CHAPTER 50

194 13 4
                                    

Damuwa Zahara take ciki, yau ta ƙare internship nata kuma wannan shi ne weekend ɗin ta na ƙarshe kafin ta koma London. Tambayoyi da yawa na yi mata yawo cikin kai, shakku ya bi ya dabaibaye ta. Shin ko ta yanke hukuncin da ya dace? Sosai take cikin ruɗu da ta rasa me ya kamata ta yi. Tuni ta shirya kayanta lokacin tafiya kawai take jira.

"Yanzu kuma so take, na ƙara bata lokaci." Muryar Habib ce ta dawo da ita daga duniyar tunani.

Sam ta manta da restaurent suke. Ta gayyaci Habib ne dan su yi magana kafin ta koma.

"Kamar ma ba kya saurare na." Habib yace da ita.

Girgiza kai tayi domin ta kora tunanin da ke addabar ta kafin ta bashi amsa
"Sosai ina sauraran ka, amma na kasa fahimtar me yasa rasuwar Maryam zata shafi soyayyarku."

"Yanda ta ce, na kasa dawowa hayyacina tun bayan rasuwar Maryam. Kawai na nemi da ta bani sati ɗaya lokacin komai ya daidaita, bayan nan da na dawo gare ta da gaske amma tace wai ban shirya ba. Ta nemi na bata lokaci kuma na bai wa kaina lokaci. Na kasa fahimtar komai kuma ina tsoron kar na rasa ta."

"It was quite a complex story amma nafi jin kamar ita ce bata san me take so ba. Ka nemi da kuyi magana once and for all sannan ka tambaye ta ka ji asalin abinda take so. It sucks to let you torture yourself like this."

"Na fara gajiya, I too want to locate myself." Ya faɗa tare da shafar fuskarsa.

"I am really sorry for you, akwai wani abu da kake ganin zan iya? Idan akwai wani taimako da zan yi iya yi zaka iya sanar da ni."

"No Zahara, ke ma kinada naki damuwan. Zan ji da wannan kar ki damu, okay?"

"Okay." Zahara ta faɗa tana mai gyaɗa masa kai.

"So, yaya zancenku ke da..."

Katse shi ta yi.

"A'a... Kar ka ƙarasa faɗa Habib."

"Ya kamata kuwa, baki daina gudun wannan hirar ba har yau. Kar dai ki ce min haka zaki koma, cikin ruɗu?"

"Me kake son na ce maka? Yana rayuwarshi ina yin tawa kuma duniya na cigaba da tafiya."

"You don't believe for a second what you say."

Ɗan tsaki Zahara tayi tare da cewa "Bana son wannan maganar kwata-kwata." Ta faɗa da alama hirar tasu ta fara ɓata mata rai abinda yake mawuyaci a gare ta kenan.

"Kar ki ɓata ranki, kawai bana son ki zo kina nadama ne domin nasan kina son shi. Matar nan tana son tayi manipulating ki kuma ina tunanin tayi nasara. Kamal ba yaro ba ne, zai iya auren har mace huɗu. Me yasa wannan matar take da ƴancin kasancewa cikin farin ciki ke banda ke? Bayan duk abinda ta aikata miki. Ina ganin ba adalci bane hakan."

"Hukuncin da na yanke baida alaƙa da ita, inada rayuwata a London kuma bana tunanin zan watsar da komai saboda shi."

"Ba cen zaki koma da rayuwa ba in jin?" Ya tambaye ta kai tsaye.

"A'a zan dawo da zaran na samu diplomana kuma ina son kayi min wata maganar daban, ina tunanin tsakanina da shi shikenan."

"Shikenan, kina son na raka ki ne airport?" Habib ya tambaye ta.

"Eh please, su Mama ba zasu samu damar zuwa ba kuma bana son tafiya ni kaɗai."

"Okay, kar ki damu zan zo akan lokaci."

ƁANGAREN KHADIJA

"Ka gane abinda na faɗa maka?" Ta tambayi matashin yaron da ke ta gyaɗa kai dan nuna mata alamar ya fahimci bayanin nata.

Tashi yaron yayi ya bar falon, ya bar Khadija da Salmah da ke ta yiwa ƙawar tata wani irin kallo.

"Humm, Khadija ni dai ban amince da duk wannan abin da kike yi ba."

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 02, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)Where stories live. Discover now