CHAPTER 40

666 12 4
                                    


“Lokaci ya yi da zaki nemi zaman lafiya da kanki da kuma mutane. Mu zamu taimaka miki ki fita daga wannan kurkukun da kika rufe kanki. Kin ɓata tsayin ƙarnuka kina ɗaukar fansa kuma na tabbatar kin fi ni sanin akwai wata rayuwa bayan mutuwa, ba zaki cigaba a haka.” Sheikh Said ya faɗa.

Dariyar takaici Amriya ta yi.

“My soul is damned my dear man. This soul is cursed kuma ba zan iya yafewa bil'adama ba kamar yanda ka ce. Ƙishirwar ɗaukar fansata a kullum ƙaruwa take idan ina ganin ku. Ba zan daina faɗa ba, mutane munafukai ne.”

“Ko yaya zaluncin mutane yake, ba ke  zaki yanke wanda zai rayu a cikinsu ko wanda zai mutu ba. Karo na biyu, lokaci ya yi da zaki yafewa kanki kuma ki yafe musu, ki samu salama da kowa domin yin sauran rayuwarki cikin salama.” Cewar Sheikh.

“Mu gama da wannan wasan kwaikwayon, ku yi abinda zaku yi ku bar ni na tafi.” Ta faɗa cikin sanyi da sigar barazana.

Malaman kamar suna jira ta faɗi hakan, suka cigaba da karatu, wannan karon tsawon awa ɗaya babu ƙaƙƙautawa. Mahaifiyar Zahara ita, koda ta gama aman ta kishingiɗa a kafaɗar mijinta. Sheikh Said ya nemi da kar ta fita daga falon.

Ita kuwa Amriya, ta kasa jurar ayoyin Allah. Tayi ta kokowa da son tsayawa cikin jikin Zahara amma ayoyin na ƙona ilahirin jikinta. Ta so ta yi taurin kai amma ina ƙarfinta ba a kwatanta shi da Allah. Tana son komai ya zo ƙarshe, ta gudu daga nan domin daina jin wannan maganganun da babu komai a cikinsu sai gaskiya. Tsawon shekaru take hatsabibancinta toh me zai sa yanzu ta canza? Kuma koda ta so tuba bata tunanin Allah zai gafarta mata bayan ta'addancin da ta aikata tsawon ƙarnuka.

“Yanzu da kika san abinda Allah ya ce game da mu hallitunsa, dalilin rayuwarmu a nan duniya, ba ki ji kina son shiga musulunci ba?”

“Zan fita amma na roƙe ku, kar da ku tilasta ni shiga addininku.” Cewar Amriya.

“Shiganki musulunci zai zama kamar wani guarantee ne, zamu bar ki ki tafi da sanin cewa kin sauya kuma zaki yi rayuwa mai kyau nan gaba. Babu wani abu da ke nuna mana idan kin tafi ba zaki je ki cutar da wani ba.”

“Haka babu abinda ke tabbatar muku da idan na shiga addininku, ba zan iya cutar da wani ba.”

“Kin gani nan ne addinin musulunci yafi ƙarfin duk wani tsafi da kika sani a duniya. Idan kika fita daga nan a musulma zaki samu duka goyon bayanmu. Zamu bar ki ki tafi muna faɗin zaki yi abubuwan alkhairi a sauran rayuwarki.”

“Wannan ba shi ake kira halin munafukai ba?”

“Ba kowa ne mu da zamu yanke miki hukunci, Allah ne kaɗai zai iya hakan. Allah kaɗai yasan abinda ke zukatanmu. Kar ki damu, Allah mai yafiya ne da jin ƙai. Duk wannan shekarun da kika ɓata kina zalunci, bayan yafiyar da Allah zai miki, wannan nauyin da yake zuciyarki zai sauka.”

Amriya duk da rashin ƙarfinta sai da ta juya ta kalli Kamal.

“Kana tuna min Musa.” Ta ce masa.

Tambayoyi ne birjik a cikin kwanyar Amriya. Komai a hargitse yake da ta kasa sanin abun yi. Ta yi iya ƙoƙarinta ganin ta gudu daga wurin domin ta dawo idan komai ya laɓa amma ta kasa. Wannan hasken da ke fita daga jikin malaman da kuma tsarkakan kalaman da ke fitowa bakinsu da take son kaucewa su ke mata yawo cikin kai.

Kamal bai san amsar da zai bata ba. Ya saurari labarin wannan aljanar kuma ya fahimci irin abinda take ji duk da ta'addacin da ta aikata ba na a taya murna ba ne.

“Zan karɓi musulunci amma ina son zaunawa kusan wannan ahalin. Bana son komawa wajen nawa ahalin. Bana son komawa kan duwatsun nan da ƙauyen nan. Wannan rayuwar da na yi marar kyau, kusan duk laifinsu ne.”

AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)Where stories live. Discover now