rai amma yana iya kokarin sa ganin ya fahimce ta.

Yarinya ce kyakyawa da hankali amma tana da karancin yarda. Tana tsoron kar ace yana tare da ita ne kawai dan yayi wasa da hankalin ta domin tana ganin bata kai ajin da zai yi soyayya da ita ba kuma zai iya samun wata fiye da ita. Ba wai ita ce ta fada masa ba, shi da kan sa ne ya karance ta.

Yana kusan kaiwa gidan su, ya sake kiranta domin ta fito amma bata daga ba. Gashi kuma ba zai iya shiga gidan su ba a wannan lokacin, domin zai iya kara hassala ta. Daga karshe yanke shawarar yi mata text yayi.

AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)Où les histoires vivent. Découvrez maintenant