CHAPTER 10

1.3K 37 2
                                    


A BANGAREN SU ZAHARA

Tafiya suke a hankali cikin duhun dare, baka jin motsin komai. Zahara ji take duk wani taku da take yi, tamkar yana tafiya da duk wani kuzarin ta ne. Mama ta rike mata hannu, amma duk haka tana jin tsoro yana kamata a hankali. Bukatar kin zuwa na kara shigar ta. Shuru da hayakin dake tashi wanda bata san ko na meye ba a cikin makabartar na ƙara sa taji kamar ta falla da gudu. Kokowa take da duk wani sassa na jikin ta, dan kar ta kalli wuraren, ta saddar da kanta ƙasa. Ita kuwa Mama na bin tsohon a baya dan kar ya ɓace musu. Zahara tasan itama Mama cikin tsoro take amma bata son nunawa ne.

Tsoro Zahara take ji da kuma da nasanin zuwa. Nadamar kin bin shawarar Abba take yi. Haka kawai sun biyo wani tsoho dan yace musu yanada mafita akan matsalar ta ba tare sun san ko waye shi ba. Mama tace ta yarda da shi dan alamun sa na nuna mutumin kirki ne. Sai dai ko me Zahara zata ce ko zata yi lokaci ya ƙure...

Mama ce ta tsaya daga tafiyar da suke yi sakamakon shima tsoho ya tsaya. Juyowa tayi ta cewa Zahara ta karaso.

"Yi hakuri ki kara daurewa." Cewar Mama. "Saurin yin abinda yace, saurin ganin kin rabu da wannan abun da ke jikin ki. Kin ji?" Mama ta sake faɗa.

Gyaɗa kai Zahara tayi sannan ta ƙaraso inda Mama take. Tafiya suke wannan karon da dan saurin su ganin sun cimma inda tsohon yake tsaye yana jiran su. Bayan sun ƙaraso wajen sa, ya kama hannun Zahara. Kallon ta yayi a tsanake kafin ya juya ya kalli Mama, sannan ya saki hannun ta ya ɗora hannayen sa biyu bisa kafaɗun ta da iya ƙarfin sa dan zaunar da ita. Ita kuwa Zahara kokarin tashi tsaye take amma tsohon yaki bata dama. Sannan ya cewa Mama ta ɗan koma gefe dan ya samu yin aikin sa. Mama kallon Zahara tayi da kokarin nuna mata komai zai je daidai, amma ita Zahara wannan bai ishe ta ba a yanda take cike da tsoro.

Rufe idanu Zahara tayi lokacin da tsohon ya shiga kewayar ta. Bata san kewaya ta sau nawa yayi ba, amma tasan yanada yawa. A duk lokacin da ya kewaya ta sai taji tamkar tana shakewa. Tsohon yace ta zauna bisa gwiwan ta, amma gajiyar da take ji ba zata barta ba. Ita babu abinda take so yanzu face ta bar wurin nan da sauri.

"Mama...ni.. gida..nake son..tafiya.." Zahara ta samu nasarar haɗa kalmomin nan, amma Mama bata ce komai ba. Shi kuwa kamar yana jira ta faɗi hakan, ya dakata daga abinda yake.

"Zan kira Amriya zuwa cikin jikin ki. Dan haka ba wani abu bane idan baki iya tuna komai ba."

Da Zahara yake amma ita ba lallai bane taji abinda yace. Domin duk a gajiye take, ga kuma bukatar barin wurin da take da.

"Ayyarubo ramataniya sasiban.."
Tsoho ya shiga maimaita wannan kalmomin ba ƙaƙƙautawa a bayan Zahara. Ya shiga zuba mata wani abu a kai, ita kuwa ta daga kanta domin samun yin cikakken numfashi. Wasu ruwan ya sake fiddowa ya watsa mata wanda wannan karon suka sanyata amai bayan wasu yan mintuna. Zahara taji tamkar zata amayo da hanjin ta. Bata gani sosai amma abinda ya fito daga cikin bakin ta baki ne sosai fiye da gawayi. Wani azababben ciwo ne ya sanyaye mata jiki ta faɗi kasa kamar wani yasa ƙarfi ya ture ta. Ta kasa magana ko motsi. Fatar idanun ta a hankali ta fara yi mata nauyi. Ta kasa controlling jikin ta.

Mama kuwa tsoro duk ya kamata, jikin ta ya shiga rawa ganin ƴarta kwance a kasa. Tambayoyi suka fara yawo cikin kanta. Anya kuwa tayi abinda ya dace? Toh in fa mijin ta yayi gaskiya? Yanke shawarar korar tunanin tayi, tabi abinda zuciyar ta ke fada mata na son taimakon ƴarta. Addu'a kawai take yayin da shi kuma tsoho Malam Shehu ke warkar da ƴarta.

Shuru wajen yayi. Malam Shehu bai daina kewaya Zahara ba, kafin shima ya dagata. Numfashin Mama da kadawar iskar bishiyun maƙabartar kawai ake ji da ya bada yanayin nan tamkar a cikin horror film. Mama kallon tsohon tayi, taga alamar kamar murmushi a fuskar sa. Tana shirin ta tambaye shi dalili, ƴarta dake kwance bata motsi ta tashi da karfi tana gurnani tamkar karen zangai.

AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)Where stories live. Discover now