CHAPTER 12

1.3K 32 0
                                    

CHAPTER 12

HOME OF QUALITIE'S WRITERS ASSOCIATION 📚

Kwanaki hudu kenan Zahara ta kasa tashi daga bisa gado. Domin duk jikin ta a mace yake, babu karfi ko kadan. Bata cin abinci ko taci ma ba mai yawa ba. Koda Mama ta tursasa ta taci, mintuna talatin sun yi yawa ta amaye shi. Yanayin da ya tsorata duk dangin ta kenan. Karon farko da Mama da Abba suka samu matsala sosai, kamar Abba zai kai ga jikin Mama. Dalilin yana ganin Mama ce silar shiga halin da Zahara take ciki. Ganin Zahara kwance ba tare da ta iya yin wani abu ba, na kara harzuka Abba. Ita kuwa Mama bata nuna wani tashin hankali, kamar koda yaushe, amma duk da haka Zahara tasan boyewa kawai take. A bangaren Zahara ma tana iya kokarin ta ganin ta tashi ta samu sauki amma ta kasa. Tayi neman tayi neman cikin kwanyar ta ganin ta tuna abinda ya faru a makabarta amma, kawai abinda ta sani ta fita hayyacin ta ne yayin da Malam Shehu ya zuba mata wasu ruwa, kuma ta dawo hayyacin ta a cikin dakin ta bisa gado, da wata laya daure a hannun ta. A lokacin da ta farka ba taso tayi tambayar abinda ya same ta ba, amma bayan wasu kwanaki ta tambayi Mama. Saidai Mama bata yi mata wani karin bayani ba. Dan haka duk a cikin rudu take, gashi babu alamun ta samu sauki.

Kwanaki biyar bayan zuwan su makabarta, Zahara ta fara samun sauki. Lokacin da Mama tazo kawo mata break fast din ta, bata tarar da ita kwance bisa gadon ta kamar kullum ba. A dan kankanin lokaci, taji gabanta ya fadi ta dauka wani abun ne ya sake faruwa, amma ganin Zahara ta fito daga ban daki, tana tafiya lafiya lau kamar komai bai faru ba, yasa Mama ta sauke doguwar ajiyar zuciya tare da jin kamar tayi tsalle dan murna. Ajiye plate din abincin tayi, ta nufi wajen Zahara tana yi mata ya jiki.

“Ya jikin naki? Da kanki kika iya yin wanka? Me ya faru? Na kasa fahimta, jiya fa ko hannu baki iya motsawa.” Cewar Mama cike da farin ciki da mamaki.

Zahara ma farin ciki take ganin Mama ma haka. Saidai ita kanta mamakin warkewar ta take farat daya.

“Bansan me ya faru ba Mama, amma lafiya lau nake jin kaina. Ina jin har zan iya tashi na kewaya gidan nan da gudu.” Zahara ta fada tana murmushi.

Nufar inda wardrobe dinta take tayi, ta dauko wata doguwar riga da zata saka. Mama da har yanzu cikin mamaki take, a zuciyar ta tana tunanin ko layar hannun Zahara ce silar warkewar ta. Daman ta yiwa Zahara kashedin kar ta yarda ta kunce layar daga hannun ta. Ganin yanda Mama ke yi mata kashedi, ya isheta gane cewa layar tana da muhimmanci. Dan haka tayi alkawarin ba zata taba cire ta ba.

“Ki ci abincin ki 'yata. Zan je in kira Abban ki dan sanar da shi. Shi ma hankalin sa a tashe yake dalilin halin da kika shiga.”

“Toh, zan sauko na taya ki aiki idan na gama.”

“A'a.. a'a kar ki ma fara, ya kamata ki kara hutawa.”

“Ki yarda da ni Mama, na warke babu abinda ke damuna. Ba zan iya jure zama a dakin nan ba, ko na minti daya.” Zahara tana fada tana mai nunawa Mama a fuskarta irin yanda ta tsani kwanakin da tayi a ciki a kwance.

“Toh shikenan zaki iya saukowa, amma ba zaki taba komai ba.” Cewar Mama da sigar gargadi.

“Shikenan Mama.”

Murmushi Mama tayi mata kafin ta bar dakin. Zahara taji sauki in dan sauki, amma bata daina tunanin ogan ta da kuma abinda Amriya ta aikata ba. Murmushin ta bacewa yayi lokacin da ta tuna, tana ganin kawai zata rubuta takardar barin aiki domin bata jin zata iya hada ido da Mr. Ammar bayan raba shi da wacce zai aura da tayi. Kunya take ji sosai, duk da ba ita bace asalin wacce tayi laifin.

Yanke shawarar rubuta takardar tayi, gobe sai taje ta kai a office. Daman tsawon kwanaki kenan bata je wajen aikin ba, kuma babu wanda ya kira ta. A ranta tace, wata kila ya samu labarin abinda tayi. Wata kila Kamal ya fada masa komai. Yace kuma kar ta fadawa dan uwan nashi, dan haka bata tunanin shi ya fada masa. Koma dai meye, zuwa gobe zata ajiye aiki. Bata san ko zata kara samun wani aikin da yakai wannan ba, da kuma ogan da yakai Ammar mai saurin fahimta. Koma dai meye kunya ba zata kashe ta.

AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)Where stories live. Discover now