Prologue

1.4K 75 11
                                    

A wata ranar alhamis bakin gabar kogi... Yanayi ne mai dadi a wurin, sama tayi baƙi kamar za'a yi ruwa, ga iska mai daɗi dake kaɗawa, igiyoyin ruwan kogin kuwa sai yawo suke daga gabas zuwa yamma wanda hakan yasa suka bayar da yanayi mai ban sha'awa. Sai dai duk da wannan yanayi mai daɗi, Zahra dake bakin kogin, bai wani sauya ta daga halin da take ciki ba. A kullum tana jin kamar bata da wani amfani a wannan rayuwar, yanayi mai muni da take ji tun lokacin da ta fara zama cikakkiyar budurwa. Da fara girman Zahra, ɗabi'unta suka sauya daga Zahra kamar sauran ƴan mata zuwa Zahra miskila, ita ce kullum shuru-shuru, dariya na yi mata wahala, kullum kai ƙasa, ga tsoron yin magana a cikin mutane da tunanin idan tayi magana za'a ce tayi laifi, ga yawan bayar da haƙuri koda kuwa ita aka yiwa laifi. Sanin balagar kowanne yaro da yanda take zo masa yasa, iyayen ta da sauran dangin ta suka yi tunanin zata daina wata rana. Gashi har yau tana da shekaru 22, ta idar da karatun ta har tana aiki a wani kamfani a matsayin sakatariya, alhali tun tana yar ƙarama take da burin zama yar jarida. Sai dai mafarkin ta bai cika ba, dalilin ƙarancin yarda da kai dake gareta. A ranar tantance shiga makarantar aikin jarida, ƙin zuwa tayi, domin tasa a cen cikin ranta koda taje ba zata ci ba. Makarantar da take son yin karatun, tana ɗaya daga cikin manyan makaratun garin wacce kowa yake da burin ace gashi a cikin ta. Da tunanin mutanen da suka fita kwarewa a rubutu zasu iya kunyatata a wajen yasa taƙi zuwa. Wannan aikin ma da taimakon mahaifin ta ne ta same shi, kuma tana ganin idan dai zata samu albashin ta ko ya yake toh ya wadatar da ita.
A hankali take kai komo bakin kogin, tayi nitso sosai a cikin tunani...

“Baiwar Allah baki duban gaban ki ne idan kina tafiya?...”

Dawowa hayyacin ta tayi, anan ta fahimci ta buge wata mata. Kyakyawar matashiyar budurwa ce sosai, dan Zahara bata taba ganin mace mai kyawun wannan ba, domin har wani ƙyalli take kai kace ita kaɗai rana ke haskawa. Rikicewa Zahara tayi da ganin wannan kyawun, dan tuni ta siffanta kanta da biri a gaban wannan kyakyawar halitta. Matashiyar budurwar tana sanye da doguwar farar riga, duk da kazantar rigar bai wani rage ko kaɗan daga kyan wannan mata ba. Siririn hancin ta, manyan fararen idanun ta da ɗan karamin bakin ta, yasa Zahara taji zata iya ƙarashe rayuwar ta tana kallon wannan matar. Zahara ta shagala da kallon budurwar da har bata jin masifar da take mata na buge ta da tayi.

“Dan Allah.. kiyi..hakuri..” Zahara ta faɗa dakyar tare da sunkuyar da kai, domin ba zata iya jure mugun kallon da matar take mata ba.

“Ke kurma ce ko me? Baki ji nace miki ni na bugeki ba? Kina cen kin lula wata duniyar, ni kuwa ina tsaka da fama da kaɗaici na.” Matar tace wa Zahara cike da fahari yayin da take fadar maganar ta ta ƙarshe.

“Dan Allah kiyi hakuri..”

Fuskar matar cike da mamakin wannan sanyin hali ko sakarci na Zahara. Ta faɗa mata ita ce ta bangaje ta toh me yasa take bata hakuri? Ita fa da mutum take son yin magana ba wai da mahaukaci ba.

“Wai meke damun ki ne? Gaki dai a shiga ta kamala amma kamar ba a daidai kike ba.” Cewar matar da ƙara jin haushin halin Zahara. Ita ma kuwa Zahra ta kasa fahimtar dalilin da yasa wannan matar take son dole sai ta janyo mata matsala. Abinda kawai take so shi ne a shafa mata lafiya.

“Shikenan, naji tausayin ki, yanzu faɗa min meye sunan ki?”

Zahra cen cikin makoshi ta fadi sunan ta, hakan kuwa ya baiwa matar nan haushi.

“Kin san dai Allah ya tsaga miki baki ko, kuma dan kiyi magana yanda za'a ji ne.”

“Sunana Zahara Usman.” Zahara ta sake maimaitawa, wannan karon ta ɗan ɗaga murya yanda matar zata ji.

“Yauwa Zahara, meye matsalar ki ne?” Matar ta tambaye ta.

Mamaki ne ya kama Zahara, domin wannan tambayar ita ya kamata ta yiwa matar nan ganin yanda ta takura ta, amma tsoro ya hana ta dan tana gudun kar ta ɓatawa matar rai. Yanke shawarar ta bata amsa tayi dan tana son su rabu lafiya.

AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)Où les histoires vivent. Découvrez maintenant