“Sai an wuce asibiti gidansa yake ko kuwa kafin a kai? Ina tunanin na ɗan manta takamaimai inda gidan yake.” Maryam ta cewa Zahara da sigar wasa.
Zahara gyara ɗakin da ta duk yamutse tayi, ita kuwa Maryam ta zauna bakin gado tana kallonta.
“Well, ina ga kinada gaskiya, ba shawara ce mai kyau ba zuwa gidan Kamal koda kuwa ina son zuwa. Bansan me zan ce masa ba, kuma nasan lamarin ne zan ƙara dagulewa maimakon inyi gyara.” Cewar Maryam.
“Naji daɗi da kika gane hakan, ban son yayi tunanin ni marar yawo ce da ba zan iya mantawa da komai ba, na cigaba da harkar gabana. Ina son cigaba da rayuwata kamar baya, wacce nake yi kafin in san shi.” Cewar Zahara.
“Ba rashin wayo bane gareki, ke mutum ce shi yasa. Wannan ce wahalar soyayyarki ta farko, kuma kinada ƴancin yin kuka. Amma kinada gaskiya, yanada kyau kiyi gaba, ki ƙara sanin wasu sabbin abubuwan rayuwa. Saidai ba zai yiwu na barki ki koma rayuwarki ta baya ba, a'a wannan ba yiyuwa bane. Zahara lokaci yayi da zaki zauna kiyi tunani akan ƙarancin yardarki. Ya kamata mu nemo wata hanyar canza hakan.”
“Ba abu bane da za'a iya zancawa, yau ko gobe." Cewar Zahara.
“Haka ne, amma ke babu wani ƙoƙari da kike yi. Zan kama miki amma kece zaki yi aikin mafi muhimmanci.”
“Eh na sani Maryam, ki yarda da ni, ina son na canza."
“Toh, yanzu mu ɗan fita. Mu je muci wani abun a waje."
“Ina?”
“Suprise ne!”
“Idan mijinki ya kira fa?"
“Bah what? Ni ba prisoner shi bace, ina zuwa inda nake so. Essential shine nasan inda nake saka ƙafata. Ya yarda da ni kuma yasan adadin yanda nake sonsa.” Maryam ta faɗa tana murmushi.
“Mtsw sannu Romeo da Juliet. Well.. ina son fita amma na gaji ba zan iya ba.” Zahara ta faɗa tareda komawa bisa gado tayi kwanciyarta.
Ba tareda ta shirya ba taji Maryam ta janyo ta daga bisa gadon, sai gata ta faɗo ƙasa.
“Wayyoo karya ni kike son yi ko me? Da fa na karya hannu.”
“Hannun naki ya karye ne?” Maryam ta tambaye ta.
“Ina tunanin bai karye ba amma...”
“Good, tashi kiyi wanka, ni zan fiddo miki kayan da zaki saka.”
“Hum ban yarda da ke ba, idan basu mini ba, ba zan saka ba."
“Ban damu da ra'ayinki ba, oya je kiyi wanka sai wari kike!”
“Nan fa ƙarya kike yarinya.” Zahara ta fada tareda tashi daga ƙasa.
“Ki je kiyi wanka ki daina wannan surutun dan Allah!” Cewar Maryam tareda jefawa Zahara pillow.
“Zan je dan Allah, daina ɗaga murya.” Zahara ta faɗa tareda shigewa bathroom kafin Maryam ta tashi gidan.
BANGAREN KHADIJA
Khadija na tunanin ciki ne da ita. Bata da wani ƙonƙonto akan hakan. Tun bayan wasu makonni, take jin alamar symptoms na mai ciki. Tana yawan jin kasala, ga yawan fitsari duk bayan mintuna goma alhali da tana iya riƙewa na yini guda bata yi fitsari ba. Da farko ta fara tunanin ita ce ke sa hakan a ranta, amma mamanta suka fara yi mata ciwo, da safe ƙwarnahi bai rabuwa da ita. Kuma wannan safiyar bayan ƙwarnahi sai ga yawan jiri. Ba coincidence bane idan hakan ya faru.
“Karɓi je kiyi gwajin." ƙawarta Sa'adiya tace mata.
Karɓa tayi ta sauka daga kan gadon ta nufi ban ɗaki.
ŞİMDİ OKUDUĞUN
AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)
KorkuLabarin wata hatsabibiya kuma fitinanniyar aljana da ta yi bayyanar bazata ga wata budurwa Zahara cikin wani irin salo na almara. Zahara tayi arba da Amriya cikin suffan mutane, har ta kwatanta mata gidansu, kuma zahara ta tafi gidan inda ta iske la...