Koda ta shigo cikin falon duka kallo ya koma kanta. Har wani shuru ya karade falon na wasu yan mintuna tsabar ta dauke hankalin kowa dake wurin. Duk da haushin ta da Salmah take amma tasan da tayi kyau. Juyawa tayi wajen Khadija da itama ke ta faman kallonta. Zungurar ta tayi domin maidota a duniyar zahiri. Salmah a ranta tace tanada kyau amma ba wani abun ayi ta kallon ta bane, kuma ita ba zata iya saka wannan rigar ba, domin ba wata mai tsada bace.
"Ki daina kallonta dan Allah Khadija. Kina kunyatar dani."
Cigaba da kallon Zahara tayi na wasu yan dakiku, kafin tace
"Wai dan Allah wacece wannan yarinyar?""Ita ce sakatariyar Amar, na tsaneta ko cen dama, karki kara bani wata hujjar da zata sa na kara tsanar ta. Ki daina kallonta."
"Ita ce tazo tace miki kiyi hankali da guy din ki? Hum.. inda nice ke, da zan yi hankalin. Kinga yanda take kuwa?"
"Oh mayar mana da hira baya zaki yi kenan, cen dama a dame nake. Kuma ke kika ce na manta da ita. Kenan kina nufin na yarda da abinda ta fada mini? Ni nasan Amar kuma nasan ba zai taba cin amanata ba."
"Eh da wannan yarinyar kam, ko limamin limamai zai iya fadawa tarkonta. Amma dai..." Khadija tacewa Salmah tana kallonta.
"Mtsw, ni bansan me yasa nake ta biye miki muna maganar ta ba."
Juyawa Salmah tayi dan ta zauna kusa da Khadija, amma taga har yanzu Khadija Zahara take kallo.
"Khadi ki daina kallonta!" Salmah ta fada da dan daga murya, amma Khadija ta riko kanta tana kokarin tirsasata sai ta kalli inda Zahara take. Kokarin kwacewa take amma koda ta tsinkayo saurayin ta ya nufi wajen Zahara, zuciyarta ta bada dam.
"Maza tashi ki je.." Khadija ke fada mata, ba tare da ta janye kallonta akan su Zahara ba.
"Kwarai kuwa zan je." Salmah ta fada tana mikewa tsaye da sauri dan kwalinta na faduwa. Ita ma ta nufi wajen su.
Suna tsaka da magana, Salmah bata san me suke tattaunawa ba amma suna ganinta suka yi shuru.
Zuwa tayi kusa da Amar tana wani shigewa jikin sa, kafin ta juyo ta kalli Zahara tace
"Sannu Zahara'u ko?""Yauwa sannu Salmah. Kin yi kyau fah. Kuma Zahara sunana."
"Humm nagode. Kema bakida laifi." Salmah ta bata amsa da murmushin ta na munafunci.
Sarat ce ta karaso inda suke.
"Sannun ku duka." Ta gaishe su.
Tana karasowa Amar ya dauke wuta, wani irin kallo yake binta dashi. Kallo daga sama zuwa kasa kafin ya koma ya kalli Zahara da itama shi take kallo. Kan Salmah ya daure, bata fahimci komai ba. Tana ganin raini ne a gareta. Sun sha zuwa wuri mai dauke da yan mata masu kyau amma Amar bai kallon su sai dai ya maida hankalin sa gareta. Kodai ya boye mata asalin halinsa ne tsawon wannan shekarun da suka yi? Kenan Zahara tayi gaskiya da tace mijin da zata aura ba wanda take tunani bane?
Ganin irin kallon da Khadija take masa, yasa a rikice yace
"Yauwa..sannun..ki Sarat.'"Rikicewar da yayi ta kara sakawa Salmah shakku. Ta kasa fahimtar me yasa zuwan wannan yarinyar ya saka shi cikin wannan yanayin. Ko yana cin amanarta da ita ne? Ko kuma ya taba gwada cin amanarta da ita?
"Zan iya magana da kai na minti biyu?" Salmah ta tambaye shi.
"Eh me zai hana? Afuwan ladies."
A hankali Salmah taja hannun sa zuwa wani bangare da babu kowa.
"Amar... ko zaka fada min meke faruwa?"
"Ke dai zaki fada min abinda ke faruwa da ke. Kina yin wani abu wanda na kasa fahimta."
YOU ARE READING
AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)
HorrorLabarin wata hatsabibiya kuma fitinanniyar aljana da ta yi bayyanar bazata ga wata budurwa Zahara cikin wani irin salo na almara. Zahara tayi arba da Amriya cikin suffan mutane, har ta kwatanta mata gidansu, kuma zahara ta tafi gidan inda ta iske la...