CHAPTER 13

1.2K 31 2
                                    


Zahara ce a bakin Window, tana kallon yanayin garin mai cike da ban sha'awa. Ta nutsu tana tunanin rayuwa, tun bayan abinda ya faru ita da Amriya, Alkur'ani ne da salloli da Azkar ne kadai suke iya kwantar mata da hankali. A halin yanzu ta mayar da hankalin ta kacokam kan addini, har makarantar dare take zuwa duk weekend. Sabuwar rayuwar da ta kirkirarwa kanta kenan..

Karatun da take zuwa ya bata damar dan sakewa da rayuwa ba kamar baya ba. Saidai ta kasa manta ita ce silar rushewar soyayyar oganta. Ta cigaba da zuwa wajen aiki, kuma ita ce shaidar halin da Mr. Ammar yake ciki. Mutumin da ya kasance a kullum cikin raha da kazar-kazar, amma yanzu ya canza. Ya daina mayar da hankali a aiki, ya daina murmushi, ya daina dariya, magana ma ya daina idan ba ta zama dole ba. Haka kayan jikin sa sai yanda yaso yake zuwa da su. Duk ma'aikatan sa sun damu da halin da yake. Kuma duk wannan a ganin ta itace sila.

Kamal yana iya kokarin sa ganin ya nuna mata ba laifin ta bane, amma ta kasa kawar da muryar dake nuna mata laifin ta ne. Tun ranar da Kamal ya bata wannan wayar, bai daina kiranta ba yana jin yanda take. Da farko kananan sakonni yake turo mata, da kawai na tambayar ya jiki ne... Amma wata rana zuwa karfe dayan dare, kusan tana bacci, taji sautin shigowar sako a wayar.

“Bacci kike?”

Sai da ta karanta sakon so ba adadi, farat daya kuma taji ta daina jin baccin. Sai da ta jira na kamar mintuna goma kafin ta tura masa amsa, bata son yayi tunanin ko daman tana jiran sakon nasa ne ( duk da kuma hakan ne.)

“A'a, not yet.”
Ta mayar masa da amsa a takaice. 5 min.. 10 minutes bai turo  wani sakon ba. Har ta fara tunanin ko dan bata mayar masa da amsa da sauri bane. Sautin karar kiran wayar ne ya dawo da ita daga tunanin da take. Koda taga sunan sa a jiki, gabanta ya fadi. A zuciyar ta tace “Wayyo Allah, murya ta a wannan lokacin, kar fa ya tsorata.” Sai da tayi ta hada yawu sau ba dadi, kafin ta dauki kiran. Tana mai gyaren murya idan ba haka zai dauka da kato yake magana. A cewar ta.

Sallama tayi, ya amsa sannan yace
“Fatan dai ban takura ki ba?”

“A'a babu abinda nake yi.” ta bashi amsa.

Bata san ya zata siffanta alakar dake tsakanin su ba. Tana son ta sanshi sosai... Tana jin kullum tana kara kusanci da shi, lokaci daya kuma tana jin tsoro. Bata da wani kwararan experience a wannan fannin. Karancin yarda da kai dake gare ta, ya hana ta gasgata abinda zuciyar ta ke raya mata. A tunanin ta, wane mutum zata iya birgewa, babu wani abu special a tattare da ita. Wata kil, ko Kamal dake dan kula ta yana turo mata da messages, tausayin ta ne kawai yake ji. Ita ma tana son jin abinda sauran mutane ke ji, amma tana tsoron abinda zai biyo baya.

“Hello, are you there?” Ya tambaye ta.

Ta bace a cikin tunani, muryar sa ce tayi nasarar dawowa da ita.

“Bacci kike ji? Idan kina so zan iya bari sai da safe muyi maganar.”

Bata son ya katse kiran.
“A'a bana jin bacci.” Ta fada a takaice.

“Ok, gobe kin zo wajen aiki ko?"

“Eh.”

“Ammar yace min kuna da seminar a Madawa, ai kin shirya da kyau ko?”

“Yace min kwana biyu ne zamu yi a cen. Har na fadawa iyaye na, sun amince.”

“Ah, ok good. Nima cen zan je. Idan kina so zamu iya yin tafiyar tare.”

“Ummh..”

“Kar ki damu da dan uwana, motar mu zata kasance a bayan motar shi ne. Kanwar mu ma Afnan tare zamu je, zasu iya tafiya tare. Kuma ina tunanin akwai abokanan aiki da suma zasu je.”

“Eh akwai Hajiya Hasana da mijin ta, Ibrahim da kuma Sarat.”

“Hajiya Hasana da mijin ta suna da motar su, Dan uwa na kuma zai iya daukar Ibrahim, Afnan da Sarat. Ni da ke kuma sai muje a mota ta.”

AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)Onde histórias criam vida. Descubra agora