CHAPTER 39

603 14 6
                                    



“A'a, baku da ƴancin shigowa nan ! Ku fitar min daga gida.”  Cewar mahaifiyar Zahara cikin masifa.

“Ki saurare mu Mama, mun zo ne ba dan komai ba sai dan mu warkar da ƴarki.” Cewar Malami Sheikh Said.

“Ban damu ba malam, ku fita ko na kira muku ƴan sanda.”

“Kwantar da hankalinki Asiya, ki daina ihu kuma ki nuna ɗa'a ko yaya ne ga waɗanan mutanen.” Cewar Abba.

“Bismillah mu je falo.” Abba ya cewa su Kamal.

Suka nufi falo ba tare da sun kula Mama da ke ta masifa ba. Dukansu a takure suke dan ba daidai ba ne su tsaya alhali tana ihun su tafi saidai daman tuni malaman sun san irin hakan zata faru. Kamal ya yi musu bayanin komai kuma sun fahimta. Sheikh Said ya ce musu zai iya yiyuwa ita ma Mama aljanar ta shafe ta.

“Wai baku ji na ne ko me? Maganata batada wani muhimmanci a gidan nan kenan? Sai da ka kira su alhali na yi maka kashedi da ka cire kanka daga wannan zancen.”

“Ba zan dawo a wannan zancen ba, ni ma Zahara ƴata kuma ni ma na damu da halin da take ciki kamar ki, dan haka zaki ƙyale mutanen nan su yi aikinsu.” Abba ya faɗa.

“Zan bar gidan nan kuma zan tafi da ƴata!” Mama ta faɗa tare da juya baya.

“Afuwan Madam.” Sheikh Said ya kira ta.

Tsayawa Mama ta yi ba tare da ta juyo ba.

“Muna bada haƙuri akan wannan lamarin da har ya kai ga haka, muna son kawai ceto ƴarki ne. Idan ba mu yi wani abu ba, wannan halittar Allah zata iya ɓata mata rayuwa ba tata ma kaɗai ba. Tsubbu babu abinda zai iya yi akan ta. Ba a yakar sharri da sharri. Allah ne kaɗai zai iya taimakon mu.” Cewar Sheikh Said.

“Ka gama? Babu abinda na nema daga gurinku. Ba ku ba ne zaku faɗa min abinda yake daidai da ba daidai ba ga ƴata.”

Daidai lokacin da Kamal ya nufi inda Mama take da niyyar ya lallaɓa ta, suka ji sautin tafiya daga kan stairs. Kowa ya yi shuru. Kowa ya san Zahara ce ko Amriya.

“Meye duk wannan? Akwai masu son yin bacci fa a gidan nan !” Ta ce musu koda ta saka ƙafa cikin falon.

“Ohh, baƙi muka yi. Kun zo ne saboda ni ko? That you are ridiculous.” Ta faɗa da sigar dariya.

“Mama ke kika ce min ba...”

Mahaifiyarta ta ƙatse ta.

“Mahaifinki ne ƴata, ni ba zan taɓa cin amanarki ba.”

Daidai lokacin ba tare da kowa ya ankara ba, malaman suka fara karanto ayoyin Alkur'ani.

Lokaci guda, Zahara ta murtuke fuska, murmushin da ke kan fuskarta ya gushe. Ta yi ƙoƙarin barin falon amma Abba cikin sauri ya riƙo hannunta da ƙyar ya kawo ta gaban su Sheikh Said. Tsawon duk wannan lokacin, Amriya bata ce komai ba, kawai tana ta kokowa ne da Abba. Sheikh Said ne ya karɓe ta daga hannun Abba ya riƙe hannunta gam ya cigaba da karatu.

Koda suka fara yin ruqya, mahaifiyar Zahara bata sake motsawa ba. Zaune ta yi ta ƙurawa babu ido. Abba ya kalli Sheikh Said, da alama ta hannu Sheikh ya nunawa Abba ita ma aljanar ta taɓa ta.  Ana haka sai ta fara amai.

Ba ma za a iya auna adadin abinda ta amayo ba. Da fari abubuwan da ta ci ne kawai... shinkafa da wasu abubuwa masu kama da kayan itatuwa. Bayan nan ta fara amayo gashi da wani ɓakin abu mai ban al'ajabi.

Da sauri Abba ya nufi inda take, shi ma haka Kamal.

“Ya kamata ta fitar da komai.”

Ɗaya daga cikin malaman ya tsayar da karatunsa dan ya faɗa musu hakan. Da yin wannan, Zahara ta yi numfashi da ƙarfi, sannan ta fara nishi kamar mai jin zafi sosai.

AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora